DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Thanks.

Sai alokacin ta kalla anty Amina tana cigaba daci suna gaisawa anty Amina na kallonta dakyau cikin nazari tace”

Naj bakida lafiyane Naga kamar kin fada.

Kallonta Hanifa tayi tana cewa”

Ramar aikice Amma duk da hakan Ni Banga ramarba haske dai Naga tayi sosai kodai bakida jini ne Naj?” Taqarasa fada tana Dan zare ido.

Batareda ta dagoba tace”

Lafiyata kalau stress ne kawai amma zanshiga hutu sbd komai yakoma yanda yake a office din Inshallah.

Saidata qoshi kafin ta qarasa dakinta tabarsu a palon ta tube ta shiga toilet wanka.
Sai datai wankan taji jikinta ya sake sosai ta fito daureda towel ta nufa jikin mirror kenan taji wayarta na ringing ta juyo ta nufa wayar dake Kan gado ta dauka sai kawai taga No din qasar waje destination id dinta ya nuna Mata United States of America.

Kai tsaye ta dauka batareda ta tsaye tantance kiranba Wanda yake Vidcall sai ganin mutum tayi ya bayyana kan screen din wayarta Yana zaune cikin lafiyayyan palonsa sanyeda uniform dinsa na sojojin America dasukai Masa wani irin kyau uwa uba hutu da nutsuwar daya samu ta bayyana ataredashi Ya zuba Mata fararen idanuwansa har zuwa kirjinta dake daureda towel Tsananin hasken data qara yasashi sake zuba Mata idanuwansa,
wannan ne Karo na farko data gansa cikin uniform ta dauke kainta ganin irin kallon dayake Mata sai alokacin ta tuna da towel ne jikinta ta kashe wayar tana jefarwa Kan gado ta tafi tahau shirinta.

Baccin maraice yayi sai magriba ta tashi ta fito bayan tayi sallar magriba sbd yunwa me tsanani datake ji.
Kicin ta nufa sbd sanin lokacin cin abincin Daren baiyiba tasan Hanifa na kicin sbd Bata jimawa bataci ba shiyasa take zuwa kicin taci ta koshi Kuma ahau dining aci da ita.

Tana Shiga kicin din ba kowa sai ruqayyat dake qarasa aikin abincin Daren ta nufa fridge ta bude ta dauko milk drink tasha sosai ta dauko cake guda hudu ta cinye ta qara da apple biyu kafin taji ta dan samu nutsuwa ta fito suna hadewa da Hanifa dazata Shiga kicin din neman abinda zataci itama tace”

Naj yunwa nakeji cake zanci da Madara tunda kin cunyemun awarar da Umma takawo min dazu.

Batace komaiba Takoma Palo ta zauna tana duba wayarta tana jiran agama abincin akawo dining.

Sallar ishai taje tayi tana fitowa hajjo na fitowa suka dunguma dining Hanifa tuni ta riga kowa Isa.

Naj din ita tazubawa hajjo abinci takawo Mata ruwa da komai ta kalli Hanifa da Bata harta zuba abincinta tafara kaiwa Baki.

Zama tayi itama tareda zubawa ta zauna suna binta da ido ta dago ta kallesu ganin irin kallon dasukewa abincinta yasata kallon abincin sai alokacin taga ta zuba da yawa ba kamar yanda ta Saba ba dama kwanakin gabaki daya cin abincinta ya sauya ta Dan fuske tana cewa”

Yunwa nakeji sosai duk yau banci wani abincin kirkiba.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107

DM 34
Hajjo kallon abincin takuma Yi kafin ta kalli Naj din cikin kulawa da nutsuwa tace”

Najma ki daina zama da yunwa Haka sbd zata iya Miki illa yanzu wannan abincin zai iya qulle Miki ciki,Kisha tea kafin ki ci abincin cikinki ya sake tukuna.
Kallon Hanifa tayi tana cewa”

Miqa Mata tea din ta zuba ta Sha.

Qaramin flask din dake cikeda black tea dinda yaji kayan qamshi da hadinsu lemon da Zuma wanda koyaushe dashi ake jere abincin safe Rana da dare Wanda qaidar hajjo ne wadda ta Saba da Shansa Kuma al’ada da dabi’ar Shan nasa ya Kama duk Wanda yake gidan ko baqi akai idan za’a kawo musu ruwa sai an tambayesa ko akawo Masa tea din.

