DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Sake fashewa tayi da wani kukan tana cewa”

Ni koma menene Dan Allah Araba auren Nan…..

Wani irin salatin Dadah sukaji data shigo tana kallon Najman bakinta na rawa gurin magana saikuma kawai ta fashe da kuka tana cewa”

Innalillahi-wainna ilaihirrajiun
Wace masifar ce zata kunno Kai rayuwarki Najma,
Wace tsanace kikewa wannan auren dako shekara daya baiyiba za’a kidawo zawarci,
Najma Dan Allah ki duba tsufana da mutuncin Dattijo ki hakura ki cirewa ranki masifa ki runguma aurenki….

Irin kukan da Najma da Dadah keyi yasa umman sake Shiga wata mummunar damuwa da baqin ciki ta tashi cikin tsananin fushi tayi Kan Naj din Hanifa da duk hankalinta itama ya tashi ta tashi da sauri ta janye Naj din tana kasa mgna sbd ganin cikin qanqanin lokaci Abu yazama tashin hankali.

Ba shiri Dadah tasa aka Kira Mata Dattijo tun kafin ya qaraso sashen yake jiyo fadan umma da ranta yayi mummunan baci qololuwa dakuma kukan dadah daya Gama daga hankalin kowa.

Anty Amina ce tayi Masa bayanin abin Dake faruwa tana dasa Aya ya kalli Naj cikin tsananin bacin Rai da baqin cikin daya rasa abin dazai Mata
Tana durqushe gefe har lokacin kuka takeyi me qarfi na rashin sanin mafitar abindayake cin ranta.

Kallon umma yayi cikin fushi da bacin Rai me tsanani yace”

Najma dai takai matakinda tafi qarfin umarnina Dan Haka ke dakika haifeta bakifi qarfin umarnin nawaba saiki shirya kayanki dan wallahi tallahi tana dawowa gidan Nan da sunan aurenta ya mutu bazata zaunaba tare zaku bar gidan nan.

Kallonsa umman tayi cikin baqin cikin koyaushe yayanta sukai laifi aurentane yake barazanar rawa,
Ta maida kallonta kan Najma tace”

Kinji ai saikije ki hado kayan naki mubi duniya tunda shine sakamakon dazaki bani.

Dadah cikin kula tace”

Najma Dan Allah ki dubi girman Allah kiyi hkr ki dangana wlh na zubarda makaman yaqina na yarda anmiki ba daidaiba ki dangana ki runguma aurenki wlh gaba Zakiyi farin ciki da yardar Allah.

Cikin fushi Dattijo yace”
Ki daina rarrashinta Dadah wlh ko ta tashi ta fice Kona nema mugun ice nai Mata dukan da bazata iya komawa da qafafuwantaba.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107

DM 33
Janyeta anty Amina da Hanifa sukayi ta suna sake bawa su dattijon da Umma hakuri Dadah kuwa kamata tayi tayi dakinta da ita ta zaunar tana kallonta tace”

Ki dauka dangana ‘yar Nan kibi umarnin mahaifinki da mahaifiyarki tunda dai kinsan bazamu zabar Miki mugun abu ba,
Banda abinki Najma kinyi aurenki kina cikin kwanciyar hankali da nutsuwa meyafi hakan,
Dan shekarun da Kika basa waye yasani tunda idan aka kalleku ma sai adauka sa’an babban yayanki ne,
Shin menene illar auren qaninka tunda?
Shin kin manta Nana Khadija ko data aura Manzon Allah ya girmesa da shekarun dasukafi Wanda kikaiwa naki mijin ita datafi daraja ma ko farin ciki da wannan koyin bazakiyiba ki faranta Mana?
Mu idan bakya Yi danmu munada fada da takura to kiyi Dan hajjo da Alfa Mana,ga Hanifa Nan haryanxu Bata ganin laifinki tana bayanki sbd irin qaunar datake miki
Dan Allah kiyi hkr kiyi zamanki gidan aurenki tunda har daga mijin harsu hajjon sun amincew zamanki ba takura sai kinji kin samu nutsuwa da auren.

Haka Dadah ta ringa Bata rarrashi da maganganu sbd ganin fadan ba inda zai kaisu saiga tone tone har Azo abata goma biyar Bata gyaru Dan ita da wannan aure ya mutu gwara aje ahakan tana zaune gurin hajjo indai da auren yafi musu zasui jira har Allah yasa auren yazama Kamar kowanne auren.

