DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Herbal tea hajjo tasa ruqayyat ta dafo Mata da Zuma kadan aka kawo Mata ta gyara zamanta daga takuren datake dunqule Kan kujerar kusada hajjon ta karba tana kallon cup din ahankali kafin takai bakinta tafara kurba tana Dan rufe ido sbd ‘dandanon da baya Mata ko kadan a Baki ta kalla Hanifa dake Mata sannu tace”

Bani tissue akusa dake.

Hannu Hanifa takai ta zaro Mata tissues din dake gefenta na ‘dan Tara  yawu datakeyi sbd cikinta ta miqawa Naj din cikin kulawa tana cewa”

Sorry sweetie.

Gyada Mata Kai Naj din tayi tana dan lumshe idanu sbd saukar herbal tea din da zafinsa cikin cikinta yasa taji tana Dan Jin Kamar ciwon na Dan fadawa ta goge bakinta da tissue tana cigaba da kurban tea din harta shanye ta ajiye cup din hajjo na Mata sannu cikin kulawa.

Ahankali ahankali ta danji ciwon Yana fadawa Yana ragewa hartaji taji Dan saukinsa ba laifi sai alokacin ta miqe ahankali ta nufi dakinta Wanda take ita kadai yanzu aciki bayan an sauya Mata komai na dakin zuwa sabin furnitures dasukafi wainda aka sauya komai na dakin fari kamar yanda Hanifa ta bada zabin kalar sbd jalal ma yawanci komai na part dinsa farine,
Raba daki sukai da Hanifa sbd yanayin laulayin cikin hahifan dayakeda tsanani da zabe zabe Dan kuwa gabaki daya batason qamshin turare Wanda Naj Kuma ko zama tayi kusa dakai saita bar maka qamshinta me sanyi da dadi Wanda kamarma yariga yakama jikinta,
Hakama hahifa yawu takeyi wnda itakuma Naj takurane gareta,
Sai qamshin toilet din dakin nasu shower gels dasu feminine wash da bataso Wanda Suma Naj ke amfani dasu shiyasa Hanifan ta tarkata takoma dayan dakin dake palon aka sauya Mata wasu abubuwan dakin wainda bataso da sabbi.

Wanka tasamu tayi da ruwa masu zafi sosai tasake Jin Dan Jin qarfin jikin ta shirya cikin riga da wando masu Fadi sosai marasa nauyi ta saka hula ta Dan kwanta Dan samun bacci Bata Farkaba Saida Dr sa’id yazo aka tadota tafito sanyeda mayafi me Dan kauri rufe da jikinta ta qaraso palon tana tafiya cikin nutsuwa ahankali ta nufi kujera tana kokarin zama anty Amina na shigowa Nan suka zauna tare itama tana gaisawa da Dr sa’id din cikin sanayya da mutuntawa kafin ta miqe ta nufi dakin hajjo dake mutuniyar hirarta Dan suna qasan Kaka sosai da hajjon.

Kallonta Dr sa’id yayi kadan tareda Dan taqaitawa daga kallon Kai tsaye yace”

Menene matsalar?
Yaya kike jin ciwon Marar?

Numfashi ta Dan sauke tana dubansa a natse tace”

Wannan ne Karo na farko danake Jin wannan kalar ciwon duk da dai Ina ciwon Mara dama Amma wannan inajinsa dabam.

Kallonta yasakeyi Yana jeho Mata tambayoyi dabam dabam tana basa amsa tsawon lokaci Yana saurarenta ya hada amsoshinta Yana nazarinsu kafin ya dago Yana kallonta dason fada Mata abinda yake tunanin yasaka ciwon fin koyaushe wannan karon yace”

Ciwon mararki ya sauya yanayin tsarin ciwonsane ta hanyar tsananta da wani launin ciwom kamakon sha’awarki ta mace da aka motsa Wanda ke nuni da Baki taba ji ko aikata wani Abu daya taba motsa sha’awarki Wanda dakin Jima ahakan batareda an motsa Miki itaba kokuma yanayi yasa ta motsa da kanta Kika dauki shekaru ahaka kofofin sha’awan naki zasu rage qarfi matuqa kokuma suyi rauni sosai ta yanda zuwan sha’awan zaiyi Miki wuya.

Wani irin nauyi kanta ya dauka akaro na farko a rayuwarta da wata irin mummunan kunyar da Bata tabajiba ta Gama rufeta tako Ina har bazata iya kallonsaba saidai ta dago ahankali ta waiwayo duba Babu Wanda yafito bare yaji wannan mugun al’amarin daya sameta sukai ido biyu da Anty Amina data fito daga dakin hajjo takumaji abinda Dr sa’id din yafada Amma sbd ragewa Naj din nauyi da kunyar data hango tareda ita saita dauke Kai tana fuskewa tace”

Zan wuce nabarowa umma aikin hada sakon turarukan daza’a Kai mota gobe zuwa wani gari,Dr sa’id sai anjima.

