DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin kulawa ta taimakawa Hanifa da wuyan ya riqe Mata sosai kamar ba lafiya ta kwanta ba tasamu ta danyi breakfast sai alokacin takira Dr said Wanda shine likitan Hanifan ta sanar dashi.
Dayake yanason ganin Naj din sai yace zaizo yakawowa Hanifan magani kafin ya wuce aiki.
Kafin Dr said din yazo taje dakin hajjo ta gaidata tareda Hado Mata ruwan dumi da Zuma Wanda itace hajjon ta koyawa Naj din Sha kasancewan itama abincin masu nauyi Basu cika Bata lafiyaba.
Bayan ta dan sha ta dago ta kalli Naj din tace”
Zaki tafi office ne?
Da fararen idanuwanta ta Dan kalli hajjon ta maida kallonta kan agogon dake daure a hannunta tana cewa”
Eh Amma ba yanzu ba Ina jiran Dr sa’id ne zai kawo maganin Hanifa wuyanta ya riqe Bata iya motsawa.
Dan numfashi hajjon ta sauke tana Dan jinjina Kai irin na manya tace”
Yau Kuma da riqewan jijiya ta tashi
Allah yabata lafiya.
Amin Naj din tace tana miqewa sbd ganin Kiran Dr sa’id akan wayarta.
Kamar dai yanda yasaba da gidan da dukkanin iyalan gidan tareda farin sani da securities na gidan sukai Masa amatsayin likitan Hanifan yasa Yana zuwa Kai tsaye aka bude Masa qaton gate din gidan yashigo har ciki da motarsa Amma iyakacinsa gate din farko baqi basa shigowa da motocinsu gate na biyun Dan Haka Yana parking ya fito yasake gaisawa dasu Mike ya wuce ciki Kai tsaye.
A babban palon farko na gidan ya tsaya Wanda yake matsayin na baqi ya zauna bayan su ruqayya sun kawo Masa ruwan black tea suna tiriri sun ajiye Masa kenan saiga Naj din ta fito ta qaraso tareda zama kujeran dake kallon tasa Tai Masa kallo daya ta Dan dauke Kai tana cewa”
Barka da safiya Daddyn Naufal.
Wani irin kyakkyawan murmushi ya sauke sbd a duk lokacinda takirasa da dadyn Naufal zancen na tsumasa sbd hakan na nuni ne da kusanci a tsakaninsu har wani lokacin Jin yake inama ace itace mahaifiyar Naufal din.
Kwarjininta yasa duk yanda mutum yaso baya iya Mata kallon qurulla Wanda shima wani lokacin hakan nasashi Jin fargaban zai iya mallakar Naj din kuwa Dan dai gskian magana bakowane namiji ne zai iya cika idon Naj din ba haryayi Mata irin kallon tsaf kona qurullaba saidai kuwa idan shima nasa kwarjinin ya take nata ne hakan zai iya yiyuwa.
Dan numfashi ya sauke Yana janyo qwazonsa na namijin daya ciki ya sake kallonta yace”
Barka da fitowa Naj.
Ya hajjo ta tashi lfy?
Yasu umma ma?
Alhmdlh” tafada a taqaice tareda sake kallonsa tace”
Maganin Hanifan.¿
Miqa Mata qaramar ledan maganin hannunsa yayi Yana cewa”
Kada a shafa Mata komi agurin Tasha maganin kawai saita gasa jikinta da ruwan dumi shikenan zai sake.
Ok bari nabata maganin yanzu coz tana buqatansa yanzu Nan.
Ta dauka lokaci sosai kusan awa daya kafin tafito cikin shirinta tsaf na zuwa office ta fito daga gidan gabaki daya tashiga gidansu cikin sa’arta Dattijo baya Nan bare maganar fadan jiya na Dadah ya tashi Dan Haka Kai tsaye sassansu ta nufa
Ummanta na daki tana ayyikanta taje ta gaidata umman ta Gama yimata Gore goren da tariga tasaba dasu ta fito suka hada ido da anty Amina dake zaune tsakar gidan tana waya Ta taso tana kashe wayar suka shiga dakin Naj din tana sake bayyanar Mata da kada kalaman umman su daga Mata hankali tacigaba da rayuwarta cikin salama sbd Haka Allah ya tsaro Mata ba komai bane rashin auren da wuri tunda su ganshinan sunyi sun fito din.
Murmushi kawai Naj tayi tana cewa”
Anty Amina Ni wlh kinmafi bani tausayi sbd fadan umma akan fitowan Nan Taki.
Kiji yarinya ke bakiga tausayin kankiba
Duk rigimarsu gwarani nayi harna tara yara nafito
Gwara dai kiji tausayin kanki kisamu kiyi shine rufin asirin.
