DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Miqewa yayi Rai bace ya gyara rigarsa zai fice yace”

Kuma duk abinda kikeyi kiyisa ki hada kayanki anjima Zaki koma gurin hajjon da zama afadawa kowa ba yanzu zata tareba kowa ya watse daga gobe banason zaman tsegumi”
juyawa yayi ya fice daga dakin Rai bace Dan baiyi tunanin zata musanya din ba yanda yasanta da komai yace hakane sbd rashin iya ja’injarta Amma wannan karon zata iya turjewa shiyasa ya rufe idon yayi Mata me gabaki.

Jajir idanuwanta sukai zuciyarta ta dauki wani irin mummunan ‘daci da nauyi dataji tana marmarin mutuwartama Dan kuwa a rayuwa ta Jima tana kunsar baqin cikin maza Dana fashin aure Dana tsangwamar iyaye da ‘yan uwa Amma Bata taba Jin an Mata tozarci da baqin ciki irin wannan,
Aure tsakaninta da Wanda ta girma Wanda yake matsayin qanin Aminyarta ta Yaya ake tunanin tayi aure da rayuwar aure da JALAL Wanda bayan sannu ta gaisuwa Babu abindayake hadasu….

Najma karki damu godiya zakiwa Allah jira da zaman gida ya qare Allah yakawo lokaci kema kin aure,
Tsananin Rabon dake tsakaninkine da JALAL din yake Kore waincan aurarrakin naki da ake fasawa,Rabo ne me qarfi na haihuwa kesa irin wannan auren Dan shi Koda aure ko Babu sai ansamu Rabon Dan Haka muke qara godewa Allah da Akai hadin, Allah ya kawo……Wani irin kukan baqin ciki Mai qarfi ta saki sbd maganganun Dadahn dasuka fasa wani qoqon baqin ciki cikin zuciyarta ta miqe tashige kuryar dakin Dadahn tareda zamewa qasa ta zauna tana wani irin kukan da tunda take rayuwarta Bata taba yinsaba.

Tun abun na Wasa Dadah hankalinta ya tashi da halinda Naj din tashiga saitaji murnarta na Shirin komawa ciki Dan kuwa matuqar Najma taje gaban hajjo ko Alhaji Alfa tana wannan kukan na tashin hankali da zallan baqin ciki zasu iya warware auren sbd gudun damuwarta Dan Haka hankali tashe tasa akai Mata Kiran Dattijo da Umma ta fasa musu kuka tana cewa”

Matuqar Najma taqi wannan auren aka warwareshi to Nima barin gidan Nan zanyi bazan zaunaba dan zuciyata harbewa zatayi da kunyar Alhaji Alfa da hajjo Dan Haka gatanan ki fada Mata gwara ta dangana da wannan tashin hankalin ta rungumi auren.

Ko kallon Najman Dattijo baiyiba ya kalli ummanta yace”

Ki saka Mata hankali cikin kanta tadawo tunaninta Dan kema nasan bazaki so auren ya warwareba Dan idanma ya warware na fada Mata hukuncina bazaiyi Mata Dadi ba Dan bazamu zauna da qatuwar budurwaba kamarta muna rarrashinta akan aure bayanma tuntuni yakamata muyi Mata auren Dole mu huta.

Kallon Najman umma tayi tareda miqewa tsaye ta Isa inda take ta janyo hannunta tana cewa”

Inshallah zata fahimta aure Amma yariga ya dauru ma maganar warwarewa tunda ai Dan an Isa da itane akai Mata auren maganar taje gaban hajjo tana wannan kukan Ni kaina bani ba ita Dan Haka Najma ki nutsu kidawo hankalinki rayuwar aure zakiyi a gidan yanzu ba wadda Kika sababa, su din yanzu dangin mijinkine Kuma kinsan son da suke Miki bazasu taba cutatar dakeba hakama jalal ki yadda ko kiqi yadda mijinkine yanzu bashi girma yazama Dole.