A dakin Dadah tayi zamanta saidata nutsu kafin Dadahn da kanta ta rakasu har palon hajjo suka Kuma taruwa suka rarrasheta kafin Dadah ta tafi
Har dare hajjo da hanifa na tarairayarta Dan tasake Haka suka Kwana
Ko Dad Alfa da kansa Saida yakirata suka sake zama da hajjo suka ringa rarrashinta cikin kulawa hartazo tanajin kunyar abin qarshe Dole ta sake Dan ganin yanda duk suketa sake lallabata shiyasa ta sake sosai ta koma bakin aikinta,

Hannah da mum Malika Koda sukaji abindaya faru Dadi Kamar me musamman suka sake maida himma gurin ganin auren Hannah da MARSHAL din ya tabbata,
Duk yanda Hannah taso fadawa marshal din rigimar Bata samu damaba sbd baida lokacinta busy yake sosai gashi yanata tafiye tafiye acan din Dole ta hakura harta samu lokacinda zata fada Masa.

Umma da Dattijo Basu duk da zancen yayi kwanaki sosai Basu daina fushi da itaba sama sama suke amsa gaisuwarta idan tashigo gidan Dadah ce dai take lallabata dataga fushin ba yayi sai anty Amina daketa aikin dawainiya da duk abinda Hanifa keso sbd cikinta daya fito sosai yanzu.

Takoma aikinta gadan gadan sai yamma take dawowa musamman da ayyuka sukai Mata yawa na ‘yar rigimar da ake wadda ta tarar Marshal ya fige Abbas daga ALFAs Amma sauran shareholders din Basu yardaba shikuma sbd yafi kowa hannun jari aciki yace hukuncinsa kenan.
Rigimar tasa ayyuka sun Mata yawa sbd dukkanin ayyukan office din president na companyn yadawo office dinta tunda Abbas an dakatar dashi say angama rikicin gashi Marshal din yatafiyarsa saiya dawo Kuma.

Da mamakin wannan qarfin halin nasa take aikin office din kullum sbd ayyukan sun Mata yawa ko yawon meetings yasa har wata Yar rama ta taso mata.
Saidatai wata daya da sati biyu tana fama da ayyuka kafin ayyukan suka Dan daidaita tafara samun kanta har tana dawowa gida da wuri.

Yau tunda tazo office din batai komaiba sbd jiri datake gani tun jiyan tafara jinsa yanayi Yana tafiya.

Dafe kanta tayi tana Dan rufe ido ta bude ahankali ta dago tana kallon Sarah data shigo office din ta bude Baki ahankali tace”

Sarah please bani ruwa me sanyi nasha.

Kallonta Sarah tayi da mamaki tace”

Me sanyi ko me Dan sanyi kadan?

Batareda ta dagoba tace”

Me sanyi sosai.

Da mamakin Sarah takuma kallonta sanin Bata Shan ruwan sanyi zatai mgn saikuma ta fasa ta nufa fridge ta bude ta dauko Mata ruwan roba masu sanyi sosai ta kawo Mata ta miqa Mata.

Karba tayi ta bude Kai tsaye takai bakinta tana Sha Sarah na kallonta da mamaki.

Ajiyar zuciya kadan ta sauke bayan tagama sha ta ajiye sauran ruwan tana cewa”

Sarah zanje gida yanzu kaina na ciwo Ina buqatan hutawa ko zai sake.

Tare suka fito da Sarah din itace take tuqin takaita gida suka nufa cikin gidan tare.

A Palo suka tararda Hanifa zaune tareda anty Amina data kawo Mata sabuwar Awarar da Umma ta Aiko Mata wadda akaiwa sauce din kayan miya dasu carrots da kwai.

Kallo daya Naj tayiwa Awarar taji tana son ci abinda Bata taba yiba shine ko dakinta Bata shigaba ta qaraso gefen Hanifan ta zauna ahankali tana cewa”

Yunwa nakeji sosai har kaina Yana ciwo.
Ta dauka plate tana miqawa Hanifan tana cewa”

Samun zanci.

Zuba Mata Hanifa tayi tana cewa”

Lallai yau ‘yar gaban goshin hajjo yunwa takeji tunda ko daki bazaki iya qarasawaba.

Batace kalaba saidataci Awarar a bakinta taji kanta dake sarawa ya daina ta dago ta kalli Hanifan ahankali tace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button