DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Ballewa hawayen idanuwanta sukai takasa daga ko qafarta sbd tsananin qunci da baqin cikin daya rufe zuciyarta kukan dakeson subuce matane yasata nufar toilet tashige tana rufo kofar da qarfi hawayenta suka qarasa ballewa suna gudu kan fuskarta.
Meya sametane?
Wace irin rayuwace wannan?
A rayuwarta kila Bata taba magana da fushiba irin yau din,
Ta Yaya za’a gane damuwarta da wannan auren,
Tayaya zasu gane Bata so da qaunar wannan auren har cikin zuciyarta.
Kuka sosai tayi idanuwanta dasuke a Dan kumbure suka qarasa kumburewar daqyar ta danne tayo wanka tareda alwala ta fito sanyeda kayan data shiga dasu tana fitowa ta dauki Kaya Takoma toilet din ta sanyo ta fito ta tayarda sallah har lokacin Yana zaune Yana aiki a laptop Babu alamar zai nuna dayasan da akwai wata halittar a dakin aikin kawai yakeyi Amma gabaki daya ransa har lokacin a bace yake Dan kuwa baitaba saka bacin ran kowabama aransa Amma yau ta kunnasa ta yanda yakejin ko ganinta baya buqatan yi.
Tana idarwa ta miqe ta tattara kayanta ta maida cikin akwatinta duka ta janyo akawatin ta dauka wayarta da handbag ta nufi kofa ta bude ta fice.
Dakin Hannah ta nufa Kai tsaye tayi Knocking tana jiran abude har lokacin idanuwanta a Dan kumbure suke.
Jin shiru yasa ta fiddo wayarta takira Hannah din.
Hannah dake bacci taji ringing wayarta na tashi ahankali ta lalubo tareda bude ido tana dubawa taga sunan Naj tasaki wani tsokin takaicin Naj din kafin ta dauka cikin bacci tace”
Yes Naj menene?
Kintafi da room card dinkine ko Yana reception ko hannun Hanifa?
Tashi zaune Hannah tayi tana bude ido dakyau Dan kuwa idan har Naj na neman Mabudin dakinta kenan Marshal ya iso kaman yanda tasani they can’t share a room.
Cikin farin cikinta da Bata boyeba tace”
The card is here with me Amma kiban 10min koma kiban 6min ganinan zuwa na bude Miki you are most welcome Naj.
Kashe wayar tayi tana dirowa gadon dakin gidansu Sofia dasuka kwana ta dauki Jakarta da kayanta a hannu tareda daukan key din motar Sofia ta fice da sauri sauri gudu gudu tana Isa inda motar take tafada tareda tadawa taja da qarfi ta fice.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR 2022????
NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA
SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA
MAMUH GEE
DEEN MARSHALL
HAFSAT RANO
HALIN GIRMA
BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA
Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
Zaku tura kudin a
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Sai shedar payment dinki a????????????
08184017082
Kokuma katin waya na MTN anan????????
09134848107[1/16, 2:58 PM] +234 808 457 6211: DM 20
ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK????????
https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share
ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK????????
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb
ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK????????
https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS
ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK????????
https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw
Batason Kiran Hanifa sbd batason damunta tunda tana tareda Isma’eel shiyasa ta takura kanta tayi tsayuwar jiran Hannah bakin kofar dakin tanajin gabaki dayama gida takeson komawa Amma sbd bazata iya barin hanifar ba ayanzu datake buqatarta akusa da ita shine kawai zaisa ta tsaya Amma da baby abun dazai hanata barin qasar a ranar gabaki daya toshewar numfashi takeji a garin gabaki daya.
Da kayan bacci riga da wando sai jacket data doro a sama jikin Hannah Babu kunya ta iso lodge din tayi parking tareda fitowa taqarasa reception ta wuce da sauri sauri
Tana qarasowa tahau bude dakin tana cewa”
Sorry nabarki kina jira,shiga
Shigo ki aje kayanki Zaki iya zama daganan har mu bar Sweden zanyi farin cikin zama taredake.
