DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL
Gaisawa sukai da hajjo tana sake Mata sannu da hayaniyar taron jama’a kafin shima Dattijo ya gaida hajjon ya maida kallonsa kan Alhaji Alfa damuwarsa na bayyanuwa gabaki daya yafara magana da cewa”
Alhaji Alfa duk da bansan dalilinka na son magana daniba a a Daren Nan Ni Ina daukeda magana me girma dazan fara fada maka akan daurin auren gobe.
Bansan menene taqamaimai abindaya faruba a dazu Amma dai a yanda nasamu bayani daga bayan Nan shine Najma da mahaifiyarta sun taru sunyiwa yaron Nan Abbas wulaqanci hakama sojojin JALALUDDEEN sukai Masa duka yanzu Haka Yana asibiti a kwance a taqaice zance dai iyayen yaron Nan sun fasa auren Nan.
Naso su fahimceni mu tsaya ayi maganar fahimta Amma ita mahaifiyar yaron ta dauki zafi sosai qarshe dai qanin mahaifin nasa Alhaji Abubakar yace ayi hakuri da maganar auren Nan yanzu Bai sanarwa gaba ba Wanda Ni nasan Babu wata gaba Dan kuwa bazasu taba dawowa ba Dan Haka qarshen maganar zance dai aure babushi ya fasu ba maganar daura aure gobe da Abbas.
Shiru dukkaninsu sukai gurin yadauki tsit na wasu mintuna kowa zuciyarsa ba Dadi musamman shi Dattijo da tasa zuciyar quna takeyi tana ‘daci.
Sauke Kai Dadah tayi tareda fashewa da kukan da baya fita sosai tace”
Innalillahi-wainna ilaihirrajiun
Wannan jarabawa nada nauyi ya Allah kabamu ikon cinyewa yasa Allah Fatima da Najman Susan kansu suke cutatarwa tareda mu da Allah ya Dora Mana nauyinsu.
Karkice Haka dadah sbd hakan Suma ba laifinsu bane musamman Fatima zatafi kowa farin cikin ganin ‘yarta tayi aure Dan Haka bazata Rusa auren yarta da ganganba musamman da aka kawo wannan gabar ta auren kawai ake jiran daurawa gobe” hajjo ce me bawa Dadah hakuri da wannan kalaman.
Shidai Dattijo shiru yayi yakasa cewa komai sbd tunanin shawarar abinyi goben.
Gyaran murya Alhaji Alfa yayi tareda tattaro nutuwa yace”
Dadah hakurin da aka Saba da tawakkali shi za’a sake dauka sbd shima Abbas din Allah baiyi shine mijinta ba Wanda a hakikanin gaskia harda wasu halayensa dana samu labarinsu yanzu yasa saidai kawai muce Allah yazaba Mata mafi alkhairi,
Sai maganar itace kokuma mahaifiyarta suka lalata auren wannna duk bashine abin dubawaba kawai Allah ne baice yazama mijintaba Dan Haka Dan Allah ayi hakuri a dauka hakan kawai a matsayin wata jarabawar
Sai maganar taron jama’ar da aka gayyato na nesa Dana kusa na daurin auren goben sai a sanar da cewar an daga auren abawa jama’a hakuri….
Sai alokacin Dattijo ya bude Baki Yana dagowa daga soken da kanshi yake tun dazu yace”
Maganar taron gobe Inshallah za’ai daurin auren tunda Allah Bai qaddari anyi dashi wanda aka tsaro dashiba na yanke goben Zan daura Mata da Mubarak sbd tun farko ma hakan yakamata muyi tunda auren na waje Bai samuba sai ayi na zumunci a rufawa Kai asiri dama shine qarin abinda dayasa nace Zan nemaka a Daren Nan na sanar da kai hukuncin Dana yanke sbd Kota bangarenka idan akai dubi da irin manyan jama’ar qasar nan dazasu zo daurin auren gobe Dominka idan akace anfasa bazasuji dadiba Dan Haka wannan shine nawa hukuncin.
Share hawaye Dadah tayi tana cewa”
Wannan hukuncin yayi gwara ayi Dana gidan Allah yasanyawa abun albarka….
Cikeda bayyanarda damuwa hajjo tace”
Mubarak yaushe akai aurensa da za’a Kuma daura Masa wani auren inace iyakacinsa wata t
Bakwai da aure hakama Najma din gabaki daya Bai kamata ayi Mata aure irin wannan ba Dan ba laifinta bane itama tanason tayi auren Amma Bata hakaba.
