DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Cire wayar tayi daga kunnenta tareda kashewa Kai tsaye batareda tasamu damar cewa maganarsa ko kalma dayaba ta maida wayar jaka tana Shirin Shiga mota ta hangosa tsaye a balcony dinsa da mug a hannunsa Yana kurba ruwa masu dumi kadan da Zuma kadan aciki Wanda yake dabiarsa kullum Shan ruwan zafi masu Zuma kadan aciki.
Sanye yake da three quarter black da armless shirt sai slippers brown a qafarsa yafitone sbd fresh air ya shigesa Dan exercise din dayayi gabaki dayansa yasashi zufa shiyasa ya fito Yana Shan fresh air din jikinsa sai daukan ido yakeyi acikin baqaqen kayan dake jikinsa.

Dauke Kai tayi tana ciro keys na motarta ta bude ta shige tareda tada motar tana Danna horn aka bude Mata gate ta figeta ta fice daga gidan
Cigaba da abinda yakeyi yayi batareda yabi inda motar tata taficeba da ido sbd tun fitowarta daga sashen Dad Alfa idonsa ya sauka akanta ya qarewa kayan jikinta idon Yana tsayar da idonsa Kan Dan qaramin qugunta da skirt din jikinta ya zauna akai daga sama ya Dan rintse idonsa Yana daukesu daga kanta.
Ciki yakoma kawai sbd Jin iskar ta sauya zuwa wani yanayi mara Dadi.

Tana Isa office tayi parking ta fito ta nufi ciki Sarah na qasa tana jiran isowarta Dan Haka kai tsaye tan isowa gurin meeting din suka wuce San sama hanyar office din chairman wato Abbas.
Ko data Shiga shareholders din companyn duk sun iso ita zatai representing Alfas,Marshal da Dad Alfa.

Sai qarfe biyu da arbain suka fito meeting din Dan Haka Kai tsaye ta wuce office dinta Dan duba wasu takardu tanayi tana duba agogo sbd komawa gida da wuri tunda tasan aikin dake jiranta a gidan.

Sai qarfe uku da hamsin da uku tasamu kanta ta fito tana sanarda Sarah Dake biye da ita takardun dazata kaiwa Abbas ya duba kafin goben a zauna next meeting.

Wayartace tahau vibrating ta Ciro tana dubawa cikin Dan yamutsa fuska ta kashe wayar tareda maidawa cikin jaka tana kallon Sarah tace”

Ki tabbatarda kin kaiwa chairman duka takardun da ake buqatan ya duba kafin goben sbd bana buqatan wani aiki dazaisa yaringa kirana.

Ok Inshallah.

Fitowa tayi tafada motarta tabar companyn gabaki daya tana sake duba agogon hannunta.

Tana Isa bataga motorsaba a harabar gidan hakama sojojinsa Dan Haka tasawa ranta sun koma kenan ta fito ta Kai tsaye ta nufi sashensu.

Bakowa a Palo hajjo na sallar la’asar a dakinta, Hanifa Kuma na daki tana baccin yamma.

Dakinta ta nufa Kai tsaye saidata Dan zauna ta huta kafin ta tashi tasauya cikin doguwar rigar roba Mara nauyi tayo alwala tayi sallah kafin ta fito ta nufi dakin hajjo.

Sai yamma sosai ta fito ta Isa dakin Hanifa har lokacin bacci takeyi ta Dan tayarda ita cikin kulawa sbd maraice yayi ta kamata ta tashi ta nufi toilet kafin it’s ta nufi kicin Dan aikin abincin dare da itace yau zatayi.

Aiki suka hau yi itadasu ruqayyat masu kama Mata wasu ayyukan
Suka Dora tuwon semo da miyar waterleaf da nama kadan aciki sbd Jin daga bakinsu ruqayyat cewan idan Marshal na gari ba’a saka nama de yawa a abinci bayason nama sosai duk da dai bawai dansun fada tayiba itama Naman Bai wani dameta bane sosai hakama Hajjo itakuma sbd tsufa da manyanci.

Fruit salad tayi sbd Hanifa me juna biyu sai normal peach drink da black lemon tea me zuma data dafa Dan gidan gabaki daya kusan kowa mayen tea da zumane duk hajjo ce ta koyar dasu hakan tun suna qananu.

