DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Thank you” ya furtawa Dr sa’id din Yana juyawa shikuma ya fada mota ya fice jikinsa a mace Dan kuwa Deen Marshal ba namijin da mace zata iya rabuwa dashi bane duk da yasan Naj dinma Babu Wanda zai sameta yayi gangancin rabuwa da ita idanba Abbas da Allah yayi Mara rabo ba a duniya.

Da kansa yabata maganin Tasha ya maidata ta kwanta baccin wahala na sake daukanta ya miqe yakoma kan sofa Yana duba saqonni a laptop dinsa daya dawo da ita jiya daya dawo.

Yana buqatan komawa Hawaii zuwa jibi Dan aikin dayake gabansa dakuma tafiyar dazasuyi Cyprus akan wasu sabbin sojojinsu da za’a qaddamar….
Dagowa yayi ahankali ya kalli gadon datake kwancen tana bacci ya Dan zubawa fuskarta datake kumbure ido ya Dan lumshe idon Yana daukesu daga kanta Yana rufe laptop din ya miqe ya fice zuwa balcony dinsa na qatoton windown dakinsa Yana amsa wayar Hanifa dake tambayarsa Naj ya bude Baki a natse Kai tsaye yace”

Tana bacci batada lafiya ne?

Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa”

Please Marshal ka kuka da ita tanada rauni.

Yaya jikinki?
Fatan keda babyn lfy?

Murmushi tayi Jin ya basar da zancenta Wanda tasan lokacin amsarta ne baida hakan Kuma na nuni da itace kenan zata fada Masa abin daya kamata da matarsa.

Kashe wayarta tayi tana cewa”

Ku kula da kanku I love you both bye.

Sai bayan sallar azahar sosai Ana gaf da la’asar ta farka lokacin zazzabin ya rage tasake yin wanka da ruwan zafi sosai ta fito tayi sallar azahar tana kokarin miqewa yashigo ta dauke Kai daga kallonsa tana komawa bakin gadon Bata qarasa zamaba ya dauketa Yana cewa”

Zo kici abinci tunda kinyi sallah.

Abincin da Hanifa ta Aiko musu ya zuba Mata white rice da kidney sauce dataji kidney din sosai dasu carrot ta miqe tana cewa Bata ci
Ya janyota tana qwacewa cikin masifa da qyar yasa taci kadan Tasha tea me zafi sosai takuma Shan magani batareda ta kalli duk inda yakeba tabar gurin tana tafiya ahankali ta Isa daki ta dauka hijab din datagama sallah tasaka ta fito tana Shirin nufar kofa ya rungumota ta baya Yana sauke ajiyar zuciya a hankali yakai fuskarsa Kan wuyanta Yana cewa”

Karkiyi wahalan tafiya Zaki qarawa kanki ciwone basai kintafiba nasan irin fushi da masifan dake cinki zo ki zauna ki huta idan kin warke Zaki iya sauke duka fushinki ba damuwa bane.

Daukanta yayi yadawo da ita palon ya zauna Yana kwantar da ita a jikinsa yace”

Ki daina Bata ranki Babu Wanda zaisan me qanin qawarki yamiki bare a rainaki Kiji kunya nasan duk wannan ne damuwar ko???” Yafada Yana shinshina wuyanta da sauke Mata numshinsa me dumi da qamshi tanajin hannunsa na yawo Kan shafaffen cikinta Yana shafawa tafara kokarin miqewa ya riqeda Yana kwantar da kansa a bayanta.

Yamma nasake dosowa zazzabinta ya dawo me qarfi ya sake Bata magani tareda kwantar da ita cikin jikinsa ya rufe zafin jikinta na shiga jikinsa nasa Dan daga ita sai qaramar shimin daya Sanya Mata kuka yadawo sabo dama Kuma tunda garin ya waye take tsiyayar hawaye Bata dainaba baqin cikin duniya ganin takeyi yau yaqare acikin zuciyarta da rayuwarta datake ganin ta rushe saidai har cikin ranta bazata iya wannan rayuwarba dashi sbd Babu Randa matsayinsa na qanin qawarta zai goge a ranta yanzu Kuma yakai kololuwar wuce hurumin haquri da juriyarta Dan Haka yakai maqura bazata Bari wannan abin daya faruba yabasa damar ji da daukan kansa cikakken miji me iko agareta,
Bazata Bari yasake samun wannan damarba dan Haka ya dauka hakan amatsayin kuskure zata sanarda iyayensu araba auren kawai Koda hakan zai kawo bacin Rai tasan zai wuce.

