DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Jiki a mace suka bar gurin suka fice gabaki daya Kai tsaye suka shige gidansu Hanifan Wanda gabaki daya Anguwar Babu kamarsa ga girma da kyau dakuma wani irin tsaro na musamman na sojoji Dan cikin gidan ma gate biyu kafin ka Isa ainihin cikin harabar gidan Wanda ke daukeda motoci na alfarma wainda ake sauyawa akai akai kusan guda shida a ajiye,
Uku na Marshal ne sai guda daya ta Dad dinsu sai daya ta Hanifan ce dayar Kuma ta hajjo ce wadda Bata cika hawa ba sbd Bata fita Sam Sam sai Dole Kuma driver ne yake tuqa ta,
Hanifa ma Sam Bata Jan mota sai Dole sbd yanayinta Wanda yasa dad dinta dashi marshal din suka qarfafa dokan rashin tuqin itama driver ne da ita sai Kuma idan zasu fita da Naj sai Naj din tayi driving.

Suna Shiga qaton palon su ruqayyat da Khadija dake palon suna gyaran yamma Wanda yake kamar Dole koba komai qaida sai sunyi gyaran safe Dana yamma suka Dan durqusa suna musu sannu da shigowo.

Kai tsaye palon dazai isar dasu dakin hajjo suka nufa suna shiga tana zaune makeken palonta me ado na qyallin arzikin duniya da Allah yabasu sanyin ac Dana qamshin turarukan wutan umman Naj daya Gama Kama koina na palon kujeru da curtains duk qamshin sukeyi me Dadi da sanyi
‘yar dattijuwar na zaune fara tas da ita me zubin hasken larabawa tana sanye da doguwar jallabiyar mutanen Kuwait me Fadi tana dagowa ta kallesu tasaki wani irin nutsatsen murmushi tana kallon kyakkyawar fuskar Naj da ako yaushe take sanyata murmushi Dan Kamar yanda take tsananin so da kaunar Jokokinta biyu rak Haka take tsananin so da kaunar Naj din musamman daya zama Naj din tazama tamkar jinin gidan itama danma Naj din taqi dawowa gurinta gabaki daya saidai yau ta kwana gidan jibi Kuma tace gidansu zata kwana danma Allah yasa Hanifa ko bayan datai aure Bata barsuba tana nan gidan saidai idan Isma’eel yazo gari ya dauketa su koma gidansu Yana komawa ta dawo Nan gida sbd duk da akwai Yan aikinta Hanifan hankalinsa Bai kwantaba daya barta ita kadai da masu aiki Dan yanayinta.

Zama gefen hajjo Naj tayi tareda kwantawa ta kwantar da kanta kan cinyar hajjon ta lumshe fararen idanuwanta tana sauke ajiyar zuciya ahankali tace”

Hajjona yau akan shimfidarki zanyi bacci.

Shafa kanta hajjo tayi cikin kulawa tace”

Kiyi hkr NAJMA kinji komai lokacine dashi rashin aure ba wata mummunar kaddara bace idan su dadan sun gaji da zamanki a gidan Ni subani inaso.

Murmushi kawai Naj din tayi tana cewa”

Hajjo idan aka baki Ni kema Zaki gaji da zamana ba aure wataran.

Murmushi kawai hajjon tayi tana kallon Hanifa da duk yanayinta bayada Dadi har lokacin akan fadan Dada Wanda akwai cin zarafi masu ‘daci da yawa aciki.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,
Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107
[1/9, 7:53 PM] +234 901 554 3771: DEEN MARSHAL
Mamuhgee

4
Anan gurin hajjo tayi niyar kwana Dan Haka Babu wata damuwa Kamar yanda tasaba rayuwarta na rashin riqe damuwan Abu ta sakewarta musamman dayake tanada daki daki me zamanta agidan a cikin babban palon hajjon wanda dakin Babu abin daya rasa najin Dadi da tsari musamman irin na rashin hayaniya da akasan Naj din batada ita Wanda hanifa ma anan dakin take yanzu idan tana gidan sbd tabaro part dinsu Dad dinsu tunda Babu kowa a part din.
Tanada Yan wasu kayan sawa a gidan Dan Haka Kai tsaye bayan sun Gama cin abincin dare Bata tsaya doguwar Hira ba Shirin bacci tayi bayan tayi sallah ta kwanta sai lokacin tabi misscalls din Sarah da Kira cikin nutsuwa tagama sauraran bayananta na aikin data bar Mata kafin ta Dora da cewa”

Ummm Naj dazu bayan tafiyarki Abaas yasake dawowa yasa an fiddo Masa da dukkanin record dinmu na aiki tun na January ya soke wasu daga ciki tareda fidda Kura kuren dazasu Iya bamu matsala Kuma Yana maganar a sauyani daga gurinki.

Dan sanyi muryarta tayi cikin bayyanarda rashin Jin dadinta tace”

Naj kiyi magana dashi please abarni agurinki sbd Ina barin gurinki na tabbatarda korata aikin zaiyi gabaki daya.

Ajiyar zuciya Me sanyi Naj din ta sauke tana tareda bude Baki cikin muryarta me Dadi Kai tsaye tace”

Karki damu zanyi magana dashi gobe
Kawai dai ki ringa kiyaye Masa tunda Kinga yanayin kalar fushinsa baya tunani me kyau idan ransa ya baci.

thank you Naj.

Ok then see you tomorrow”Naj din tafada tana kashe wayar tareda ajewa gefe tana Dan zamewa daga jingine datake akan gadon ta kwanta tana lumshe fararen idanuwanta ta rufe tana Dan yin bacci.

Hanifa dake zaune tana kokarin Kiran wayar mijinta tana sauraron wayar da Naj din keyi ta Dan saki guntin tsokin baqin cikin Abaas din datakeson koyawa zuciyarta Aminta dashi amatsayin mijin ‘yar uwar tata tun yanzu.
Kashe wayarta tayi tareda miqewa ta zagayo tahau gadon ta kwanta tunda takasa samun Isma’eel din ga Naj shegen miskilancinta wani lokacin baya barinsu yin wata doguwar fira.

Qarfe 8 na safe ta fito wanka daure da towel me kauri tanaji wayarta na ringing Taki ko kallon inda take ta nufi gaban madubi tafara shafa Mai Wanda dama kusan komai product daya suke amfani dashi itada Hanifan.
Shiryawa tayi cikin doguwar riga maroon ta daura qaramin gyale akanta ta fito tana qamshin turaren Vivian rosalle har lokacin Hanifa na kwance sbd ciwon wuya data tashi dashi Wanda dama kullum cikin ciwuka take sbd sikla ce lafiyarta qarantacciyace sun Saba da rauninta shiyasa qaninta marshal baida wani abinda yafi komai so a duniyarsa bayan ita sai kakarsa tukuna mahaifinsa.

Dakin hajjo tafara zuwa har lokacin hajjon Bata farka ba itama Dan Haka Kai tsaye ta wuce kitchen su ruqayyat na ganinta cikin girmamawa sukace”

Ina kwana Anty.

Lafiya kalau ruqayyat
Please ku hado breakfast din Hanifa akawo daki batajin dadi.

Fridge ta qarasa ta bude ta dauko madara ta zuba a cup tareda zuba ruwan zafi aciki tayi dumi ta zuba Zuma kadan aciki ta dauka ta shanye ahankali tareda aje cup din ta koma ta diba dabino uku taci ta fice daga kicin din su ruqayyat suka bita da kallo Kamar dai yanda suka Saba sbd mamakinta har kullum Baya sakinsu na yanda take komai nata cikin wani irin burgewa da qaidojinta da nata ita ta shardantawa kanta su sbd maintaining rayuwarta.

Kalar abincin datake duk da gidansu ba masu halineba ta qayyade abinda take ciwa cikinta Wanda yake kamar dieting ne takewa kanta sbd gabaki daya rayuwarta batason abinci me nauyi tun tana yarinya Haka take idan taci abinci me nauyi sosai Yana wahalar da ita shiyasa data girma ta San yancin kanta tanada abubuwan datake ci kawai da wainda bataci Wanda shima yake qara bayyanarda miskilancinta da burgewarta da wasu ke gani acikin gidansu kuwa suna daukan hakan amatsayin nuna wayewa da nuna kudi Wanda yasa mazan ke ganin tafi karfinsu Ana samun matsalar fasa aurenta Kashi Kashi Kuma Sam Bata nuna damuwar hakan shiyasama ta tabbata dai itace Bata tashi aurenba inji su Dadah da Dattijo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button