DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Dakatawa tayi tareda waiwayowa ta kallesa ta cikin wayar zatai magana saita kasa ta fuske tana kokarin wucewa tabar Hanifa ta riqota tareda maidata zaune tana cewa”

Dawo ki zauna Bari Ni natashi kicin zanima.

Miqewa tayi tabar gurin bayan ta aje wayar saiti da Naj din.

Dauke Kai Naj din tayi tana cigaba da duba wayarta tanajin idanuwansa na yawo akanta duk sai hakan yasata kasa nutsuwa ta dago ahankali fuskarta a hade suka hada idanuwa ta dauke Kai kafin tayi wani motsi a natse yace”

You look sexy in that dress.

Da wani irin yanayi na kunya da takaicin kayan dake jikin nata ta motsa zata kashe wayar yasakar Mata wani kallon daya sata hadiye wani yawun dake neman sarqeta yace”

Ok goodnight jeki kwanta.

Kashe wayar yayi sai alokacin ta sake daure fuska tana dauke idanuwanta daga gefen wayar tana kallon kayan jikinta da gaban rigar take a Dan bude Ana hango tsakiyar kirjinta da condom bra Dinta ta rabasu ta miqe tabar gurin ta nufa dakinta.
Tana shiga tubewa tayi Bata sake wankaba sbd Dan sanyi datakeji ta saka kayan bacci tayi kwanciyarta take bacci ya dauketa.

Washe gari sallar asuba kawai ta Gama ta fito taje kitchen Tasha tea me zafi tana lumshe ido sbd rashin shansa a Daren jiyan yasa takejin yunwa Kamar hakan.

Da cake Tasha tea din ruqayyat data fara ayyukanta tana binta da satar kallo sbd sanin gabaki daya Naj din batada ciye ciyen abinci qaidarta taci lokacin cin abinci tagama takuma shikenan.
Har tagama tafito Hanifa Bata zoba Dan Haka Takoma daki ta kwanta wani sabon baccin me nauyi yakuma dauketa.

Sai qarfe goma da mintuna ta farka tana kallon agogo ta saki wani qaramin numfashi tana dafe Kai sbd ganin irin lattin datai Wanda Bata Saba lattin ba irin Haka.
Zuro qafafunta tayi ta sauko gadon tana nufar toilet Kai tsaye tayo wanka ta fito.

Babu Bata lokaci ta shirya cikin doguwar jallabiya Maroon da qaramin mayafin data nade kanta dashi Wanda kalar abayar ta fitarda tsananin hasken data qara ta fito qamshin khumrah kadan Yana Dan tashi a jikinta..

Kai tsaye gurin hajjo dake zaune palon ta qarasa ta zauna gefenta cikin kulawa tace”

Good morning hajjo, muntashi lafiya?

Kallonta hajjo tayi cikin kulawa tana cewa”

Lfy kalau,yau kinyi lattine?

Eh,zanci abinci na wuce.

Dining ta nufa ta zauna tareda Kiran ruqayyat takawo Mata ruwan sanyi tafara cin abincin kenan saiga Zainab din Anty Amina tashigo da sallama ruqayyat data bude Mata kofar palon tana biyeda ita zuwa dining din.

Anty Naj Ina kwana?

Lafiya kalau zainab yasu umma da anty Amina suka tashi da Dadah?

Lafiya kalau,ga wainar Anty Hanifa Nan Zan koma aikin su daughnuts mukeyi da ummana da aka kawo Mata na wani bikin idan Anty Hanifa ta fito Ina Mata Ina kwana.

Juyawa tayi ta qarasa gurin hajjo tana gaidata har hajjon na Bata sako gurin umma kafin ta wuce.

Qamshin wainar ya ringa Shiga hancinta Amma dayake Sam waina Bata dametaba saita dauke Kai tana daukan hakan amatsayin rashin damuwa da bataiba da waina
Amma qamshin sai sake Shiga hancinta yakeyi Yana sata Jin wani iri ba shiri ta miqe tabar gurin tana goge bakinta da yawunta keyi Kamar zasu tsinke Dan Haka Kai tsaye handbag dinta ta dauka tana cewa”

Hajjo na tafi office saina dawo.

Ok ki kula,saikin dawo.

Sai data Shiga motarta ta sauke wata irin Ajiyar zuciya tana sauke numfashi ahankali.

Sai data samu nutsuwa kafin ta tayarda motar ta fice daga gidan ta nufi office.

Isarta office taji abinda take no yakuma taso Mata da qyar ta daure ta iya kaiwa office dinta tana Shiga ta nufa toilet da sauri wani irin amai me qarfi da wahala na kufce Mata.