Bata cewa Hannah din komaiba ta shiga ta aje kayanta tareda nufar toilet tashige sbd tasan zatai matuqar wahala zama da Hannah sbd banbancin halayensu da rashin Jin juna dasukeyi,
Sam Hannah batai mataba sbd yanayin rawar kanta da iyayi dama komaima ita gabaki dayama Hannah is suffocating her Amma yanxu Haka zata zauna da ita kamema takeji akanta.
Wanka tayo tafito ta saka doguwar riga Mara nauyi ta zauna kan sofa tana shan tea me zafi ahankali tanajin Hannah dake cikin farin ciki shigewa toilet wanka,tana gamawa ta Haye gado ta kwanta ta rufa tana rufe ido.
Qarfe biyu zasuje asibiti Dan Haka biyu saura ta tashi tayi alwala tayi sallah ta shirya cikin Pal zileri drawstring straight skirt navy blue da milk long sleeves sai milk scarf data daura ta fito daga ita sai wayarta a hannunta daidai Hanifa na qarasowa dakin zatai knocking suka kalli juna tana mamakin ganinta dakin Hannah ta waiwaya ta kalli hanyar kofar dakin Marshal tasake dawo da kallonta kan Naj din Kai tsaye tace”
Me kikeyi Anan Naj?
Kallonta Naj tayi Kai tsaye kafin ta Dan dauke tana cewa”
Nan nadawo.
Kallon mamaki Hanifa tabita dashi kafin ta kalli Hannah dake shiryawa cikin Adonta na daukan hankali ta Kama hannun Naj din tajata suka fita gabaki daya zuwa gurin motocin da zasu fita dasu ta saketa suna fuskantar juna cikin fara gajiya da halin Naj din tace”
Naj banso shiga cikin zancenku ba sbd ku duka biyun Ina sonku Ina qaunarku banason dayanku yashiga takura ko damuwa shiyasa nake dakatar da kaina ga fada Miki gskia duba da yanda akai Miki ba daidaiba ta hanyar daura Miki aure da Wanda kike ganin kin girma Amma Naga kinason yiwa kanki illa Dan kuwa shekarunki sun tashi sunbi iska daga lokacinda aka shafa fatihar aurenki da Marshal Dan kuwa yanzu shine me ikonki,
Duk ba wannan ba meyesa Zaki ringa bawa Hannah damar dazata ringa qara samun kusanci da mijinki bayan kinsan zata iya Jan raayinsa tunda ita mace ce Kuma itama din kyakkyawace kina ganin Jin kan Nan naki bazai damekiba agaba idan Baki dakata wannan shirmenba koni da hajjo bazamu iya taimaka Miki ba agurin Wanda kike rainawar sbd namijine wani lokacin Kaine zaka sauke Kai kabisa Amma bazaki gane hakan yanzuba sbd Baki Gama sanin meye auren ba kokuma nace kinsani zuciya ta hanaki fahimta.
Da yanayi na rashin me zatace ta kalli Hanifan idanuwanta akanta da damuwar meyene abin tattaunawa anan ta bude Baki zatai magana idanuwanta suka sauka kanshi Yana tahowa sanye cikin Escada jeans blue da farar Saint Lauren long sleeves sai Shiels Emerald sunglasses dake fuskarsa daya Gama fito da fuskarsa dake wani irin daukan hankali Hannah ce taredashi tana sanye da jeans da Lois chiffon shirt sai qamshi take fitarwa suna tafe tana Masa firar outing dinta da friends dinta gabaki daya ta cika Masa kunne Amma baiyi yunqurin dakatar da itaba.
‘dauke idonta tayi akansu tana fasa maganar dazatai ta Dan dauke Kai,
Waiwayawa Hanifa tayi tagansu ta juyo ta kalli Naj din data dauke Kai cikin kawar da zancen dasuka fara tace”
Muje wainda ake Kira sun fito.
Isma’eel yafadawa su hadu a asibitin kawai ya nufa motar dayasa aka kawo Masa ya karba key yashiga Hannah tashige gaba ya tayar suka bar gurin batareda ko kallon inda suke yayiba har it’s har Hanifan Bai nuna yasan dasu dinba ya wucewarsa.