Numfashi Dattijo ya sauke Yace”
Mubarak ne me aikin Yi me Dan girma acikin mazan gidan Kuma tunda kamawa tayi Haka zai hadasu su biyun da matarshi ya riqe Amma Kam da yardar Allah Najma tagama zama tana Kore mazan aurenta rantsuwace akaina da alqawari danai Mata daga ita har mahaifiyarta akan wannan karon Inshallah wlh natara jama’a aka fasa aure bazan Bari ayi abanzaba Zan aura Mata duk Wanda ya samu da wannan rantsuwar akaina Amma suka taru suka shure maganata Dan Haka auren Najma gobe da yardar Allah ba fashi za’a daura.
Cikin sanyin murya sbd jikinta daya Gama mutuwa gabaki daya da al’amarin Dadah tace”
Allah yasa hakan shine mafi alkhairi Amma dai banason ayi abinda zai Kuma kawo matsala idan aka fita wannan Dan Haka daga waya ka Kira Mubarak a fara sanar dashi zancen aji ta bakinsa kada ayi abinda zai janyo wata fitinar.
Zallar bacin rai ne da takaici suka Danni zuciyar hajjo ace yarinya Kamar Naj Ana Shirin yimata auren wulaqancinda sai Ankira Mubarak an tambayeshi bayan kowa yasan cewa zaiyi bayaso tunda duka duka yaushe yayi aure da matarsa wadda take yarinyace qanqanuwa sosai bayan cin zarafi da tazarci Babu abinda kishi bazaisa tayiwa Najma wadda take mace me tsananin kamewa da sanin qima da darajar kanta cikin bayyanarda bacin ranta a fili tace”
Basai Ankira Mubarak ba Alfa biyawa JALALUDDEEN sadakinta a daura auren dashi gobe.
Cikin sauke numfashi Alhaji Alfa ya kalli hajjon wadda kowa yasan ranta yariga yayi mummunan baci akan al’amarin shi kansa Alhaji Alfan ransa yabaci da hukuncin Dattijon saidai kawai Yana iya kokarinsa gurin dannewane sbd kada ya nuna isarsa da yawa bayan sunfisa iko da Isa akan Najman Kuma shima da hukuncinda yayi niyar yankewa kenan na nemawa Marshal auren amaimakon Mubarak dasukace Dan shikuma aikin Mubarak din ne Bai yarda dashiba Dan harka yakeyi da yan siyasa saikuma maganar Hannah da duk sunsan da maganarta da jalal din saigashi hajjo ta rigasa yanke hukuncin Dan Haka take ya maida kallonsa kan Dattijo dayayi tsit Yana soke Kai sbd ganin ran hajjo ya baci sosai cikin girmamawa ya kalleta zaiyi magana tace”
Aurenta da jalal zai kawo qarshen matsalar komai Inshallah tazarar shekarun ba komai bane tunda duka duka baifi shekaru uku ne tabashi ba dan Haka wannan ba matsala bane.
Wani kukan Dadah takuma fashewa dashi tana cewa”
Ni kulu dame zamu saka mukune da koyaushe kuke binmu da alkhairi¿
Tunda mahaifin yarinyar Nan ya rasu kuka zama gatanta kuka ginata akan kyakkyawar rayuwa yanzu Kuma gashi kun amince da ita adaidai lokacin datake cikin irin wannan tsaka me wuyar ya Allah yasaka muku da mafificin Alkhairinsa Kuma maganar ba ko anbawa jalalu ko ba’a bashiba babuta Dan kuwa Alhaji Alfa kaima mahaifintane Kai tsaye zaka iya cewa kawai kazaba Mata jalalun adaura dashi Kuma ayi hakan sbd ka Isa indai akantane.
Jinjina Kai yayi Yana kallon Dattijo yace”
To Ibrahim me kagani akan hakan??
Jiki mace Dattijo ya girgiza Kai Yana saukewa sbd shi wata irin kunyace ta dabaibayeshi sbd irin qaunar dasu hajjo kewa Najma yasa bazasu iya Bari ayi Mata auren tozarciba daya dage akan sai yayi din Dan Haka kasa kallon hajjo yayi ya kalli Alhaji Alfa yace”
Allah yasa hakan shine alkhairi.
Tashi hajjo tayi tafara ficewa kafin Suma suka fito Dadah hankalinta kwance murna fal cikin ranta tunda damuwarta Bata Kwana da itaba an kaudata Dan kuwa yanzu auren ya sauka inda Babu halin fasawa bare tashiga shakku shidai Dattijo duk ransa har lokacin a jagule yake Dan Haka Babu Wanda yasanda maganar sauyin auren aunbarshi akan sai goben.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR 2022????
NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA
SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA
MAMUH GEE
DEEN MARSHALL
HAFSAT RANO
HALIN GIRMA
BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA