DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Koda qarfe goma Sha biyun Rana tayi baqi kowa ya hada jakarsa ya kama hanyar komawa gida Dan Haka gidan su anty Amina dasu Khadija da zainab din Anty Amina sai aikin gyaran gidan suke Dan Haka Koda la’asar tayi gidan koina yayi fes fes sai mutan gidan kawai Kamar ba’ai taron biki ba dan ma da Dattijo Bai tsaya akan kowa ya watse yau ba da akwai wainda sai sunqara sati kila kafin su koma.

Bayan sallar isha tayi wanka tareda Shirin bacci tasaka riga da wando masu tsantsi na baccin kalar maroon ta janyo wayarta datun jiya data shiga tashin hankali take kashe ta kunna tareda ajewa gefe batareda tabi takan wayarba ta Haye gadonta tana Shirin kwanciya ummanta tashigo daukeda wani ruwan turaren humra me shegen qarfin qamshi ta ajiye gaban madubi tana zubawa a hannunta tahau shafawa Naj din akoina ajikinta tana cewa”

Sauko Dadah na Kira kutafi gurin hajjo duk da wannan baza’a kirashi da tarewaba Amma dai tafiyar kenan kila sauko ki sauya Kaya Mana.

Bata dago ta kalli ummanba tayi kamar bazata saukoba tsawon mintuna kafin dai ta sauko tana zura slippers dinta dake bakin gadonta ta nufi wardrobe dinta ta bude ta dauko wata sabuwar jallabiyarta me Fadi kalar coffee brown ta warware ahankali ta saka kan kayan baccin Dake jikinta kafin ta jawo qaramin Chantelle veil ta yafa akanta Dan Bata daura ko dankwanlin jallabiya
Umma kuwa binta tayi tayi tana watsa Mata turaren harya ushers Yana Mata yawa murya a shaqe tace”

Umma Dan Allah ya Isa
Yana min yawa cikin Kai.

Dainawa umma tayi tana murmushi cikin kulawa tace”

To shikenan ai na barshi Haka Amma bazaki sauya kayaba…..idon da Naj din ta zuba Mata yasa ta waske zancen da sakin murmushi tana cewa”

Ko hakan ba laifi muje ku tafi gobe Amina zata kawo Miki kayanki Dattijo ma na gurin Dadah suna jiranki.

A dakin Dadah abun takaici agareta sabuwar nasiha da lallashi suka Dora Mata da dadin Baki da komai itadai tana jinsu batace komaiba sai sauraro  kawai sai Kuma zuciyarta dake Mata zafi da baqin ciki har lokacin Haka suka Gama ta ta fito itada Dadah da Dattijo Wanda ya fito da Kaya niqi niqi shida Anty Amina da Umma habiba kishiyar ummanta zasu maida gidansu Abbas acikin Daren.

Suna isowa bakin gate da wani irin sauri sojojin Marshal suka taso suka bude Mata kofa suna Mata gaisuwa cikin tsananin girmamawa dayasa Dadah sakin wata sabuwar hamdala cikin ranta abun na Mata Dadi sabanin Naj da “thank you” kawai ta iya bude Baki ahankali tace tana wucewarta kamar ba Amarya ba Kai tsaye gurin sashen hajjo suka nufa gidan tsit Suma duk baqi sun tafiyarsu.

Itace a gaba Dadah na bayanta da kallon ikon Allah da wannan Alamari saidai dayake lallabata sukeson Yi sai batace komaiba suka Isa babban palon gidan dazai isar da ita bangaren hajjo.

Kai tsaye ta shigo palon hajjo idonta dasuka kumbura suna kan kofar dakinta datakeda niyar shigewa ta rufe ta kwanta data shigo Dan Haka Bata lura da mutum dake zaune a palonba Yana cin abinci kan dining ta shige tabar Dadah dake shigowa da zama tana washe Baki ganin Jalal din zaune yanacin abinci tareda hajjo.

Cikin sakewa da farin cikin ganin Naj hajjo ta taso tana yiwa Dadahn barka da zuwa suka zauna suna sake gaisawa.
A ‘dan taqaice ya taso yaxo suka gaisa da dadah yakoma dining din Dan baima faraba yanzune zai fara cin.

Hajjo na kallon kofar dakin da Naj tashige tasaki murmushi tana cewa”

Inshallah ahankali zata sake ai tamayi kokari da biyayya ko ahakan Dan Haka baza’a takirata ba zatai zamanta taredani har su daidaita da mijin.