Miqawa Naj Hanifa tayi tana cewa”

Kin riga kinfara cin abincin kinsha tea din daga baya” ta aje tana daukan spoon tafara cin nata abincin.

Kamar yanda tasaba cin abinci a natse ta cinye abincin tas tasha ruwa kadan ta zuba tea din Wanda kurba daya Tai Masa ta ajiye tana cewa Alhmdlh ahankali.

Kallonta hajjo tayi tana sake cewa”

Idan Zaki ringa zama da yunwa irin Haka Zaki sa ciwofa ya kamaki karki sake hakan daga yau.

Guntun murmushi tasaki ahankali tana kallon Hanifa da har lokacin abincin takeci tace”

Yaune kawai hakan bazai Kara faruwa Inshallah hajjo.

Barin gurin tayi ahankali tanajin nutsuwarta ta dawo ta dawo palo ta zauna sai alokacin ta dauka wayarta tana dubawa har Hanifa da hajjon suka Gama suka baro dining din hajjo tayi dakinta sbd qafafunta da ruqayyat zata gasa Mata da ruwan dumi.
Hanifa Kuma gefenta ta zauna tana daukan tata wayar itama tace”

Naj gobe umma zata faramun sabon gyara Isma’eel zai dawo next week fa.

Juyowa Naj din tayi ta kalleta tana sake maida hankali kan abinda take dubawa a wayar tace”

Shine kike Zillo Haka?
Cemasa zanyi yayi zamansa sai zaki haihu yadawo muga qarshen gyaran.

Dariya Hanifan tasake tana cewa”

Zillo ma ai kadan ne zille zille zanyi ma idan ya dawo tunda bansan kalar zille zillen da matan duniya ke can suna Masa ba tunda bana kusa Dana Haka idan yazo nawa lokacin ne nayi haukama idan Zan iya,
Hannah kina ganin duk ranarda tasamu auren Marshal wannan rawar kan datake ai uwar ubansa zamu gani akan wannan datakeyi Yan…….

Hade sauran maganar tayi tana rufe bakinta Jin Naj din tayi shiru sbd gabaki daya ta manta da Naj take maganar,ta Dan kalli fuskar Naj din data juyo itama ta kalleta tareda sake wani irin guntun murmushi tana basarwa da cewa”

Ashe kinada qarfin yiwa miji zille zillen Kike makure Mana fuska ki nade muna dawainiya da matarsa.

Haba sirikita idan bakiyi hidima daniba waye zaiyi….

Dan kame fuska Naj din tayi Hanifan tasaki dariya tana cewa”

Sorry my Naj.

Wayar Hanifan ce tayi ringing ta waiwayo tana kallon wayar ta maida kallonta kan Naj da kallo daya tayiwa wayar taga sunan me Kira ta dauke tana maida hankali akan tata wayar.

Dauka Hanifa tayi cikin murmushin ganin video call ne ta dauka Kai tsaye tana cewa”

Hey Deen Marshal,ya kake?

Kallonta yayi Yana Dan gyara crossing qafafunsa da yayi wayar na ajiye saiti dashi a gabansa Yana zaune acikin office dinsa sbd sun safiyace har hantsi ma yafara,
Ya bude Baki ahankali yace”

Lafiya kalau,ya baby?
Kinje scanning din kuwa?
Nayi mgna da Dr sa’id,ki turamun scanning din I want to see it.

Ok,ok,Baby is fine,and iam fine also” satar kallon Naj tayi tana cewa”

And Naj ma tana Lafiya.

Jingina yayi baya Yana folding hannuwansa fararen idanuwansa akan wayar cikin muryarsa data Gama Isa cikin kunnuwanta yace”

Bata wayan.

Kallonsa Hanifa tayi tana Dan kame fuska da murmushi akan fuskarta tace”

JALAL karka damu qawata da wannan kamewan naka,
Wani irin kallo yayi Maya Wanda yasata harararsa tana cewa”

Kome ka zama karka manta dai Ni yayarkace.

Dan rufe idanuwansa yayi ya bude da wata muryar yace”

Matan auren dake gefenki Zaki bawa wayar.

Naj dake zaune duk takasa ma qarasa abinda take a waya sbd zancen a bayyane yake fita ta miqe zata bar gurin lokacinda Hanifa ke kokarin miqa Mata wayar Kai tsaye taji muryarsa ba Wasa aciki yace”

Kika bar gurin Zakiyi mamakin hukuncin hakan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button