DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Palo suka dawo suka zauna bayan sunyi sallar azahar da akai suka dasa Hira hajjo na daki yau batajin Hira karance karancen Islamic books dinta takeyi.

Da yamma sosai saiga Sarah takawo Mata wasu files da ake buqatan tayiwa signing Nan ta maida hankali kan takardun tana dubawa Sarah na qara koro Mata sauran bayanan ayyukan dasuke zaman jiranta a office din tanason ta sanar da ita Abbas yadawo aikin da kowa yayi tunanin zai ajiye Amma Kuma ganin Hanifa yasa takasa fadar maganar tunda yanzu Naj din surukarsu ce kawo Mata maganar wani ba daidai bane zata Bari sai Takoma office din zata sanar Mata.

Ganin hankalin Naj yakoma kan aiki gabaki daya dama ita abida yasa takeson aikinta sbd shi kadaine zata zauna tayi batareda wani surutu ko hayaniyaba shirun tana aiki Yana bada nutsuwa Dan Haka Hanifa tabarta Takoma kicin gurinsu ruqayyat suna aikin abincin dare dama ita tana aiki cikinsu lokuta da dama sbd tanada sha’awan girke girken.

Sai bayan magriba tagama duba ayyukan da Sarah din takawo Mata suka tashi sukai sallah kafin Sukaci abinci Sarah tayi shirin tafiya gida suka fito tare ta rakota har waje tareda miqa Mata 10k tace tadauka drp na taxi taje gida.
daidai ta juya zata shige ta hango Hannah tafe tun Bata qarasoba tayi wucewarta Dan bazata iya da sauraren maganganuntaba.

Tana Isa daki ta wuce saidatai sallar ishai kafin tayi wanka tayi Shirin bacci takwanta sbd tana jiyo hirarsu Hanifa har lokacin Hannah na sashen.

Washe gari Haka ta wuni tana aikin wasu takardun data saka Sarah kawo Mata tun tanayi sama sama kwanaki suka Dan fara ja kusan tadawo da aikin office dinta gida takeyi saidai Sarah Dake faman Shan yawo tsakanin office da zuwa gidan kullum.
Hajjo data lura da aikin na Sanya Naj din samun nutsuwa sai tafadawa Dad Alfa akan maganar komawar Naj din aiki duk da Bata wani so Naj din Takoma aikinba Amma Haka ta hakura tabari saidai tasan JALAL zaiyi wuya yabari tunda ita din yanzu matarsace.
Dad alfa dakansa yayiwa Marshal magana cikin nasa mamakin yaji Kai tsaye yace abarta taje
Shikuma kawai bayason arinqa nanata Masa maganar auren da nauyinta dake kansa Dan tunda ya dawoma yamanta da maganar auren yake aikinsa da rayuwarsa yanda ya Saba ko tunota sai Yana waya dasu hajjo yakeyi idan sun jeho Masa maganarta.

Ta bangarentama tunda aka Bata damar komawa aiki tafisa mantawa da auren musamman da Dad Alfa ya siya Mata lafiyayyar sabuwar motar datake hawa Dan Haka yanzu aiki takeyi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,
Babu damuwa da tunanin fada da gorin dattijo, Dadah da ummanta akan rashin aure saima kulawa da qauna dasuke nuna Mata a yanzu din Wanda yake na lallabawa kada ta bijire auren ya kwabe lissafi yadawo musu sabo,
Ta bangaren office kuwa yanzu girman datake samu gurin ya zarta na kowa dake ALFAS din sbd yanzu tana amatsayin Matar me company dinne sbd sanin da kowa yayi Marshal shikeda 60% shares a company din.

Abbas duk wani Abu dazai hadasu bayan meetings batabi sbd har lokacin Yana sauran ‘danyar haukarsa atare dashi Dan kuwa kallo yake Mata harna qurulla wani lokacin Kuma harda ‘yan maganganu Amma Bata taba ko kallon inda yakeba Dan dama wannan tun suna tare yasan halinta dabi’artane rashin tankawa da kulawa.
Qarshe sbd nunawa da son nuna rashin gazawarsa da kausar yafara soyayya receptionist dinsu Kuma cikin gaggawa suka fara gabatarda komai lokaci qanqani saigashi Ana sanarwar aurensu Nanda wata biyu masu zuwa.
Duk wannan sha’anin nasane yakeyi shi kadai Dan kuwa ko hankalin saurara Bata badawa idan Sarah na kawo Mata zancen abindayeke faruwa bare ta fahimci menene dinma yake faruwa.

