DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107[1/14, 3:33 PM] +234 901 771 2720: DM 11
Acikin Daren Koda hajjo tadawo palonta Hanifa na zaune Palo tana waya da Isma’eel dinta dazai qaraso goben tunda safe sbd yasamu daurin auren cikin sanyin jiki Dana murya tareda damuwa tace”

Zawj ko yanzu wannan karon Babu auren Naj.

Subhanallh”yace cikin mamaki da firgici yace”

Meya faru Kuma wannan karon?
Yaya Naj din tana lafiya kuwa?
Innalillahi Wannan labarin bamai Dadi bane.

Kasa cewa komai tayi saima damuwarta akan Naj dake qaruwa sbd wannan karon Naj din abinda Abbas yayi ya daki zuciyarta Dan ba’a taba cin Mata mutunciba kamar Haka yaga Mata sutura a waje dasu Hanifan da ummanta Basu isoba alokacin batasan Yaya zatayiba da jikinta.

Ko palon hajjo Bata zaunaba ta nufi dakinta ruqayyat dake jiran dawowarta tayi Mata gashin qafafunta Wanda ake Mata kullum da daddare kafin ta kwanta sbd nauyin qafafu tana ganin hajjon ta shige taje ta dauko kayan aikin zata nufi dakin Hanifa ta tsayar da ita ta karba kayan tana cewa”

Jeki Zan Mata da kaina.

Karaban kayan tayi ta tura kofar dakin ta shige ta tadda hajjo zaune tasake ajiyar zuciya sai alokacin taji nutsuwa da fushinta ya sauka sbd koba komai shikenan Naj din tazama tasu ta har abada Babu me sake takurawa rayuwarta ta bangare daya Kuma tuno jalal da irin girman miskilancinsa da Kuma yanda girman matsayi yasamesa a cikin shekarunsa na samartaka dan Haka ba lallai hadin nasu yayi ba Dan kuwa shi yanzu yaro da kudine abokin manya itakuma idan ba Allah ya rufa asiriba kallon qani zatamai Wanda zai kawo musu matsala a tarayyar Amma dai koma yayane za’ai auren Kuma Inshallah zai zama alkhairi hakama bazasu takurasuba ko bayan auren za’a barsu ahankali komai zai daidaita Dan Haka ita ko ahakan komai yayi Mata.

Kallon Hanifa tayi tana nuna Mata kusa da ita tace”

Zo ki zauna kusa Dani mu Taya juna murna da Allah ya Sanya alkhairi sbd kema Zakiyi sirika a goben amatsayinki na yayar ango.

Hanifa Bata gane me hajjon ke nufiba ta qaraso ta aje kayan hannunta tana zama gefenta tace”

Naji dadin da auren Abbas da Naj Bai yiyuba Amma hajjo ai bazamuyi murna ba Kuma tunda Naj din na cikin damuwa duk da itama nasan Bata fasa auren bace ta abin daya faru ne.

Tunda safiyar ranar ta waye sai alokacin hajjo ta Dan saki guntun murmushi tana miqar da qafafunta kan qaramin sofa table dake gabanta tana cewa”

Gasamun qafafun ko da Dan sakemin gobe nasamu damar Dan zagayawa dasu cikin gidan kodan jama’a
Gobe Allah yayi damuwarmu akan rashin zuwan Marshal ta qare Dan kuwa yanzu tunda yanada Mata anan taredamu Dole zai ringa zuwa,
Mahaifinki ya nemawa Marshal auren Naj a Daren Nan Dan Haka ankai qarshen duk wata fitina gobe da Marsha za’a daurawa Najma aure Aminyarki ta zama sirikarki yanzu ita din tamuce halak malak.

Ruwan zafin da ba’a sirkaba ta tsunduma qafar hajjon aciki sbd rudewa cikin mamaki dason tabbatarwa tace”

Hajjo Aure tsakanin Naj da marshal??

Zare qafa hajjo tayi tana cewa”

Qonani kike Shirin yine kome?
Bari Naga auren nasu harma da ‘yayansu idan Allah yace kafin ki qona qafafun na rasa na zuwa.

Da dai hajjo tayiwa Hanifan bayanin komai Jin tayi wani farin ciki da Bata tabajinsaba anan kusa ya dabaibata tako Ina duk da can qasan zuciyarta tanajin akwai qalubale a tsakanin yardarsu da auren su biyun Dan kuwa Babu me sauqin saukowa wani acikinsu ga maganar aurensa da Hannah gefe daya Amma Kuma tana danne hakan da farin cikin hadin Dan kuwa wannan shine perfect match agurinta ita da Marshal dinta da Naj dinta
Miqewa tayi tana cewa”

Alhamdulillah ya Allah mungode maka da wannan zabi naka.

