DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Rintse idanuwansa dasukai wani iri yayi tareda dauke Kai daga wayar bayan ya kashe ya Nemo no din Hanifan yasake Danna Mata wani Kiran wanda ba video ba Amma ba’a daukabaya saki wani guntun numfashi me Dan zafi tana jefar da wayar gefensa Kan kejera ya lumshe idanuwansa ahankali.

Amai tayi Sosai Wanda ya mugun galabaitar da ita ta sake watso ruwan zafi sosai ta fito ta saka Kaya masu kauri sbd zazzabin daya taso Mata ga mutuwar jiki ta Haye gado tareda shigewa bargo tana rufe idanuwanta.

Baccin rashin lafiya ne ya dauketa Koda Hanifa tashigo daukan wayarta Bata tashetaba ta dauka wayar ta fice sai alokacin taga misscall dinsa ta saka kiransa saidai Bai dagaba Dan Haka itama ta wuce daki Kai tsaye tafara Shirin kwanciya tana gamawa ta kwanta.

Washe gari sosai Naj din ta tashi da zazzabi, hankalin hajjo ya ‘dan tashi sbd dama tasan Najma batada lafiya boyewa kawai takeyi sbd duka alamun Bata daidai ya bayyana.

Dr sa’id aka Kira yazo dubata Dan ko abinci daqyar aka samu ta iya ci sai Amai takeyi Wanda duk ya qarar Mata da qarfin jiki.

Koda Dr sa’id ya iso Anty Amina na gidan itama harta shigo duba Naj din Dan Haka itace ta kamota suka fito Palo bayan ta sanyo doguwar hijab akan kayan baccinta.
Zama sukai Dr sa’id ya Dan zubawa Naj din ido Yana yimata kallon tsaf.
Dauke idonsa yayi tareda Ciro paracetamol ya miqawa Hanifa yace”

Inaga Tasha paracetamol sbd wannan Dan zafin zazzabin ya sauka tukuna Dan gskia inaga saitaje asibiti saina dubata acan Dan inason Zan Mata wasu test musan asalin menene yake damunta.

Cikin kulawa hajjo dake kallonta tace”

Babu wani maganin wannan Aman datajeyine?duk qarfinta ya qare,kodai food poison ne yake wahalar da ita?

Eh zai iya yiyuwa hakan ne Amma dai saimun gwadata zamu sani.

Bayan tafiyar Dr sa’id aka kawo Mata abinci taci ko kadan Amma takasa cin komai,
Kallonta Anty Amina tayi tace”

To akwai abinda kikaji Zaki iyacin sai akawo kici ko kadan ne Kisha maganin.

Ahankali tace”

Aban orange drink ma kawai is ok.

Kawo Mata akai Tasha sosai Tasha maganin sai alokacin tasamu damar watsa ruwan zafi tayi salloli kafin ta iyacin white rice da miyar busasshen kifi.

Tana gamawa anty Amina dasu biyun ne kawai suka rage a dakin ta kalleta dakyau hat zuwa yatsin hannayenta dasukai wani irin fresh ta maida kallonta zuwa Kan fuskarta data Dan ciko kadan Kai tsaye cikin mamaki da shakku idanuwanta cikeda kasa boye mamakin tambayar tace”

Naj ciki ne dake?????

Dukan zuciyarta da qarfi maganar tayi harsaida kanta ya Sara ta dago ahankali ta kalli anty Aminan data tsareta da ido a waje tana jiran amsarta ta dauke Kai Yana sauke wani irin numfashi me wahala na gabanta daya dauki faduwa da tambayar sbd Karo na biyu kenan Ana Mata wannan tambayar,Sarah tayi yanzu Kuma Anty Amina.

Girgiza Kai tayi Kai tsaye tace”

Tayaya zakice ciki ajikina Anty Amina.
Cikin fa haihuwa kike mgn,Ina Zan samesa.

Da wani sabon mamakin anty Amina tace”

Kinada Miji kike tambayar Ina Zaki samu Miji duk da dai ansan auren baigama daidaitaba Amma yanayin naki ne da sauye sauyen danaga duk kin samu a Yan kwanakin Nan yasa nayi tunanin hakan sorry.
Duk da hakan kije asibitin gobe Dr yadubaki ciwo Haka batareda kasan menene yake damunka ba Dadi wuya zakiyita Sha.