Wani murmushin kawai tasaki tareda daukan abubuwan dazata dauka ta fito ta fice
Tana fitowa ga mamakinta Dr sa’id na Nan waje Yana jiran fitowarta ya ajeta office Dan batason doguwar hayaniya yasa kawai tashiga suka wuce Amma cikin ranta tana Dan fatan kada su tadda Abaas a ALFA’S din sbd bazata iya daukan hayaniyarsa da fitinarsaba ciwon Kai kawai zai sakar Mata na Wunin gaba daya.
MAMUH
ZAFAFA BIYAR 2022????
Ina masoyan Kuma mabiya littaffan zafafa biyar wainda sukai fice gurin kawo muku littafansu masu tsafta da ilimantarwa tareda nishadantarwa,
Wannan shekarar sun dawo muku da wani sabon salon Kamar kowane zuwan inda suka kawo muku dada’dan labaransu da bazaku taba Dana sanin biya ba,
NANA HAFSAT(MISS XOXO)
SO DA ZUCIYA
SAFIYYA HUGUMA
DABI’AR ZUCIYA
MAMUH GEE
DEEN MARSHALL
HAFSAT RANO
HALIN GIRMA
BILLYN ABDULL
TAKUN SAKA
Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka????????
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
Zaku tura kudin a
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Sai shedar payment dinki a????????????
08184017082
Kokuma katin waya na MTN anan????????
09134848107
DEEN MARSHAL
Mamuhgee
5
Duk yanda Dr sa’id yaso suyi mgn Bata yiyuba sbd ganin motar Abaas lamido na cikin gurin hakan ke tabbatarda Yana Nan Kuma ko ayanzu Haka yasan Yana iya ganinsu daga sama ta office dinshi
Shi kansa baya buqatan iya zallan wulaqancin Abaas din a bainar jama’a bakuma Dan komai ba sai Dan Naj dayasan tana iya kokarinta gurin tolerating din Abaas din Wanda gabaki daya Bai cancancetaba Kota Ina Sam sam Allah ne kawai ya bashi babbar sa’ar samunta idanma shine ya aurentan kenan Dan shima Bai cire raiba yanama Dan ji a jiki jikinsa Kamar shine ma me sa’ar aureta din kowama ya huta.
Fitowa yayi ya zagayo zai bude Mata ta bude da kanta ta fito da Dan guntun murmushi akan fuskarta tace”
Thanks Dr.
Jinjina Kai yayi Yana kallonta yace”
Atashi lafiya.
Ya juya ya koma cikin motarsa ya tada yabar gurin bayan tuni ta shige alfas din Sarah dake jiran isowarta ko Dama Bata hayeba tana qasa tana Nan reception tana jiranta sbd bazata fara isaba it’s kadai Dan shakkar Abaas zai iya Mata komai kafin Naj din taqaraso bazata iya ba gskia Dan yanda ya qware agurin cin zarafin mutum ta yanda duk hakurinka da dannewarka sai ranka yayi mummunan baci zata iya kasa hkr ta maida Masa mgna saidai ya koreta aikin Amma sbd Naj yasa itama take kokari tana hadiyewa tareda jinjinawa jarumta da qarfin zuciya irin na Naj datake hadiye maganganunsa.
Ma’aikatan dake gurin na qasa da Naj din gaidata suka hau yi suna Mata barka da isowa ta amsa musu tana wucewa kaman yanda ta Saba suka wuce Sarah na gefenta tana fada Mata Abaas yariga ya iso yau tunda safe ya iso office din.
Suna Isa cikin office dinta ta ajiye handbag dinta tareda waiwayo ta kalli Sarah dakyau kafin ta bude Baki tace”
Sarah daga yau banason maganar Abaas a office please
Zuwansa da rashin zuwansa duk bana buqatan sani okay??
Yes ma’am.
Juyawa tayi tana Shirin zaunawa aka turo kofar aka shigo
Sarah ce kawai ta juya tana ganin Waye ta Dan matsa gefe tana cewa”
Good morning chairman.
Ko kallonta baiyiba ya qaraso ya zauna kan sofa dake office din tana ganin Haka ta sulale ta fice bayan ta ajewa Naj laptop dinta.
Har lokacin Naj dake tsaye Bata juyoba tana hankalinta nakan wasu takardu dake hannunta ta sai qamshinta me sanyi da Dadi dayaketa sake gauraye office din Hadi da sanyin AC Wanda suke qara qona zuciyar Abaas din.
Dagowa yayi ya kalleta tareda zubawa fuskarta dakeda wani irin sanyin kyawu da nutsuwa tareda wani irin fizgar mutum ido kafin ya taso ahankali ya dawo gabanta ya tsaya Kai tsaye yace”