DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Miqewa Naj din tayi tana cewa”
Bari nayi wanka nafito zamuyi mgna akan Isma’eel ya kirani dazu akan maganar zuwanki ganin likita A Jamaica.
Kallon kyakkyawar fuskarta Hanifa tayi tana murmushi tace”
Allah sarki Zawj.
Da yanayi na sanyi Naj ta kalleta zuciyarta na yin sanyi da dukkanin wata damuwar Hanifa ko ciwonta.
Toilet din dakin nata ta shige Dan dama wanka zatayi Hanifan ta shigo.
Bayan shigarta wanka miqewa Hanifan tayi ta sauko daga kan gadon ta zura flat slippers dinta na Jimmy choo ta fita dakin ta nufi gurin umma dake zaune har lokacin tana aikin zuba wasu turaren wuta masu tsananin qamshi ta zauna gefen umman tun kafin ta qarasa zama umman tace”
Kun gamo shawaran yanda zaku fuskanci Dattijo da Dadah idan Maganar aurenta da Abbas ta fasu Dan nasan wannan doguwar fuskar da Kika shigo da ita bata lafiya bace Dole akwai abinda yake faruwa tsakaninta da Abbas.
Dan guntun murmushi Hanifa ta sauke tana Taya umman rufe kwalaben turarukan tace”
Umma meyesa kuka kasa gane irin taurin zuciya da qarfin imanin da Naj take dashi sbd ba kowane zai iya hadiyewa ba yakuma danne irin Gori da takura tareda cin fuskan da ake Mata akan rashin yin aure ba?
Umma kowa Yana yiwa Naj kallon taqi aure sbd zurfin ilimi da karatun bokon datayiba a cikin gidan Nan hakama Ana Mata kallon wadda ta Raina maza sbd ganin Kamar matsayinsu da nata daya ne Wanda umma keda Kika haifi Naj kinsan ba Haka takeba kawai dai ita Allah Haka yayita miskila me halin ko oho ga abinda ake fada akanta bayan Haka shi fa aure nufi ne na Allah Kuma ba lallai ne ita lokacin nata auren yayi ba idan lokacin yayi zatayi.
Hmmn Hanifa nagaji da bin bayan Najma akan maganar fasa aurarrakin Nan nata da akeyi kusan Kashi biyar tun Ina yadda da qaddarane a gaskia yanzu na yadda da hadda halinta na miskilanci Wanda kesa mazan ganin Kamar tafi karfinsu ne kokuma tana tuna tafi karfin nasu,
Kunfi kowa sanin yanda Dadah da Dattijo suka sakoni gaba a cikin gidan Nan akan Najma
Kullum fa qara shekaru akeyi ba ragewa ba yanzu ke da Allah yakawo rabo na haihuwa aurenki da yanzu ba kinada yara biyu ko ukuba koma hudu idan anyi haihuwar ritsa Amma Sam Naj ko ‘yar damuwar Nan Bata nunawa kullum itace a nutse a kammale saikace wata lissafi ahaka takeson qarewane saidai aiki kawai..
To ku zauna ku dasa sabuwar shawara wannan karon wlh Dattijo rantsuwa ce a bakinsu shida Dadah matuqar aurenta da Abbas ya fasu to wlh bazata rufa sati ba agidan zasu aura Mata duk Wanda ya samu ciki kuwa hadda sojojin dake gadin gidanku yace zai kaiwa tayi idan hakan ta faru Ni kaina danake mahaifiyarta wlh zuciyata zata iya bugawa bare ita Dan Haka ki zaunar da ita kuyi shawara koma menene matsalar su zauna suyi sulhun abarsu itada Abbas din asamu ayi auren Nan ta tafiyarta ta huta Nima na huta da zancen kullum din.
Batasan wane bayani zata yiwa umman ta fahimta ba sbd matsuwar su dattijon tariga tasaka umman itama gajiya tana kasa fahimtar ‘yar tata,
Tana tsananin qaunar Naj tamkar ‘yar uwarta ta jini dasuka fito ciki daya Dan kuwa tsananin qaunar datake Mata har kasa tantance cikin su biyun tsakanin ita da marshal batasan waye tafiso ba duk da shi din jinintane dasuka fito ciki daya,
Bazata iya Bari Naj ta cutu takowane irin Hanya ba Dan Haka ita da kanta zata nema Ganin Abbas lamido suyi magana idan har yanason Naj da dukkanin zuciyarsa da gaskia to yakamata ya sauya su fuskanci rayuwar aure zasuyi su fahimci juna tun yanzu.
