DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Sama sama ta fesa turarukan kafin ta nufa jakar siyayyar data gani a dakin ta bude taga duk cikin siyayyar kayan dayayi jiyan ne ta fiddosu tana dagawa taga wata fitinanniyar rigar baccin data sanyata maidata da sauri cikin jekar tana yamutsa fuska da zallar mamaki da qin gasgata me tunanin hakan ke nufi?
Yagama wulaqanta rayuwarta tako Ina idan har ya siyo wainnan kayan baccin ne Dan Yana tunanin ita tasaka.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107

DM 26
Akwai riga da wando three quarter red Wanda Suma kadaine kayan sawar ta fitar ta Sanya daqyar sai alokacin ta lura hadda bra da panties acikin siyayyar ta dago bra din ahankali tana dubawa cikin tsoro da mamakin ganin dukkaninsu size dintane,
Cikeda takaici da qin yadda da ya akai ya San sizes din nata ta maida kayan ta fice daga dakin tana Jin koina na gidan siqe Mata numfashi yake sbd tsananin kosawa da tsanar komai na gidan datake ji.

Sallar azahar Tai Takoma takuma hada tea tana cikin sha aka Danna doorbell ta waiwayo tana kallon hanyar kofar tana ayyana bashi bane
Idan shine baya buqatan doorbell din Dan Haka ta tashi da tunanin ko waye zai taimaka Mata ta nufa kofar bayan ta Sanya hijab ta bude Kai tsaye.

Sojace mace sanyeda uniform ta kalleta cikin tsananin girmamawa tace”

Good afternoon mah.

Qaton basket din hannunta dayake daukeda food warmers kusan guda uku sai ledojin fresh fruits ta nunawa Naj din tana cewa”

Marshal yasa akawo Miki wannan Yana meeting tareda sauran Marshals dinnmu dasuka zo.

Ahankali ta bude Baki ta furta”

Thank you” tana miqa hannu ta karba ta shige dasu sojar tabar gurin tana cewa”

Idan kina buqatan wani Abu Ina daga Nan waje tareda dayan soldier dinmu mune muke gadin Nan.

Tana ganin kulolin tasan na gidane take taji hankalinta a na neman tashi da fatar basusan tana Nan dinba gurinsa, daqyar ta iya takura kanta taci abincin sbd batason taqici takasa samun qarfin Hana kanta bacci yau bare yasamu damar kaita dakinsa.
Tana gamawa ta Kai kayan kicin tadawo ta zauna a palon lissafinta na neman mafita na ninkuwa Dan kuwa zuwa yanzu din tana ganin zai iya Kai hakurinta da rashin maganarta maqura Kuma batasan kwanaki nawa zai jata anan dinba tunda tasan ko ajikinsa tunda kamar tozarcine yakeson yimata Dan Haka kawai ta yanke hukuncin idan yadawo zatai masa magana Dan idan ya manta matsayinta na qawar yayarsa to ya tuna ita batada abin Yi dashi.

Hankalinta ko daya baya Kan TV dake aiki zuciyarta a cunkushe take bayan komawarta gida Babu abinda take buqata.
Sake daga Kai ta duba agogo tayi tana Jan numfashi me zafi ganin karfe hudu harda mintuna ashirin ta miqe takoma dayar dakin tayi sallar la’asar tayi zamanta Bata fito tana karatun wani littafin yaren French data gani a palon har akai sallar magriba Bai dawoba Dan Haka ta sake fitowa palon ta nufa dining ta zuba abinci kadan taci Tasha lemon tea da Zuma tana kicin taji dawowarsa taqi fitowa sai daya shige tafito ta nufa dakin tashige ta rufe kofar tana tayarda sallar ishai.

Baya tareda wata doguwar gajiya Dan Haka kayansa yafara rabuwa dasu duka ya daura towel a qugunsa ya nufa toilet ya sakarwa kansa ruwan dumi Yana lumshe ido sbd Jin kansa dayake yau din free Dan meeting dinsa na yau din ya kammala aikin daya dawo dashi dan lokacin dayake dawowar baiyiba.

Fitowa yayi yana goge jikinsa ya tsaya gaban madubi Yana sake goge kansa ya dauki Neutrogena oil kadan ya shafa ajikinsa kafin ya shafa body spray na Creed Aventus yabar gaban madubin ya qarasa closet ya Sanya kayan bacci farare masu tsantsi ya zura slippers yafito Yana waya da Hannah a natse cikin qowa da surutunta nason zuwa Nan gurinsa tagansa.

