DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Ina kwana hajjo.
Amsawa hajjon tayi tana cewa”
Kinyi waya da Hanifa kuwa?
Tun jiya Isma’eel yakira batajin Dadi Wai hannunta na dama ya riqe Yana ciwo kamarma yakira wayarki a kashe yace.
Miqewa tayi tana cewa”
Bari na dauko wayar tun jiya na kunna inaga Banda caji ne Bari nasaka nasamu ko kadan ne saina kirasu kafin na Isa.
Kallonta hajjo tayi tana cewa”
Ki Isa Ina da sabon aurenki akai Najma¿
Kinga hakuri Zakiyi tunda Isma’eel din na Nan Kuma Dr sa’id ma yaje tun jiyan Dan Haka basai kinjeba yanxu Bari a kwana biyu tukuna.
Shiru tayi yanayinta ba Dadi idanuwanta na sauyawa da ciko hawaye kafin Tai magana Hannah tashigo dakin da sallama muryarta a shaqe,hajjo na ganin fuskarta tasan itama kwana tayi kukan Dan kuwa a kumbure idanuwanta suke jajir.
Naj ta qurawa ido zuciyarta na wani irin harbawa da zafin radadin kishinta me qarfi saidai kamar yanda mum Malika ta hudubar da ita akan danne fushi da boye bacin Rai shine matakin nasarar komai tunda dai kowa yasan daga Naj din har marshal ba son juna sukeba aurene kawai na Hadi na huce takaici da fita kunya Dan Haka fushi da qunci ba nasu bane samun zama Matar JALAL da rabuwarsa da Naj ba wani Abune dazai Basu wuyaba ko daga musu hankali Dan Haka dole zasu danne ‘dacin zuciyarsu.
Dan yaqen dole tayi tana qarasowa ciki ta zauna kusada Naj tana cewa”
Hajjo Ina kwana?
Ya gajiyan taro?
Allah yasanya alkhairi.
Hawayen datake dannewa suka gangaro ta qarasa gaban hajjo ta durqusa tana sake siririn kuka ahankali tace”
Dan Allah karkiga laifin kukana hajjo zuciyatace ke zafi bansan yazanyiba naji sauki bayan kukan sbd abin yazomin a bazatane.
‘dan tausayinta hajjo taji Kuma tasan Kam Dole hannah zataji damuwar abin musamman datasan ayanzu Kam babu ranar auren Hannah din da jalal sai taga Najmanta tasamu zama dakyau tukuna Dan Hakan takejin tausayin Hannah ta dafa kanta tana cewa”
Kiyi hkr shi aure muqaddarine Kuma Allah yayi itace zata zama Matar ayanzu Amma kadaki daga hankalinki Matar mutum kabarinsace kema lokacin ne baiyiba ki kwantar da hankalinki kinji.
Shiru tayi tanajin wani qaton takaicin tsohuwar Yana tsaya Mata a maqoshi datake Mata zancen wani lokaci bayan ba Haka takeson ji ba.
Share hawayenta tayi tana miqewa a sanyaye ta juyo gurin Naj datake Shan tea dinta batareda ta maida hankalinta kan zancensuba ta Dan saki yaqen murmushi tace”
Naj Allah ya Sanya alkhairi da fatan bazaki ringa Jin damuwar alaqata da Marshal ba.
‘dan kallonta Naj tayi kafin Kai tsaye tace”
Thank you” kawai taci gaba da Shan tea dinta Dan ita abundama zai ringa alaqantata da Marshal din Bata buqata Dan Haka Hannah ma na cikin abinda zata nesa kanta dasu.
Kallon tsaf Hannah taqare Mata tana ayyana wannan shariyar ta Naj datake Kamar wulaqantawa gareta kafin ta juya ta fice idanuwanta na sake kadawa da Jan baqin ciki da takaicin hajjo da Naj din.
Cajin wayarta Takoma daki tayi takira Hanifa sukahau wayarsu duk da taqi Bari Hanifan tayi Mata maganar auren itama Hanifan data fahimci Haka saita bar yimata maganar suka hau zantukansu.
Saida tayi sallar azahar ta ‘dan ci abinci kafin taje gurin gaida Dad Alfa datun jiya Basu haduba tafara zuwa gurin mum Malika ta gaidata Kamar yanda suka Saba Babu komai a fuska mum din ta tarbeta suka gaisa Tai Mata addua da fatan alkhairi Hannah na daki tanajinsu taqi fitowa sbd ayanzu kyakkyawan fuskar Naj tafasa zuciyarta yake itakuwa Naj Kai tsaye palon Dad din ta nufa tana duba wayarta ahankali tashiga da sallama ta tura kofar palon tana kashe wayarta Yana zaune kuwa a palon suna magana da jalal dake gefensa sanye cikin farar jallabiyar datasa takasa ganesa sosai Dan kuwa hardasu qaramar farar hular tabani kaji hadisi datai Masa wani irin kyau sbd kayane dabai cika sawaba sai yazo Nan Dan acan kayansa idan ba suit ba sai uniform din aikinsa sai kuwa qananun kayan Shan iska dayafi sakawa idan baya aiki komai Wanda suna cikin kayan dasuke Masa kyau sbd kyan fatar jikinsa.