Wucewa tayi batareda ta jira amsar Naj din ba sbd tasan bazata samu amsawar daga garetaba sbd halin datake ciki na tsananin Jin nauyi.

Babu wata kunya ko nauyin maganar dayaji sbd shi likita ne Babu kunya a tsakaninsa da patient dinsa Dan Haka Kai tsaye yabata shawaran ringa Shan ruwan dumi akai akai tareda bada shawaran zama guri daya da mijinta.

Tagane ma’anarsa ta cewa ta zauna guri daya da mijinta Dan Haka ko kallonsa bataiba tace”

Ngd Dr sa’id” tana miqewa daga zaunen shima ya miqe sukai sai anjima ya fice ita Kuma ta nufi daki tana dafa mararta datai nauyi.

Kwana biyu tagama period dinta ciwon Mara ya wuce Dan Haka ko maganar Dr sa’id Bata sake tunawaba bare sakawa arai taci gaba da sha’anoninta hankalinta kwance Babu tunani ko damuwar komai.

Yau da yamma sosai tadawo aiki sbd wani meeting da sukai me mahimmanci Wanda yasa take cikin farin ciki sosai sbd project ne dasuka Jima Suna buqatansa sai yanzu Allah yasa suka karbe.
Tana sanyo kan motarta cikin layin ta hangi qarin sojoji a kofar gidan Wanda yasa gabanta mummunan faduwa akaro na farko data tuna zai iya yiyuwa shine yadawo.
Sake faduwa gabanta yayi taji kaman tana neman shiga damuwa Amma dai ta danne ta qaraso suka bude Mata gate tashige da motarta tana amsa gaisuwar dasuke Mata daga ciki ta hanyar jinjina musu Kai da daga hannu.

Parking tayi tareda kashewa ta fito riqe da handbag dinta tasamu kanta da qin ko kallon daya daga cikin motocinsa dakeda alamar da ita akaje daukarsa airport ta dauke Kai ta nufi cikin gidan Kai tsaye tana nufar sashensu ma’ana na hajjo.

Da siririyar sallama ta shiga palon Kai tsaye tana kallon Hanifa dake zaune palon da tissue dinta ta yawu,
Gurinta ta qaraso tana sauke qaramin numfashi tace”

Maman baby Yaya??

Murmushin farin ciki Hanifa ta saki tana cewa”

Sannu da dawowa sirikar maman baby.

Naj din Bata tankata ba sbd yanzu tasaba da wannan neman fitinar da Hanifa keyi yanzu Dan Haka Kai tsaye daki ta nufa tana cewa”

Bari na tube nayi sallah yau na gaji sosai jikina na ciwo sosai.

Shigewa tayi daki tareda rufo kofar ta tana aje handbag dinta tareda Dan mayafin dake kanta ta tube tareda Kai kayan cikin laundry ta janyo towel ta daura tashige toilet.
Jin Ana Kiran sallar magriba yasa tafasa wankan tayo alwala tafito ta Sanya doguwar riga ta tafara yin sallolin Dake kanta saidata gamasu kafin ta miqe tana tubewa wayarta tahau ringing batabi ta kanta ba ta nufi toilet tashige.

Wanka tayo tafito ta shafa Mai kadan sai body mist da khumrah ta Sanya doguwar riga me qaramin hannu ta Sanya hular da Bata Gama rufe kanta gashin kanta dukaba tana kokarin fitowa taga lokacin sallar Isha yayi ta tsaya tayi abarta kafin ta dauko wayarta ta fito tana duba Kiran da aketa Mata tun dazu ga zallar mamakinta sai taga no din kamar ta santa ta sake dubawa taga 9misscalls Dan Haka sai mamakin Kiran ya Dan kamata ta nufi palon da hajjo da Hanifa ke zaune a dining ta nufa gurinsu Kai tsaye tana cewa”

Me maman baby keyi a dining hajjo itada baby bayason cin abinci a dining San……kasa qarasa maganarta tayi sakamakon Wanda idanuwanta suka Shiga cikin nasa Yana zaune kan kujerar da Bata hangosaba saidata iso gurin gabaki daya fararen idanuwansa masu rikitarwa a zubasu akanta jikinsa sanyeda jallabiya fara qal tana qyallin daya tabbatarda tsadarta,
Samun kanta tayi da kallon hajjo ahankali kafin ta maida kallonta kan Hanifa dake kallonta da murmushi a fuskarta sai kawai ta juya zatabar gurin Kai tsaye taji muryarsa a kame yace”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button