Zare jallabiyar jikinta tayi tabar kayan baccinta har zata kwanta ta fasa ta fito Dan zuwa gurin hajjo Dan Bata Saba fushi da hajjon ba duk kuwa yanzu tanajin kaman antaru an Mata rashin kyautawa da adalci.

Tana fitowa dukkaninsu suka kalleta hajjo na murmushi tace”

Zo ki zauna Nan Najma Babu Mai takuraki akan auren Nan Inshallah,
Zaki zauna Dani har sai lokacinda kikaji da kanki kinason komawa gurin mijinki…. Da sauri Dadah tace”

Ba maganar saita buqata da kanta tunda ba itace me ikon kanta da yanda takeso ba,
Idan Kika biyeta tunda ba tunani cikakke akantaba da Haka zata qare rayuwar auren bare tana ganin cewan ta girmesa Wanda girmewar ta zama ta banza da wofi dankuwa yanzu a qasanshi kike.

Murmushi manya hajjo tayi tana kallon Najman dake gefenta zuru tace”

Bazata tareba saita buqata hakan da kanta inshallah,
Ina Kuma da tabbacin zata buqaci hakan Inshallah.

Kasa wata magana Dadah tayi sbd takaicin Najman datai shiru alamar hakan shine yayi Mata daidai ta miqe tana cewa”

To na tafi Ni Saida safenku Allah ya bamu alheri Dan dai Naga alamar a sashenki kila za’a haif….katseta hajjo tayi da cewa”

Amin ya Allah Dadah Saida safe” saboda sanin Dadah zata iya yanko zancenta tsakani da Allah.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107DM 14
Bayan tafiyar dadah hajjo ta kalli Najma da kallo daya zakai Mata kasan Kuka ta kwana ta yini tanayi duk da hakan fuskarta is so fresh sbd wankan da Bata Jima dayiba ga qamshinta tunda tafito ta zauna yake gauraye palon maida kallonta kan hanyar dining da jalal ke gurin har lokacin yanacin abinci Kamar wani sarki Wanda har lokacin Naj batasan da Yana palon ba ta miqe tana nufar hanyar dakinta tace”

Jeki ki kawomin ruwan dumi daki da Zuma zansha na kwanta ‘yar gajiya nakeji.
Shigewa dakinta tayi tabar Naj na lumshe ido ahankali cikin sanyin jiki ta miqe ta nufi dining hanyar dining Dan dauko zuman tana tafiya a natse har saidata shiga dining area din da kyau taga Wanda ke tsaye agurin hannuwansa sanye cikin aljihun guntayen qananun kayan dake jikinsa zai bar gurin tana isowa.

Mayun fararen idanuwansa ya ‘dan zuba Mata sbd yaji maganar Dadah ta banbancin shekarunsu data kawo Wanda yasashima ‘dan kallon nata Dan ganin abinda ake ikirarin ya girmesa a jikin nata Wanda a iya ganinsa baiga komaiba sai kayan baccin dake jikinta riga da wando ba bra ajikinta sai idanuwanta dasukai nuni da kukan datai ya kalli iya tsayinta da shafaffen cikinta ya dauke Kai ahankali Yana barin gurin yabarta tsaye tanajin wani irin damuwa da ‘dacin zuciya me qarfi duba da kallon tsaf sama sama da yayi Mata ya dauke Kai ya wuce yabar gurin da qamshinsa na Tom Ford, Tobacco vanille daya zama Kamar maita tasan qamshim kamar me sbd shikadai tasani me amfani da turaren Dan tsadarsa.

Numfashi me zafi ta sauke tareda shaqaqqen tsokin dabai fitoba taji duk komai ya fice Mata a sukwane ta hadowa hajjo ruwan takai Mata ta fito ta wuce daki ta kwanta tanajin wani Abu toshe a maqogoranta da qyar tasamu bacci ya dauketa.

Qarfe Tara na safe ta fito Palo sanyeda doguwar straight gown ta atampar super exclusive maroon dataiwa farar fatarta kyau fuskarta fayau ko kwalli Bata sakaba saidai qamshinta daya zama na koyaushe dayake tashi jikinta idan ta kusantoka.
Da slippers a qafarta ta nufi kicin ta hado tea me zafi sosai tadawo Palo ta nufi dakin hajjo tana sha ta zauna kujerar dakin tana cewa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button