Dauke Kai tayi daga gefensa tanajin idanuwansa na yawo a jikinta ta qaraso ta zauna a qasa tana gaida Dad din cikin nutsuwa.
Amsawa yayi Yana Mata barka da gajiyar biki cikin farin ciki kafin ya Dora da yimusu nasiha musamman ita akan dole tabi umarni da hukunci JALAL kowane irine cikin biyayya.
Shiru kawai tayi batareda ta dagoba har yagama ta Dan dago tace”
Nagode Dad” ta miqe ta fice batareda Tama nuna tasan da akwai wanzuwar wani a palonba bayan su.
Bayan fitarta waiwayowa dad yayi ya kallesa batareda yace komaiba ya Dan saki gajeran murmushi Yana mamakin qarfin girman Kai irin nasu su duka biyun Wanda bazai taimakesuba.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR 2022????
NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA
SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA
MAMUH GEE
DEEN MARSHALL
HAFSAT RANO
HALIN GIRMA
BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA
Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
Zaku tura kudin a
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Sai shedar payment dinki a????????????
08184017082
Kokuma katin waya na MTN anan????????
09134848107[1/16, 2:58 PM] +234 808 457 6211: DM 15
Washe gari sanin a daki ta wuni taqi fitowa sbd fahimtar dai a sashen hajjon yakecin abinci abinda Bata saniba shine baya fitowa zuwa cin abincin Rana acan ake Kai Masa sbd baya fitowa da ranar sai dare yake fitowa cin abincin Daren Dan masallaci kawai yake iya fita cikin Rana Amma bayan sallah Babu abinda yake sakashi fitowa cikin Rana Wanda hakan ne yasa skin dinsa yake fresh koyaushe.
Hajjo na sane da dalilin qin fitowar tata Dan Haka itama Bata damuba tunda lallabata takeson Yi Dan Haka Bata dametaba ta qyaleta,
Sai dare ta fito sanye da riga da wando na bacci farare masu tsantsi kanta sanye da qaramar hular da Bata Gama rufe gashintaba hannunta riqe da waya tana sai qamshi takeyi me sanyi ta nufi kicin ta dauko fresh milk Mara sanyi sosai tafito tanasha ta nufi dining tana shiga idanuwanta suka sauka kansa Yana zaune cikin fararen qananun Kaya hannunsa riqe da cup din ruwa marasa sanyi yanasha ahankali.
Dauke kanta tayi tana kokarin juyawa hajjo dake zaune taredashi tace”
Zoki zauna.
Dakatawa tayi tareda Dan rufe idanuwanta kafin ta bude ta juyo tareda kallon hajjon fuskarta Babu wani sauyi daga straight din datake cikin muryarta me nutsuwa Kai tsaye tace”
Banajin yunwa freshi milk din ya isheni bacci zanyi Dan natashi da wuri gobe zankoma aiki office.
Dan kallon Marshal hajjo tayi taga ko dagowa baiyiba bare yanuna yasan da zuwan wani agurin saidai tasan yanajinsu,
Ta maida kallonta kan Najma cikin kulawa da tausasawa tace”
Wane aiki bayan Baki Gama hutawa daga hidimar biki ba Kuma saikun zauna da mijinki kunyi magana akan aikin idan yaji zai Bari kici gaba.
Dagowa Najma tayi da idanuwanta dasuka sauya Nan take da maganar ta kalli hajjo sai Kuma takasa magana tayi shiru tana hadiye wani daci daya danne zuciyarta ta Dan rufe ido tabude ahankali tace”
Kaina Yana ciwo zanje na kwanta Saida safe hajjo.
Juyawa tayi zata wuce hajjo tace”
Dawo Najma zoki zauna.
Dakatawa tayi tafara sauke numfashi kadan kafin ta juyo tadawo taja kujera ta zauna batareda tace komaiba sbd Jin numfashinta ma takeyi Kamar siqe zamanta agurin da Wanda har lokacin Bai nuna yasan da wanzuwar wata halittar Dan Adam agurinba Wanda Kamar Ana sake sukar martabartane na mace dakuma girmanta.