Basu Gama aikinba ta fito kicin sai bayan sallar magriba Dan Haka tana fitowa Kai tsaye ta nufi dakinta tafara tubewa gabaki daya ta nufi toilet yin wanka.
Ta Jima ciki kafin tafito daureda towel me girma blue tazo tafara saka doguwar riga tayi sallar magriba Da Isha kafin ta zare rigar ta zauna gaban madubi tashafa Mai kadan da spray din Chanel ta sako doguwar riga Mara hannu ta fito daukeda wayarta lokacin hajjo da Hanifa tuni suka Isa dining Dan Haka Kai tsaye itama can ta nufa tana ajiye wayarta Kan kujerar palon.

Bata ganshiba Amma hancinta ya shaqo Mata qamshi Tom Ford turarensa Dan Haka ta rage takun tahowar tata tana Dan Kai idanuwanta kujerar dayake zama a dining din wadda ba’a hangota sai ankawo cikin dining area din tana Kai idonta gurin tagansa zaune da tea gabansa Yana tiriri cikin Dan qaramin cup,Bai dagoba bare ya nuna yasan da zuwanta saidai ta tabbatarda yaji zuwan mutum agurin ta ‘dan dakata kadan zata koma saikuma ta fasa ta qaraso ahankali tana Dan fuskewa batareda itama ta kalla inda yakenba tace”

Sorry nabarku jirana.

Bata zaunaba ta zubawa hajjo abincin kafin tazubawa Hanifa fruit salad da tuwon Dan kadan sai ta zuba itama Dan kadan Takoma ta zauna sai alokacin ya kalleta baice komaiba ya qarasa Shan tea dinsa ya miqe ahankali hajjo ta kallesa tace”

Abincin fa?
Najma kiyi serving mijinki abinci yagama Shan tea din.

Wani irin kallo yayi Mata dayasata kusan sarqewa duk da Bata dagoba Amma tanajin kallon ajikinta ga rigar jikinta duk tasata Jin haushi da takaicin fitowa ahaka.

Da muryarsa me kamewa yace”

Takaimun abincin acan ba anan zanciba.

Yana Gama fadar Haka ya wuce yabar gurin batareda yasake kallon inda takeba yabarta da wani irin takaici,baqin ciki da takaicin rashin gane meyake nufi da “Takaimun”
Wa yake nufi da kalmar Dan Bata tunanin da ita yake Dan kuwa bataga ranarda hakan zata faruba takai kanta sashensa to tace tazo ubanme.

Ganin idon hajjo akanta dake nuni da zallar rashin Wasa na tayi abinda yace din yasata sarqewa tana sakin tari ahankali
Hanifa ta dauki ruwa ta miqa Mata ta a cewa”

Sorry sweetie,sannu bi ahankali kije kidawo tukuna saiki qarasa.

Da manyan idanuwanta ta dago ta kalli Hanifa wannan karon Kamar sun sauya da yin Dan ja da Kamar hawayen takaici dasuka Dan ciko aciki sbd halinda take Jin zuciyarta aciki na takaici saidai Kuma Bata hango ranarda zata iyayiwa hajjo gardamaba.

Hanifa dakanta ta miqe taje ta dauko Kaya ta hada Masa abincin da komai aciki tasaka a basket ta miqawa Naj din tana cewa”

Bari na dauko Miki wayarki da hijab.

MAMUH

ZAFAFA BIYAR 2022????

NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA

SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA

MAMUH GEE
DEEN MARSHALL

HAFSAT RANO
HALIN GIRMA

BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA

Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

Zaku tura kudin a

6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank

Sai shedar payment dinki a????????????

08184017082

Kokuma katin waya na MTN anan????????

09134848107

DM 25
Miqewa take kokarin Yi ya ajiye cup din dake hannunsa ya kalleta da mamaki akan fuskarsa datake sata dauke idonta daga kallonsa ya mayarda ita zaune kan qafafun NASA tareda zura hannayensa ya rungumota ta baya Ya zuro kansa ta wuyanta daidai kunnenta ya bude Baki ahankali ya furta”

Me kike yiwa gaggawa na guduwa bayan kin shanyemun yoghurt¿
Kinsan me hakan ke nufi kuwa?””” Ya qarasa maganar Yana shafa fuskarta da tasa.

Yi tayi kamar bataji abin daya fadan ba taci gaba da kokarin kwacewa daga jikin nasa yasake shigewa da ita jikinsa Yana kallon wuyanta dayake shaqo qamshi daga gurin ya lumshe fararen idanuwansa ahankali kafin ya saketa ahankali Yana Dan dauke kallonsa daga kanta ta miqe tsaye fuskarta a daure sosai duk da tanajin takaici da kunyar kanta data Sha yoghurt din gashi Yana kawo Mata wani zancen kunya da takaici Dan kuwa tasan fassarar kalmar daya fada ta cewan” tasan me Shan yoghurt dinsa yake nufi”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button