Direct dining ya nufa Yana zaunawa ahankali yaci abinci kadan ya taso riqeda Red Bull energy drink yanasha yazo ya zauna palon Yana kallon labarai.

Ya Jima zaune a palon Yana kallon labarai tareda amsa waya akai akai.
Bude kofar dakin tayi ta fito sanyeda hijab din datai sallah ta nufosa fuskarta a Dan hade ta qaraso tsakiyar palon ta Dan tsaya daga gefensa ta Dan kallesa tana taqaita kallon nasa Kai tsaye da muryarta mara hayaniya tace”

Inada abubuwan dasuke jirana a gida da gurin ai….shiru tayi tareda waiwayowa ta kallesa har lokacin Bai juyo ya kalletaba idanuwansa na Kan TV da waya ahannunsa ta dauke Kai tana tamke fuska Kai tsaye taci gaba da cewa”

Inada abinyi Babu wani dalili ko amfanin zamana anan pass na shigowa anguwar kawai nake buqata inada inda zansa Azo daukana acikin Daren Nan Dan bana buqatan qarin ko kwana daya anan.

Juyowa yayi ahankali ya zuba Mata fararen idanuwansa Yana qarewa fuskarta kallo zuwa hijab din dayayi Mata kyau tsawon seconds kafin juyar da kansa Yana duba Kiran daya shigo wayarsa yaga sunan Hannah ya dauke Kai Yana sake maidawa kan tv ya bude Baki Yana waiwayowa kadan ya kalleta da wani irin kallo yace”

Kije ki kawomun ruwa marasa sanyi sosai zansha.

Da mamaki me girma ta kallesa ganin yanda yayi maganar Kai tsaye fuska a kame ba alamar tsokana ko wani Abu Mai Kama da hakan,ranta ya ninka baci ta juyo gaba daya gabansa ta kallesa cikin gajiya tareda kosawa da duka wannan abubuwan dake faruwa tsakaninsu kai tsaye tana bayyanarda bacin ranta tace”

Inaga ai kaji abin Dana fada farko right?
Menene wannan kakeson nunawa?
Mijin ko me bada umarni? kokuma me?
Banda lokacin duka wainnan ban buqatan fada maka Amma ai kasan matsayinka da matsayin auren so please just quit all this kaban pass Ina buqatan barin Nan.

fararen idanuwansa ya dago ya zuba Mata dasuka fara saka maganarta gargadan fita ta dauke idonta akansa tana Jin idanuwansa akanta suna neman hanata fadar abubuwan datake fadar ta juya cikin takaici zata bar garin ya riqo hannunta ahankali tareda janyota tadawo baya ta Fado jikinsa zaune yayi Mata wani irin riqo Yana kallon fuskarta dake kaucewa kallonsa cikin muryar data sanyata waiwayowa ta kallesa batareda ta saniba yace”

Meyasa kikeson nanata kalmar girman ikona akanki?

Ahankali ya zare Mata hijabin ya aje Yana sake shigarda fuskarsa cikin wuyanta Yana shinshinawa cikin ya zura hannuwa ya shafo cikinta Yana cewa”

Abin dake nuna kansa basai nafadaba shine nine mijin,nine me ikon,nine me bada umarnin Kuma nine Zan zamo me damar Amma yanzu bazaki gane hakan ba sai Nanda watanni Inshallah result din damata zai bayyanarda kansa Amma dai shi bakin Nan daga yau zai daina magana akan iko da dama…

Bata ankaraba taji hannuwansa cikin wuyanta Yana juyo da fuskarta ya hade bakinsa da nata yana lumshe fararen idanuwansa cikin nutsuwa.

Qwacewa tafara kokarin Yi Amma takasa sbd irin shigar da itan da yayi ajikinsa gabaki daya ya rufeta bayan sarquqan numfashinsu saitaji bugun zuciyarta na tsanantuwa da fargaba ta bude idanuwanta akan nasa idanuwan dake rufe takai hannuwanta biyu Kan fadadden kirjinsa zata turesa daga jikinta ya cirata gabaki daya ya nufi dakinsa da ita Yana sake Bata kyakkyawar runguma cikin jikinsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button