Idan har zai qaunaci Naj da gaskia zaifi Mata ace Dattijo yabada auren Naj wa duk Wanda yasamu.
Wanka ta fito taga Hanifan Bata dakin tasan tana gurin umma ko anty Amina Dan Haka Kai tsaye ta nufi gaban mirror ta zauna ta kalli fuskarta zuwa kirjinta da kafadunta dake bayyane suna wani qyallin haske da samun lafiyar fata ta maida kallonta kan fuskarta datafi komai kyau da daukan ido atare da ita ta lumshe fararen idanuwanta ahankali tareda sauke numfashi kadan kafin ta janyo lotion na jagggins tana shafawa kadan kadan Dan batason Mai da yawa Ta miqe bayan ta shafa turaren POSSES ajikinta tareda mist na Rednight ta zare band din kanta ta gyara daurin gashinta tayisa sako sako sbd Taji dadin kan nata ta nufi wardrobe ta Ciro doguwar riga Mara nauyi zata saka wayar Hanifa data bari kan mirror din nata takawo haske tana vibrating ahankali ba qara sbd Wanda Dabi’arsune rashin sakawa waya qarar ringing Dan kusan itace ta koyawa Hanifan hakan qarar waya na damunta shiyasa Sam wayarta Bata qara idan Ankira saidai vibrating shiyasa itama Hanifan ta koya sbd Naj din.
Ahankali ta waiwayo ta kalla wayar taga sunan dayake Kai MARSHAL
dauke Kai tayi tana cigaba da saka kayanta Dan tunda takeda Hanifa Bata taba daga wayar ‘dan uwanta ba idan yakira Wanda shi kadaine kawai Bata daukan wayarta idan shine yakira idan har Bata kusa tun kuwa tasowarsu suna qananu haryanxu.
Sanin baya Kira biyu ‘daya yakeyi yasa ta sake waiwayo wayar tana kallon sunan destination dinda caller ID ta rubuto HAWAII US STATE
Hanifa Babu wani Abu a duniya dayafi Mata qanin nata Wanda su biyu kacal mahaifiyarsu ta Haifa ta bar duniya Wanda tazarar shekara uku ce a tsakaninsu yanayin aikinsa da girman matsayinsa yasa baya tareda ita wayama sai yasamu lokaci suke iya Yi Dan Haka Babu abinda Hanifan Bata Wasa dashi irin waya da marshal din Dan Haka bazata so ta rasa kiranba takai hannu a natse ta dauka tareda nufar kofa ta bude ta fito ta kalli zainab dake kusa tace”
Miqawa Hanifa wayarta Ana Kiranta.
Karba zainab tayi ta nufi Hanifan da sauri ta miqa Mata cikin sa’a kuwa har lokacin Kiran Bai katseba tana ganin me Kiran ta dauka tana Kiran sunansa cikin tsananin kaunarsa da kowa ya shaida kaunace me girman gaske a tsananinsu.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR 2022????
Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,
Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,
NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA
SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA
MAMUH GEE
DEEN MARSHALL
HAFSAT RANO
HALIN GIRMA
BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA
Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
Zaku tura kudin a
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Sai shedar payment dinki a????????????
08184017082
Kokuma katin waya na MTN anan????????
09134848107
[1/9, 7:53 PM] +234 901 554 3771: DEEN MARSHAL
Mamuhgee
3
Komawa Naj din tayi Dan tayi sallah tana Shiga dakin tun kafin Hanifan ta qaraso dakin ta tayar da sallarta Dan tasan Babu ranar da zasuyi wayan Hanifan Bata hadasu ba suka gaisa Wanda daga ita harshi din basa buqatan gaisawar sbd shi dai Bai taba gaidata ba hakama itama batajin zata iya gaidashi din tun koba komai shine qani Amma gabaki daya matsayi dayake dashi da jin yazama billionaire yasa baya iya gaida mutane kokuma tace wasu mutanen tunda Yana gaida Hanifa da hajjo kakarsu,itadaima gabaki daya Bata wani buqatan shiga rayuwar kowa musamman irin tasa rayuwar wata iri kamar ta Mara kowa komai nasa yawanci kafin suji sunfara gani a labarai kullum koken hajjo da Hanifan rashin dawowarsa akai akai duk da dai taga kamar yafara sauyawa Dan yanzu Yana Dan yin kokari a shekara yazo so uku ko so biyu Haka.