Ficewa tayi da sauri ta nufa dakinsu da Naj din take kwance tayi sallah ta saka kayan bacci tayi kwanciyarta da gudunta taqarasa ta fada kanta tareda rungumeta tana cewa”

I love you Naj
I love you Naj

Da idanuwanta dasukai laushi ta Dan kalli Hanifan tana maidasu ta lumshe batareda tace komaiba sbd har tafara Jin bacci sai kawai ta maida idanuwan ta rufe da muryarta me taushi tace”

I love you too Amma bacci nakeji barni Dan Allah.

Dariya Hanifan ta Dan sake cikin tsananin farin ciki tace”

Yi baccinki Lafiya MRS DEEN MARSHAL ALFA.

Bataji abinda Hanifan taceba sbd baccin daya fizgeta.
Daganan Hanifa fita tayi dakin Takoma palo ta miqe a kujera ta Danna Kiran mijinta tafada Masa Nan take cikin Daren tafara Dora sabbin shirye shiryen komai danma kamar yanda hajjo tafada Mata a yanke auren kawai za’a daura baza’a daga maganar takurasu tarewaba yanzu sai kowannensu ya Dan nutsu Dan wannan alamari na gaggawar daya riskesu musamman sbd yanayi na yanda suke kallon junansu na tazarar shekarun.

Ta bangaren ummanta da anty Amina kuwa a Daren Basu rintsa ba sbd tsananin damuwa da rashin sanin mezai faru mezai biyo baya ga Dattijo har lokacin umman Bata sake sakashi a ido ba bare tasan da maganar auren a gobe ko babu ga anty Amina zuwanta biyu yinin tana dubo Naj Wanda tunda abun yafaru take daki kwance Bata buqatan ko tada maganar ayi.

Koda akai sallar asuba kusan daga Dadah har Dattijo da Hanifa Basu rintsaba sbd zumudin safiya tayi ta waye a daura auren Nan kada wani abun ya gitta afasa Dan Haka daqyar kowannensu yaga anyi sallar asuba gari ya waye aka hau sabuwar hidima gadan gadan.


Tsaye yake daga bakin qatoton window na cikin geam room dinsa dake cikin flat dinsa Wanda Babu kalar tsadadden lafiyayyan geaming machine dinda Babu aciki Wanda duk inda yake yasaba amfani dasu shiyasa jikinsa kallo daya macen datasan asalin jikin namiji me kyau qaqqarfa bazataji ta mutu a sonsaba take musamman idan tsautsayi yasa kasamu ganinsa ba riga.

Tsaye yake Yana amsa waya sanyeda black three quarter da black armless riga Wanda suka fidda hasken fatarsa sosai dama Kuma black shine kalar kayan dayafi so kila Kiran kalar tana Masa tsananin kyau ne.

Gama wayar yayi daidai knocking kofarsa da akai Wanda hanifa ce kawai yasan tana zuwa ta buga kofarsa Kai tsaye saidai akirasa a waya sbd sanin shi ba mutum bane Mai son hayaniya.

Kashe wayar yayi ya fito daga geam room din ya nufi Palo ya ajiye wayarsa akan kujera ya nufi kofar cikin nutsuwa ya saka hannu ya bude tareda juyawa Yana cewa”

Menene Kuma tunda safe Nan?kinsan bana ganin kowa fa tunda safe is too early now Hanifa.

Muryar Dad Alfa yaji yace”

Munsani Marshal Deen Dan hakan before anything ma we are really sorry to disturb.

Waiwayowa yayi tareda kallon Hanifa dake gefen dad din kafin ya maida kallonsa kan dad din ya na Nuna Masa kujera Yana cewa”

Sorry Dad banyi tunanin ganinkaba Ina tunanin haniface sbd itace tafi iya damuwa musamman da safe.

Zama yayi bayan dad din ya zauna Yana cewa”

Good morning Dad antashi lfy?

Lfy Alhmdlh.

Hanifa ya kalla ahankali yace mata”
Gud morning madam.

Murmushi tayi tana ajiye kayan data riqowa dad tana miqewa tsaye da farin ciki shimfide kan fuskarta ta kalli qafafunsa dake sanye da slippers na Gucci farare tas kaman baya tafiya dasu sai qafafun Naj dake tsaf fes fes Kamar hakan suka fado mata tace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button