DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Na yarda da qaddara hajjo Amma tayaya Dattijo zai lalata rayuwarta ta hanyar aura Mata wani cikin fushi idan ikirarinsa yazama gaskia rayuwarta zata iya lalacewa a qarshe dai auren da aka dage da sai tayin baiyi Rana ba kenan.

Inshallah rayuwar Najma bazata lalace Alfa bazai Bari a lalata rayuwar Najma ba zanyi magana dashi idan har sun fasa auren a hakura Allah zai kawo Mata wani.

Sai alokacin Anty Amina dake dakin Naj da Babu mutane tareda umman taji abin daya faru hankalinta yayi mummunan tashi cikin damuwa da Dan tsoro ta kalla idanuwan umman dake son cikowa da hawaye a raunane tace”

Umma Dan Allah kada kiyi kuka wannan jarabawace Allah kewa Naj Inshallah zata cinye.

Sauke Kai umma tayi tana girgizawa ahankali cikin tsananin baqin ciki da damuwa tace”

Wannan jarabawatace Nima sbd Ina cikin wani hali na tsananin baqin ciki da damuwar rashin auren Naj
Dadah bazata qara Bari nasha ruwa gidan Nan ba cikin kwanciyar hankali
Ga Dattijo Yana rantsuwar aurar da ita ko duk Wanda yasamu wannan karon tayaya Zan iya kwantar da hankalina da hakan?.

Zama Anty Amina tayi itama tana rafka tagumi cikin tashin hankali da tsoro ta bangare daya tana adduar Allah yasa kada Abbas din yafasa sbd duk halinsa gwarashi an sanshi idan yafasa ba’a San wa dattijo zai aurawa Naj din ba tunda yayi rantsuwa to tabbas kowa yasamu zai iya daura mata Dan Haka ita dai anata gwara Abbas din dai ko yayane.

Ta bangaren Dad Alfa hajjo takirasa yazo tayi Masa bayanin komai ta dora da cewa”

Auren wannan yaro ga yarinya Mara hayaniya da nutsuwa Kamar Naj Sam baiyiba Kuma hakan ya nuna Babu da’ar sanin darajar mace data aure atare dashi Dan Haka idanma su Basu fasa din ba kayi magana da Dattijo a hakura afasa bashi auren.

Shiru Dad Alfa yayi Yana nazarin maganar wadda ta Sosa ransa matuqa shima sbd yanajin Najma tamkar Hanifa Dan Haka Aure Kam kosu Abbas Basu janyeba babushi Dan idan har zai iya yaga Mata rigar mutunci Haka acikin gidan iyayenta tun kafin aure bayan aure al’amarin bazaiyi kyau da dadin ji ba Dan Haka take ya yanke shawarar neman Dattijon tun Daren suyi magana hajjo ma tace”

Idan ka aika kiransa zakuyi magana ka kirani Nima zanyi Masa mgn Dan kada ya qarfafa abin sbd hankalin Fatima umman Najma din ya tashi matuqa da hukuncin dazai yanke.

A asibiti su kawu sai kame kamen zancen ban haquri yakeyiwa mahaifiyar Abbas da qanin babansa Dan mahaifinsa ya rasu Yana Basu hakuri da Basu tabbacin bayan daurin auren gobe za’a zauna ayi magana.
Hajiyar Abbas da ranta yagama mummunan baci ganin yanda kamannin danta ya sauya lokaci guda take ta rufe ido tace wallahi tallahi ko ‘yar gwal ce Naj danta bazai auretaba Kuma bazasu yarda ba saisunyi shari’a dasu dattijon akan wannan dukan da akaiwa Abbas dan kuwa zata saki dukiya iya dukiya sai an hukunsu.

Kawu najin Haka wani irin dunqulallen baqin ciki ya tsaya Masa a zuciya ba Dan qarar datace ba sai fasa auren da akai Wanda dama jikinsa yabasa za’ai hakan.
Danne baqin cikinsa yayi yaso qanin mahaifin Abbas din yabashi dama suyi magana ta maza a fahimci juna idan yaso bayan an daura auren ayi maganar wannan Amma Sam shima abin Bai Masa ba ace anyiwa ango duka a gidansu amarya wannan al’amarin babbane.