Kinga Fatima jeki da ita can kuyi sauran abinda zakuyi na tsakaninku ganinan zuwa na maidata gurin hajjon da kaina shikenan.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107DM 13
Zaunar da ita bakin gadon dakinta umma tayi tana kallon yanda fuskarta gabaki daya tayi jajir sbd kukan tashin hankali musamman dogon hancinta yafi yin ja ta zauna gefenta tana tausasa murya cikin kulawa da tausayi tareda kewar rabuwa da ita dazatayi duk da kusa suke tace”

Najma Dan Allah ki daina daga hankalinki akan abindaya kamata kiyi farin ciki akansa,
Farin ciki mukeyi kowama shiyake Dan tayaki murnar aure da Allah yabaki ikon Yi Wanda kinsani auren rahamace tunda kin dau lokaci da gwagwarmaya kafin kisamu kiga hakan.,
A shawarance matsayina na mahaifiyarki Ina Baki shawaran karki watsawasu hajjo da Alhaji Alfa qasa a ido kodan tsananin qaunar dasuke Miki wadda itace ta Sanya hakan,
Hakama Yaya kike tunanin Zaki iya kallon Hanifa kice bakyason Dan uwanta datafi so fiyeda komai a duniya wannan tunanin baiyiba ki ajiyesa Anan gida ki barsa zaman qarqashin ikon mijinki zakije kiyi bakida wani majagorancinki bayansa Dan Haka biyayya da bin umarninsa dole ne….

Wannan kalmar tasa wasu hawayen baqin ciki da ciwo masu zafi suka gangaro Mata tana sake sheshekar kuka ahankali, umma taci gaba da cewa”

A umarni Kuma na matsayina na mahaifiyarki Ina Baki umarnin ki aje maganar Araba aure anan ki barta Dan duk ranarda kikaiwa wani acikin gidan Alfa maganar daga ranar zakisan asalin kalan fushi da bacin Raina Dan Haka Dan Allah Najma na rokeki daki dauka dangana kiyi biyayya kaman yanda Kika Saba yiwa qanin mahaifinki Dattijo daya dauki damuwar tsakani da Allah yasakawa kansa akan al’amarinki,
Qanin mahaifinki ne Kuma Miji gareni Ni mahaifiyarki Dan Haka ya cancanta kiyiwa hukunsa biyayya Koba Dadi sbd baitaba nuna banbanci ko gazawaba a tsakaninku da nasa ‘yayan daya Haifa tun bayan rasuwar mahaifinku da wannan biyayyar kawai Zaki iya saka Masa kodan yanda yake Shiga tashin hankali da damuwa ba dare ba Rana aduk lokacinda neman aurenki yasamu matsala Dan Haka kiyi hkr ki dauki dangana Allah ya sanyawa rayuwar auren albarka.

Amin anty Amina tace tana qarawa da nata nasihar da rarrashi Dan kuwa duk Wanda yasan Naj baitaba ganinta a mummunar yanayiba irin yanxu Dan kukan datakeyi harya zama abin kayar da gaba.

Ganin idan aka biyeta sanyi jikin kowa zaiyi yasa aka qyaleta quryar dakin umman ta dunqule a gado cikin mummunan yanayi na qunci da baqin ciki hawaye Kuma sun kasa tsayuwa daga idanuwanta.

Hidimar Wunin biki akaci gaba dayi har dare masu tafiya gida suka tafi akabar baqin nesa kawai wainda Suma washe gari Dattijo yace kowa ya watse yakoma ‘dakinsa.

Mummunan yanayin da Naj din take yasa Dadah tacewa Dattijo yaje ya sanarwa Alhaji Alfa abar Naj din ta kwana gida har gobe tadawo sbd sudai duwarsu da tashin hankalinsu kada hajjo ko Alhajin sugan Naj a wannan halin komai zai iya faruwa Ana fadawa Alhajin yace bakomai abarta ta nutsu tukuna tazo Koda fiyeda goben nema zai fadawa mijin nata,da wannan aka barta gidan ta kwana.

Har safe tana dakin umma Nan takwana ko ganinta batason mutane nayi sbd tsananin kunyar kanta da wannan aure ga idanuwanta dasuka kumbura tsabar kukan data kwana tayi a Daren.

Hanifa na sane taqi zuwa sbd tana gidanta tun jiya da daddare mijinta ya dauketa suka tafi takuma qi kira Dan taji labarin kukan da Naj din keta faman Yi a bakin Anty Amina,
Taji tausayinta matuqa hakama tana iya kwatanta jin yanayi na damuwa da Naj din take ciki na auren Kai tsaye da Wanda ko taqamaimai kalma biyar Bata taba shiga tsakaninsu ba duk suka hadu tsawon shekaru kuwa Dan Haka take tausayin Naj din ga sanin halin JALAL datai na tsagwaron kamewa da basarwa Dan kuwa kafin Naj taganewa komai sai anga wuya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button