DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Mun iso hajiya” me taxi din yafada daidai Yana parking bakin Babbar kofar gidan Marshal Alfa Wanda sojoji hudu ke zaune kofar gidan suna gadi.
Fitowa tayi ahankali cikin nutsuwa wadda zallar ilimi da wayewartane tareda ajin datake dashine yasa komai nata yake cikin nutsuwa ta bude jeka ta fiddo nera dubu daya ta miqa Masa tana cewa”
Nagode Mal Hafiz.
Juyawa tayi ta nufi gefen gidan daya bangaren dake gefen gidan Alfa wani ‘dan madaidaicin gidan gado Wanda yakeda Dan zurfi daga cikinsa sbd ‘Dan yawan dasuke dashi a gidan danma kusan duk Yan Matan gidan sunyi aure duk da bawai yawane dasuba sosai.
Cikin sabo sojojin dake zaunen dasukaga dawowarta sukace”
Welcome Ms Naj.
Dan murmushi tasaki tana waiwayowa tace”
Barkanku da aiki da hutawa.
Gidansu ta qarasa Wanda yake gefen da ‘yar tazara da gidan Alfa din ta shige Wanda ba gate bane koface irin ta gidan me ‘dan rufin asiri.
Gefen Dattijo ne a farko Dan Haka ta wuce Kai tsaye kuryar gidan inda taci Karo da Umma habiba zaune a kofar nata sashen kan kujera tana duba kayan ‘yan kananan atampopinta datake saidawa tana waya autarta Asmau na gefenta tana jera kayan cikin qatuwar ledar da aka kawo kayan.
Cikin girmamawa asma’un ta dago tana cewa”
Anty Naj sannu da dawowa.
Yauwa sannu Asmau
Ina yiwa umma sannu idan tagama wayar.
Hannu kawai umma habiban ta daga alamar amsawa tana bin bayan Najma din da kallo tana yamutsa Baki cikeda shaguben Naj din sbd aikin datakeyi Amma aure ya gagara.
Tana Isa sashen mahaifiyarta ta taddata a tsakar gida zaune itama tana lissafin nata kudin na turarukan wuta datake saidawa duk kwalaben turarukan a gabanta baje sai wani irin kamshi Mai qarfi ke tashi ta kalli umman tana nufar dakinta tace”
Ummi sannu da aiki.
Itama Bata wani dagoba tanaci gaba da aikinta gabanta tace”
Yawwa,
Lafiya dai Naga kin dawo yau da wuri.
Tana qarasa shigewa dakin nata tace”
Lafiya kalau hutawa nakeson Yi jiya bansamu bacci sosaiba.
Dama Ina Zaki samu maganar bacci me Dadi bakida abokin Hira acikin gida kowa Yana dakin aurensa,
Dayake Kuma ga wata babbar kwabon Nan kinsamu” taqarasa fada tana kallon gefen Anty Amina dake gefe tana yiwa babbar ‘yarta zainab bayanin karatunta da Bata ganeba.
Kallon umman tasu anty Amina tayi tana cewa”
Umma Dan Allah ki daina cewa”
Naqi zaman auren Nan a gaban zainab zata ringa daukan abin aranta tana ajewa da wata fassarar.
Wani mugun kallo ta watsawa Anty aminan kafin tace”
To Yaya kukeson na bayyanarda damuwata da halinda nake ciki akanku?
Ke zaman auren ya gagara kin tattara kindawo gida da budurwar ‘ya,
Ita wannan aurenma ya gagareta Yi kwata kwata ta koma ta zama wata ma’aikaciya mutane na qarqashinta ta Yaya zata iya auren
Shiyasa nake sake cewa Hanifa wannan aikin na Najma bazai Bari tayi aureba matuqar tana ganin mazan daidai take dasu..
Lokacin auren ne baiyiba umma” cewar Hanifa data shigo gidan tana qarasowa gurin umman fuskarta daukeda murmushi tace”
Umma Naj zatai aure kamar kowa lokacine kawai Allah Bai kawoba.
Cigaba da aikinta umman tayi tana cewa”
Duk da hakan dai ta rage ganin girman kanta ta sallamawa duk namijin daya samu tayi aure Dan shine mutuncinta da nawa Nima Dan ko Nima na huta da gorin dattijo da Dada dasuke ganin da saka hannuna a riqewar datai Kamar rake.