Kallon Dattijo alhajin yayi a natse yace”

Alhaji Ibrahim katafi kawai maganar Nan bazata yuyuba yanzu sbd halinda shi Abbas din yake ciki maganar auren Kuma a goben dai gskia bazai yiyuba saidai ko kila gaba.

Shiru Dattijo yayi zuciyarsa na quna da tarin baqin ciki,
Shi shikenan kullum cikin gayyata yake Yana Tara mutane Ana fasa aure har sai yakai ya gayyata ba’a zuwa.
To anyi na qarshe da yardar Allah.

Juyowa sukai suka fice daga asibitin suka tari adaidaita sahu suka shiga Babu me cewa qala dagashi har jamilu Wanda shima fasa auren Bai Masa Dadi ba sbd baiga abin fasa aurenba idan an zauna anyi magana Amma sun dauka zafi har suna maganar qara da shari’a Wanda zaice Dan basusan a Ina akai dukan bane da bazasuma fara kawo maganar qara da shari’ar ba Dan kuwa yanasa ran sojojin Marsha ne sukai dukan bama na Alhaji Alfan ba bare ace da sauki.

Koda suka iso gida Saida Dattijo sukai sallar ishai a masallaci kafin yashiga gida dake danqam da hayaniyar Yan biki dasuka zozzo cikinma da yawa zuriar wasu Basu zoba sbd sunsha zuwa bikin Naj din Ana fasawa shiyasa ba kowane yasamu zuwaba.

Gurin Dadah ya aika jamilu yace yakirata sbd zancen bazai yiyu acikin gidanba dayake da mutane ko Ina.

Dadah dake zaune tana Shan radionta cikin kwanciyar hankali ta kalli jamilun daya fada Mata Dattijo na son mgna da ita ta kalli fuskarsa tsaf taga ba wata annushuwa jikinta yabata ba lafiya Allah yasa ba abinda yasaba faruwa bane,ta kashe radiyon tareda miqewa da hijabinta dake jikinta ta nufi kofa tana tafiya ahankali irin ta tsofin da qafafunsu Basu cika wata isashiyar lafiya ba ta nufi waje batareda kowa yasan ta fitar ba.

Dattijo dake tsaye Yana jiran isowarta Kiran alhaji Alfa yashigo wayarsa dama shima gurin nashi suka nufa ayi maganar gabaki dama Dan Haka Dadah na qarasowa yace”

Dadah muje can gurin Alhaji Alfa ayi maganar sbd Nan akwai mutane yanacan Yana jiranmu.

Dadah najin Haka tun Basu qarasaba take cewa”
Ibrahim maganar auren Naj din ce Babu ko?

Shiru yayi zuciyarsa a jagule Bai amsaba har Saida suka Isa cikin babban palon gidan na baqi suka zauna dama Alfa na palon shida hajjo suna Kiran isowarsu.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107DM 10

MG’s SKINCARE
Ina manyan Mata da manyan yara masu buqatan gyaran jiki da fata akan tabbaci da ingancin kyawu da aikin me kyau kuzo ga mg’s skincare inda sukeda nagartattun sabulai da creams masu kyau da aiki,
mg’s skincare nada black soap dasu molato soap hakama akwai gangariyar sabulu na musamman Mixed na Molato/black soap Wanda hadinsa da aikinsa karshene sbd mun gwada mun tabbatar ????

Akwai Kuma herbal whitening black soap Wanda shima aikinsa na musamman ne,

Saikuma beauty kit gbdy nagyaranjiki su cream dakomai ne acikin shi,

Then akwai bridal kit  shima abu 6 be aciki Wanda sai angwada za’a San kayan MG skincare qarshe ne agurin aiki.

Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call
08064532391
Instagram: glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare
Location:kaduna buh we deliver Nationwide
Delivery is not free buh gamasu sari ko wnd yasiya Kaya dayawa kmn 20k above there will be free delivery+ gift

sannan sunada different varieties of frames gamai siyan daya Koh sari
Sannan muna karban order gamasu hidimar biki kmn dg abinci, snacks,juices nd so on
Kindly chat with us via 08062991549.


Cikin girmama Alfa ya kalli Dadah bayan sun zauna a mutunce yace”

Dadah barka da zuwa ansaki fitowar dare ko¿Sannu da kokari.

Ba dole nafitoba Alhaji Alfa tunda dai Haka Allah ya rubuto Dani na tsufa lafiya da ‘yayana Amma matsalar jikoki na neman sakamun ciwon damuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button