Da sauri Sarah tabiyo bayanta ganin irin yunqurin Aman datake me wuya da qarfi.

Daqyar Aman ya tsaya ta wanke fuskarta tareda dagowa ahankali tana miqewa dukkanin Rabin qarfinta ya tafi ta kalli Sarah tana cewa”

Bani ruwan sanyi zansha.

Cikin kulawa da damuwa Sarah tace”

Naj kinci wani Abu ne?
Ko Zan Kira Dr sa’id ne yazo ya dubaki idan bakyajin Dadi.

Girgiza Mata Kai Naj din tayi tana fitowa toilet ta zauna a kujera tana karban ruwan sanyin ta bude Tasha ahankali tana ajewa tace”

Basai kinkira Dr sa’id ba inaga naci abinci da yawane kawai zanji sauki yanzu tunda na same na rage kawai dai karki Bari a dameni banajin Dadi Kuma.
Lumshe idanuwa tayi tana dafe kanta dake Dan juyawa sbd Aman, Sarah ta fice tana sake Mata sannu.

Wunin kasa gane kanta tayi gabaki daya a office din Haka dai ta tattara Takoma gida wani Dan zazzabi na damunta.
Ko a gidan data Isa abinci kawai tasamu taci ta kwanta saikuma taji daughnuts din dazu da Zainab tafada Mata takeson ci Dan Haka ta daga wayarta takira anty Amina tace”

Anty Amina kibawa zainab daughnuts takawomin nakasa cin abinci cikina ya qulle.

Kash wlh wainda akaiwa harsun Aiko an karba duka saidai ko samosa akwai sauranta Bari akawo Miki.

No ki barshi banasonta zanci cake kawai.

Tana kashe wayar taji zazzabinta na neman qaruwa Haka dai ta lallaba har dare shima tanacin abincin dare ta kwanta gabaki daya Aman ya sakar Mata da mutuwar jiki da guntun zazzabi.

Ko washe gari wani sabon uban latti ta buga dayasa fita ko abinci bataciba
Sai data Isa office Tasha milk drink aikuwa tana gamasha Amai ya biyo bayansa Wanda yafi na jiya take hankalin Sarah ya tashi ta zubawa Naj din data Gama galabaita tana cewa”

Naj please kibari nakira Dr sa’id.

No tattara min kayana gida zankoma jiri nake gani.

Tsayawa Sarah tayi tana kallonta cikin tsananin shakkun tunanin daya shigeta da mamaki me tsananin qarfi tareda kasa gasgata tambayar dazatayin tace”

Naj are you pregnant?

Wani kallon mamaki da takaici tayiwa Sarah din duk da tana Dan jin jiri ta yamutsa fuska a hade tace”

Are you stupid?
Ta Yaya zakimun wannan tambayar inada Wanda zaimun cikine?
Sarah please karki karamun ciwon Kai just leave,kije ki dauki key din motar muje ki kaini bazan iya tuqin ba.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107

DM 35

Albishirinku mata????shin Ina ma’abota ado da kwalliya????️Ina team no makeup????️Mata gareku inamai tabbatar muku dacewa duk wnd takeneman kayan gyaranjiki walau matsalan fata kike fama dashi kamarsu pimples, tabo, sunburn,nankarwa, knuckle ko Mai Kika shafa yabatamiki jiki Dama sauransu walau Kuma kawai kinasan kigyara fatarki kizamto tauraruwa abarso abar marari agurin kowa????Mata inamai tabbatar muku dacewa kujaraba kayan mg’s skincare Koda gudane dg cikin kayansu kuga abun mamaki????????‍♀️ domin kayansu kankat ne Koda iya sabulunsu Kika Dana saikinfita zarra cikin Mata domin ynd fatarki zaikoma Shar kamar Madara kidinga kyalli kina haskakawa duk inda kikayi se ankalleki????Kuma wani abun jindadin ma shine duka kayansu organic ne Babu na bleaching kawai zaigyaramiki jikine yafiddomiki d ainihin natural beauty dinki inma NASA haske kikasiya natural ne kawai bn bleaching b????‍♀️mekike jira hjy maza garzayo kinemi naki acikin farashi merahusa kigyara jiki kiyi fes abinki baruwanki da sekinyi kwalliya inzaki fita????kifita aganki da zallar kyawunki hjy????kanawa mutanenmu ina godiya Kuna nunama mg’s one luv tnx for ur patronage dama Yan sauran state mg’s na godiya may your pocket never lck azo asiya Kaya hilis karnakoma kauyenmu????Yar shawarmannan karta gagareni????????
Henajiku lvs????
Meso should chat
08062991549
07046881166
Call 08064532391
Soap:3k, beauty kit:11k,bridal kit 18k
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg’s skincare

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button