Murmushi Hanifa ta saki tana barin gurin umman tana cewa”
Umma Naj zata auri namijin daya kamaceta bawai ko wanne ba gskia
Kumafa ba riqeqa tayiba kawai dai Wanda zai Mana ciki da itane Bai bayyana ba haryanzu
Idan ya bayyana shikenan muma mun huta da damunta da kowa keyi da maganar aure,
Ni wlh bansan meyasa kuka sakamun Naj Dina a gaba ba duk kun damarmun ita.
Qarasawa kofar dakin tayi ta shige tana cewa”
Anty Amina barka da hutawa.
Da ‘yar dariya anty Aminar tabi hanifar sbd ganin Kamar ta kunna umma databi kofar dakin da harara kamar zata hadasu su duka Tai musu duka ko zasu fahimci ciwon ranta na rashin auren Naj din wadda ita Sam kamarma abin baya damunta.
Mamuh
ZAFAFA BIYAR 2022????
Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,
Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,
NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA
SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA
MAMUH GEE
DEEN MARSHALL
HAFSAT RANO
HALIN GIRMA
BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA
Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
Zaku tura kudin a
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Sai shedar payment dinki a????????????
08184017082
Kokuma katin waya na MTN anan????????
09134848107
[1/9, 7:53 PM] +234 901 554 3771: DEEN MARSHALL
Mamuhgee
2
Da wani irin kallo Hanifa kebin Naj dake tsaye bakin wardrobe daure da towel me kauri da girma brown color fuskarta fayau Kamar ko yaushe Babu wata damuwar abubuwan dake addabe da rayuwarta Kamar fitinar ummanta data su dattaji uwa uba ta Abaas datafi ta kowa zama abin baqin ciki da takaici.
Sake kallon fuskarta Hanifa tayi tana zaunawa kan gadon tareda ajiye wayarta gaban madubi tana cewa”
Nayi waya da Sarah dazu.
Batareda ta juyoba tana zare Yan kunnayenta tace”
Kada ki damu da abinda tafada Miki
Idan Akan Abaas ne zuwa yanzu kema kinsaba da halinsa,
Abinsa ya daina damuna yanzu saidai kawai yanda Naga kamar abin nasa kullum rikidewa yake zuwa ga zargi
Zarginma me muni Wanda nake dannewa Ina sharewa sbd Umma dasu Dattijo…
Sai alokacin Hanifa ta katseta da cewa”
Meyesa Zaki daure sbd su umma bayan su dinma da zasu bude ido da kyau su duba dabi’u da wasu abubuwan tako Ina Abaas Bai cancanta ba bama Haka ba yaushe Kika fara damuwa da abinda ake fada na cewan kece Kika qi aure da har Kika zabi auren Abaas lamido Wanda Ni kwata kwata baima kwantaminba
Gabaki daya Banga halayen maza masu hakuriba ko iya tattala mace atareda Abaas.
Ajiyar zuciya Naj din ta sauke Jin ran Hanifan yafara baci da zancen ta waiwayo ahankali ta kalleta tareda sakin wani irin lafiyyan murmushi Wanda kusan Arayuwarta tunda tazama budurwa cikakkiya kaf kannenta sukai aure aka sakota gaba tako Ina Hanifan ce kawai take iya ganin murmushinta me fidda asalin kyawunta Wanda yafito daga ainihin cikin zuciyarta sai kuwa Dr sa’id Wanda yake tamkar ‘dan uwa Kuma aboki agareta shima idan tana tare dashi takanji nutsuwa da kwanciyar hankali sbd ya fahimceta tareda sanin halayyarta fiyeda ‘yan uwanta na jini duk da kuwa Bata hada komai dashi ba face kasancewarsa likitan Hanifa tun suna yara har yanzu dasuka girma.
Zama tayi gefen Hanifan tana kallonta tace”
Ba abun damuwa bane basai kin saka damuwan Abaas ba aranki
Mubar maganan ma sunan Harya fara sakamun ciwon Kai.
Hanifa Sam ko sunan Abaas din tafi kowa takaicin saurara sbd tun ranar farko da zancen Yana son Naj din ya sauka a kunnenta ta qarewa background dinsa da halayyarsa bincike bataga ta inda ya cancanta Naj ba kafin daga baya taji fara aikinsa da zuba hannun jarinsa a ALFA’S dinsu Wanda Sam bataso hakan ba Amma sbd zagayen da yayi akai Masa Hanya ya bullo ta gurin JALALUDDEEN qaninta Wanda dukiyarsa tafi ta kowa yawa acikin ALFA’S din hadda kuwa mahaifinsu da shine me asalin companies din na Nan portharcourt dama na wajenta.