DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Tare suke da Hanifa dan haka Kai tsaye sashensu dad da mum Malika din suka nufa.

Babban lafiyayyan palon farko suka yadda mum Malika zaune tana waya tana ganinsu ta saki murmushi tana sallama da Wanda take wayar ta miqa musu hannu tana cewa”

Oh our beautiful bride is here
Naj you’re looking morethan beautiful.

Murmushi me qayatarwa tasaki tana cewa”

Thank you mum Malika kun iso lafiya?
Ya gajiyan hanya?

Alhmdlh alhmdlh hanya alhmdlh.

Kallon Hanifa tayi dayake ita tunda suka iso tazo tana tareda dad Alfa tace”

Hanifa I’m so happy for Naj
Allah yasa albarka a wannan auren.

Amin mum.

Congratulations Naj.

Thank you mum Malika.

Hannah ce ta fito sanye cikin doguwar riga Mara dogon hannu kanta daure da wani Dan qaramin scarf da tsadaddiyar wayarta a hannu tana dubawa tana ganinsu ta qaraso da murmushi akan fuskarta tana zama gefen Hanifa tace”

Sister in-law Hanifa barka da shigowa I’ve been looking for you tun dazu hajjo tace kuna gidansu Naj.

Murmushi Hanifa tayi tana kallonta tace”

Dazu nashigo kina ciki kina wanka
Ya hanya?

Lafiya kalau sis Hanifa.

Maida kallonta tayi kan Naj dake duba massage din Sarah akan Wai Abaas ya  dakatar da ita daga aiki.

Fuskar Naj din ta zubawa ido tana kallon kyan fuska Dana jiki da Allah yabawa Naj din ta gangara da idonta kan hannayenta dake farare tas kamar Bata aikin komai dasu gashi Tasha gyara tako Ina fatarta sai glowing takeyi
Dama can Naj na tsananin burgeta sbd tanason Abu me kyau ita shiyasa take tsananin son Marshal dinta ga wani aji da Naj din takedashi kamar ba Yar masu rufin asiri ba Dan Haka ta saki qayataccen murmushi tana kallonta cikin tayata murna tace”

Naj mijinki dinnan yayi sa’a
Congratulations to you Allah yabaku zaman lafiya.

Murmushi Naj tasaki tana kallon Hannah din tace”

Amin nagode Hannah.

Palon dad Alfa suka nufa inda suka samesa zaune Yana waya Dan kusan jama’arsa da yawa zasuzo daurin auren Yana ganinsu yasaki murmushi Yana kallon Naj datake murmushin Dole sbd saqon Sarah yabata matuqar mamaki shiyasa ta yanke shawaran Kiran Abbas din zatayi tana fita taji dalilinsa na korar Mata Sarah.

Zaunawa sukai Banda ita Naj din data zauna a qasa cikin biyayya da farin cikin zuwansa tace”

Dad Alfa barka da zuwa,ya Hanya?

Alhmdlh Najma ya hidiman?
Babu dai matsalar komai ko?

Babu komai Inshallah.

To shikenan Allah yasawa auren albarka yasa agama taron lafiya.

Hanifa ce tace Amin kafin suka Dora da zancen tahowar da Marshal zaiyi Wanda tun kafin suyi nisa Naj ta miqe tana cewa”

Zan Dan karba waya” ta fice.

No Abaas din ta Nemo Kai tsaye tareda Danna Masa kira tahau ringing.
Harta katse Bai dagaba ta sake Danna Masa Kiran sai akaro na uku ya dauka da cewa”

Hello.

Kai tsaye da muryarta me taushi tace”

Maganar office ce zanyi dakai akan Sarah ko Zan iya sanin abindaya faru ka dakatar da ita?

Takaicin zancen nata yaji Dan dama Yana sane yayi hakan Dan kuwa idan ba hakan yayiba yasan wlh har abada Naj bazata taba kiransaba har ayi auren kuwa to Amma yanzun data Kiran sai abin yabasa takaici ko gaidashi bazata iyayiba sai magnar Sarah Dan Haka cikin baqin ciki Kai tsaye yace”

Bana wannan maganar sai a office”

Kashe wayarsa yayi Yana sakin numfashi me zafi tareda komawa jifa da wayar Yana Jin tafasar zuciya.
Jin bazai iya hakura ba yasa ya zari key din motarsa ya fice daga palon mahaifinsa Kota cikin gidansu Bai bi ya fice sbd gidan Suma cikeda jama’ar biki.
Itama akaro na farko dataji bazata dauka wannan wulaqancin nasa ba cikeda takaici ta fasa sake kiransa ta wuce gidansu ranta a Dan jagule.