Koda gari ya waye ta bude idanuwanta akan fuskarsa suka sauka ta juyar da Kai tana cire jikinta daga nasa ta sauka Kan gadon tareda ficewa dakin ta koma dayan dakin tayi sallah tahirya cikin hijab ta fito palon da niyar ficewa saigashi tagansa a tsaye cikin jallabiya da waya da laptop dinsa a hannu sai key din mota ya kalleta da fararen idanuwansa kafin ya tako ahankali ya qaraso gabanta Yana kallon fuskarta ya ranqwafa ahankali yakai bakinsa saitin kunnenta ya furta”

Yanzune kike Kama da matan sure cikkaki Dan Haka be very careful idan bana nan,
Maganar aikinki Kuma Zaki iya komawa kafin wani dalilin na hanaki zuwa ya bayyana.

Kallo ma Bata samu damar binsa dashiba ta nufi kofar ta fice Allah yasa driver zai jasu Dan Haka tana fitowa motar ta nufa ta shige Koda yafito fuskarsa a matuqar kame sai zuba qamshi da kwarjini yake kamar bashine yagama maganaba aciki yanzu ta hade fuska sosai tana kallon gefe harya shigo aka tada motar suka bar gidan Babu Wanda yasake magana acikinsu suna barin anguwar suka hau titi ta bude Baki tareda Dan kallon drivern ta dauke Kai tana cewa”

Kayi parking Zan sauka anan.

Ta madubi ya kalla uban gidansa yaga ko kallonsa baiyiba yasan ba wannan maganar Dan hakan Bai tsayaba yaci gaba da tafiya har Saida suka Kai gida ta kallesa cikin bacin Rai zatai magana Deen din ya waiwayo ya kalleta Kai tsaye yace”

Bakya gane shiru ne idan anmiki?
Koba yau ba duk ranarda na samu labarin anganki a hanya bazaki Kuma marmarin ko fita ba.

Anayin parking ta fito ta daidai fitowar Hannah zata fita a mota ta gansu zuciyarta na wata irin bugawa da ganinsu tare suda akace musu Naj tayi tafiyar aiki tareda Sarah ko hajjo ma Haka Hanifa ta fada Mata to daga Ina suka hadu suke tahowa gida tare da sassafen Nan bayan shi Daren yau jirginsa zai tashi na komawa.

Dannewa tayi tana qarasowa gurinsa cikin wani irin yanayi na Jan hankali tana cewa”

Good morning my Zawj.

Kota kansu batabiba tayi hanyar sashen hajjo tana tafiya ahankali Dan har lokacin Bata Gama warkewaba.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107

DM 28
Da wani irin kallo yabi bayanta da fitinannin idanunsa Yana karewa tafiyar datakeyi ahankali kallo wadda ke sake tabbatar Masa da ita din tasace tako ina,wannan hurumin nasane iya shi daya.
Saidata shige ya dan sake kamewa Yana kallon Hannah kadan wadda tagama shagwabe Masa tana cewa”

A hanya ka hadu da Naj ne ka rage Mata Hanya?
Sbd nasan dai cewan tayi tafiyane tareda secretary dinta yakamata ace tare suka dawo.

Wucewa yayi hanyar sashensa batareda ya Bata amsar tambayar dataiba cikin muryarsa datake bayyanarda kamewarsa Yana tafiya tana biye dashi yace”

Tambayan nada mahimmanci ne?

Zatai mgna ya bude kofar palonsa tareda waiwayowa kadan sai alokacin ya kalleta dakyau tana sanyeda Gucci pencil jeans da farar long sleeves me yankakken hannu sai scarf qarami dake kanta daure ya dauke Kai Yana nuna Mata kofar da ido da alamar kosawa da ita yace”

Kinada abin yi ne idan kinbini ciki?

Dakatawa tayi tana kallonsa cikin tsananin sonsa dayasa Sam batajin haushi ko zafin duk abinda zai Mata ta saki wani yalwataccen murmushi tana kashe Masa ido daya tace”

A yanzu dai banidashi Amma zuwa gaba nice nakeda abinyi aciki
Zan fita,bye,take care I love you.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button