Gyada Kai tayi ahankali zuciyarta na wani irin daukan nauyi da maganar Anty Aminan ta farko,
Ta Yaya za’a ringa tunanin ciki ajikinta?
Shin ciki zai iya shigartane a mu’amala biyu da akai bama da so ko yardartaba?
Rufe idonta dasuka sauya tayi tana girgiza Kai da cewan bazai yiyuba wannan masiface me girma,
Aa aa Bata fata, Allah ya tsareta daga wannan abun kunyar me girmanda bazata taba iya kallon ko kanta a madubi ba bare wani.

Bayan tafiyar Anty Amina daurewa tayi ta cije tafara nuna tasamu sauki Sosai sbd abar wani maganar zuwa asibitin Dan kuwa da kanta zata samu zuwa asibitin ita kadai saita fara Jin abinda yake damunta.

Haka ta tilastawa kanta dauriyar ciwon Wanda take matuqar jinsa Amma ta daure tana kannewa ta nuna taji sauki Sosai da wannan tasa aka bar zancen zuwanta asibiti har aka kwana biyu anty Amina ma data saka Mata ido Dan ta basar da ita akan zancen kullum tare suke zuwa gidan da Hanifa gurin gyara da ake Mata na zuwan Isma’eel itama wani lokacin takanyi wani lokacin Kuma batayi sbd qamshin su kurkum da bataso.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107

DM 37
A gidansu duk wani Abu dazai sake bawa Anty Amina damar sake saka ido akanta tana kokarin kauce Masa
Sbd gabaki dayama ta rasa tunanin Yi abinda dai tasani shine cikin Marshal ajikinta bazai zama gskia ba.

Washe garin ranarda taji abun yafara Mata yawa ta yanke shawaran komawa aiki ranar Isma’eel ya dawo suna zaune Palo tareda hajjo Hanifa na daki tana sake shiryawa ya iso da sallama ya shigo palon bayan ruqayyat taje ta bude Masa kofa ya qaraso fuskarsa daukeda murmushi ya nema gurin ya zauna Yana gaida hajjo cikin tsananin girmamawa
Naj kuwa kallonsa tayi murmushi akan fuskarta tace”

Sannu da dawowa dadyn baby da maman babyn.

Dariya yayi Yana kallonta yace”

Sannu da zaman hutawa Amarya Kuma uwar gidan Marshal,
Hajjo ta daure Miki kina zuba ikonki akan Marshal.

Basarwa tayi tareda sauya zancen da cewa”

Yanzu dauke matarka zakayi ko kunyar hajjo bakwaji.

Satar kallon hajjo dake duba sako a waya yayi Yana maida da kallonsa kanta Yana hadiye dariyarsa Dan kuwa ta shammacesa agaban hajjon yace”

Zan Rama ne kinci bashi Naj.

Murmushi tayi tana maida kallonta kan Hanifa data fito cikin Ado sai daukan ido takeyi sbd fatarta datai kyau Tasha gyaran umma dakuma cikin daya qara Mata kyau sbd ya fito sosai.

Zaunawa tayi tana Masa sannu da isowa daganan suka koma dayar palon hajjo kafin aka gama jere abinci Sukaci abincin dare kafin suka wuce Naj din ta rakasu har mota bayan Isma’eel yaje gurin Dad Alfa ya dade Kuma acan din suna mgna.

Bayan tafiyarsu a hanyarta takomawa sashensu ta hadu da mum Malika da Hannah zasu nufa part din zuwa gurin hajjo
Mum Malika na ganin Naj din ta zuba Mata ido tana Dan bude idanuwanta akanta sosai tana qare Mata kallo a sirrance,
Dan shiga tunani tayi tana sake kallon Naj har Naj din ta iso gabansu cikin nutsuwa tace”

Barka da maraice mum Malika.

Washe Baki mum din tayi tana Dan dawowa daga tunanin data shiga ta kalli Naj din suna qarasawa tace”

Naj Yaya kike?yaya jikin naki kinji sauki kuwa?
Ki daure kije asibiti,idanma bakyason zuwa akwai wani babban likita Dan uwan baban Hannah dake Nan ko Zan kirasa yazo ya dubaki harma da kayan dibar samples na awon idan ya Kama kokuma Hannah ma zata iya kaiki ki gansa.

Da Dan wani yanayi na kame fuska Naj din ta kalli mum din kadan kafin ta dauke Kai batareda ko inda Hannah take ta kallaba tace”

No thank you mum Malika ba buqatan hakan,Dr sa’id ma ya Isa.

Wucewa take kokarin Yi Hannah da tuni Naj din tagama isarta data bar gurin ta daga wayarta tana dorawa a kunne tace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button