Sosai yanzu takejin dadin rayuwarta Babu takura Babu wani damuwa Haka take gudanarwa,
Kullum zata tashi tayi Shirin office tafito tasa masu aiki suyi Mata abinda takeso taci taredasu hajjo da Hanifa, tafito taje gurin dad Alfa tai Masa gaisuwar safe kafin tafito ta wuce aiki,
Idan tadawo zatai wanka tayi sallah taci abincin tayi baccin yamma kafin tatashi tayi sallar magriba sai suyi firar dare dasu hajjo wani lokacin idan Batai baccin yammaba gidansu take zuwa acan take baccin dakin ummanta kokuma firarta dasu duk da ba itace me firarba Yi akeyi tana Dan amsawa da eh ko aa sai ido datafi sauraron hira dasu.

Ahaka lokaci Mai Dan tsayi yaja tasamu sauyi sosai na jiki da rayuwa Dan kuwa fatarta ayanzu tafi samun qarin hutu da lafiya tareda kyau.
Tayi fresh sosai sbd har wani irin haske take qarawa kullum musamman dayake itama Bata cika Shiga Rana ba Dan rayuwarta bazata iya yaushene zuwanta kasuwaba kokuma siyayya irin gurare masu Rana sosai haka yawanci siyayyarta online shopping takeyi akawo Mata har gida sai idan sunso su fita da Hanifa zuwa manyan malls Haka siyayyan Yan abubuwan amfaninsu kaman su turaruka dasu Mai sai undies da qananun Kaya Haka
Musamman ita Naj indies basa isarta kullum cikin siyansu take.

Gabaki daya rayuwarta ta manta da auren dake kanta sbd rayuwar data samu kanta aciki ta rashin takura shiyasa ta sake sosai tana gudanar da rayuwar yanda takeso.

Kamar dai yanda Dr said yasake hadawa Hanifa appointment da Dr Kenneth a Sweden yanzu lokacin zuwanta ya qaraso Dan Haka suke cikin damuwa musamman Hanifan Wanda tasaka ran samun haihuwa sosai a ranta.
A yanda suka bibiyi likitoci tun shekarun aurensu na farko an tabbatar musu da cewa Hanifa bazata iya daukan ciki da kanta ba ma’ana zaiyi wuya saidai ayi Mata dashensa Wanda ta daga hankalinta sosai tashiga damuwa Suma sumshiga damuwa sbd halindata shiga qarshe akai dashen cikin na wata biyu ya fita shima tashiga wani mawuyacin hali na tashin hankali da shiga qunci da addua da komai aka samu ta dangana tayi tawakkali tadawo daidai saidai sun dibar Mata lokacinda zata dawo asake Mata dashen Wanda shine lokacin yayi yanzu saidai Kuma damuwa da tsoron ko zata samu ko bazata samuba ya Hana zuciyarta sukuni duk yanda takeson danne damuwar kasawa takeyi Wanda yake sake sakawa hajjo tausayinta sbd tana cikin jarabawa ta lalurar lafiya yau gobe Babu ga wannan jarabawa ta rashin samun haihuwa Dan ma tanada tawakkaline soda dama Koda damuwar abin ta taso Mata tana dannewa da rokon sassauci gurin ubangiji gashi a zuriar gidan basuda iyali da yawa sune suke fatar su cika gidan da nasu yayan Amma batajin za’a samu daga gareta kila saidai ‘dan uwanta JALAL.

Damuwar da Hanifa take ciki tasa gidan kusan kowa damuwar yakeji ita kanta Naj din tunda aka tsaida ranar tafiya Sweden din ta nema hutu office ta daina zuwa koyaushe tana tareda Hanifar wadda damuwa tasaka ciwon gefen ciki ya kamata cikin lokaci qanqani ya kwantar da ita Nan hankalinsu yakuma tashi ga tafiyar nata sake qarasowa Dan saura Kwana biyu su wuce wannan karon tareda Naj din zasu sbd zasu hade da Isma’eel acan sai Hannah data nace akan zataje itama sbd ta tabbatarda Marshal zaije can daga Hawaii.

Kwana biyu Ana fama da jikin Hanifan ansamu ta ‘dan ji sauki ta warware Haka suka lallaba suka tafi tareda Dr sa’id din Wanda yake likitanta.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button