Washe gari akai gagarumar taron walima kawai sbd gabaki daya Naj din batada raayi na biki sbd komaima yafita kanta har akai waliman aka gama Bata cikin wani dadin zuciya sbd batasan me Abaas din yafadawa Dattijo ba yakirata itada ummanta a Daren yayi musu wani irin fadan cin zarafi duk da ummanta na cikin farin ciki na hidimar bikin Saida tayi kwanan bacin Rai.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107[1/14, 3:33 PM] +234 901 771 2720: DM 8
Washe gari kodata tashi miscalls din Dr sa’id biyar tagani a wayarta da text na cewan zaizo yau din yanason Mata fatan Allah ya Sanya alkhairi batai replying nashi ba sbd ganin massage din tun safe yayi Dan Haka ta share akan sai ya zo din.

Yau Bata leqo gidansu ba tunda tatashi tana tareda Hanifa data tashi da ciwon qafafu Dan Haka sai yamma tasamu fitowa ta da dogon hijab har qasa ta mask a fuskarta ta nufi gidansu inda acan tayi wani wankan ta shirya cikin wani brown lace riga da skirt saiga kiran Dr sa’id ta yafa gyale ta fito fuskarta ba kwalliyan komai sai Kohl dake cikin fararen idanuwanta.

Ko data fito Kai tsaye gidansu Hanifa ta shiga sbd tasan Yana ciki baya tsayawa waje musamman irin yanzu da komai zai iya faruwa.
Sabbin qarin securities tagani a waje da cikin gate na farko na gidan tareda ganin sabuwar motar gidan dake rufe a fili da alamun anfita da ita hakan yasa ta fahimci cewan DM na iso kenan ta Dan waiwaya hanyar sashen dayake matsayin nasa acikin gidan kafin ta dauke Kai ta qarasa sashen hajjo daidai shigowar Kiran Abbas tana gani taji bazata daukaba Dan Haka ta kashe wayar gabaki daya tana Shiga palon Kai tsaye.

Hajjo ce zaune a palon sai Dr sa’id shima suna maganar qafafun Hanifan daya duba ta kallesa tana cewa”

Dr barka da zuwa.

Kallon quralla yaso yimata Amma sbd hajjo na gurin yasa ya taqaita kallonsa fuska a sake yace”

Barka Amarya,ya hidima?

Murmushi kawai tayi tana qarasa dakinsu Kai tsaye tashige tana kokarin sake kunna wayarta Bata tsaya koina ba sai bakin gado ta zauna tana Kiran sunan Hanifan batareda ta dagoba.

Dakatawa tayi da abinda takeyi Jin shiru tareda Kuma qamshin turaren TOM FORD Tobacco Vannile daya Gama gauraye dakin sanyin qamshinsa ko Bata dago ba tabbas tasan kodai DM Yana dakin kokuma yashigo ya fita sbd tsadar turaren kawai yasa Babu Wanda zata canka bayan shi Dan Haka ta miqe ahankali tareda juyowa akaro na farko idanuwansu suka shiga cikin na juna a bazata Yana zaune kan sofa gefen Hanifa da farin cikinta yasa ta daina Jin ciwon gabaki daya daga ita har shi Naj din suka zubawa ido
Ta dauke nata idon tana Dan dauke Kai daga kallonsa ta bude Baki Kai tsaye cikin dan sake fuska tace”

Barka da zuwa JALAL.

Dauke idanuwansa yayi daga kanta cikin muryarsa me Kai tsaye yace”

Ya hidima? Allah ya Sanya alkhairi.

Amin” tace Kai tsaye tana juyawa ta fice tana cewa”

Hanifan zanyi magana da Dr sa’id kafin kigama okay.

Tana fitowa palon Dr sa’id ma yagama mgna da hajjo suka fito zuwa harabar gidan inda suka tsaya suna mgna tsawon mintuna suna Shirin fita saiga taga Dr sa’id na kallon bayanta ta waiwaya ahankali daidai qarasowarshi zai wuce zuwa sashensa lafiyayyar fatarsa tana haskawa hakama qaqqarfan jikinsa dayake geaming yagama budewa tako Ina ta yanda duk qwaqwarka bazaka gano shekarunsaba sbd mugun miskilancinsa da kamewarsa dasuka shige da shekarun nasa Dan kuwa ko Dr sa’id daya girmesa da kusan shekaru shida koma fiye Yana ganin tsananin kwarjininsa da cika idonsa Wanda yasa manyansama suna bashi girman hakan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button