DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

Meyasa Dr sa’id ne kawai zai kawo office?
Dan dagowa tayi ahankali ta kallesa tareda rufe takardun hannunta din ta ajiye ta koma ta zauna a natse tareda fiddo wayarta daga jaka cikin muryarta me kamewa tace”
Yaje duba Hanifa ne ya wuto Dani.
Rintse idanu yayi cikin qoqarin controlling zuciyarsa yace”
Kullum bashida aikine saina zuwa dubata kokuwa itace kullum batada aiki saina kwantawa ciwon dashine zaije Yana dubata ta yanda ke Kuma zai ringa kasancewa dake kokuwa nine da akewa kallon Mara hankali akeson shashantarwa da wannan zancen kullum”” ya qarasa fada Yana Dan daga murya sbd maqura da bacin ran nasa yake qara kaiwa.
Wannan karon kallon mintuna biyu cif tayi Masa tanason fahimtan idan Abaas din Yana lafiya kokuwa sbd kalamansa sun Sosa ranta Dan kuwa kamar Yana cin zarafinsu ne daga ita har Hanifan.
Kamar bazata tankasa ba saita dauke kallonta daga kanshi tace”
Zaifi idan ka tsaya da rashin fahimtanka a iya inda ka Saba kawai.
Cikin fushi yace”
Alaqarki da likitan Nan ta wuce dukkanin hakurina sbd Naga kin sabarwa kanki iya zama cikin motarsa Dan Haka tunda kin yanke zama taxi motar kowa saiki zaba tsakanin Ni ko shi waye Dan bansan ya alqarku zata cigaba da kasancewa ba bayan munyi auren….
Jajir idanuwanta sukai saidai har lokacin Bata dago ta tankasaba saima hakan yaqara qunan zuciyarsa yaci gaba da fada cikin maganganu masu dacin sauraro Amma taqi sake ko dagowa ta kallesa hakan yaqara lalata duk wani sauran hakurinsa ya fice ransa amatuqar bace.
Harya Gama ya fice tana zaune a inda take da wayarta a hannunta tana dubawa,
No Hanifa takira Bata daukaba Dan Haka takira no hajjo taji Yaya Hanifan take hajjon ta sanar da ita cewan wuyan dai Bai sakiba har lokacin.
Sama sama tasamu tayi wasu ayyukan ta tattara tabar office din Takoma gida sbd hankalinta gabaki daya yakoma kan Hanifa sbd tasan yanayin ciwukanta yanzu a Haka saita share kwanaki wuyan a riqe.
Tana Isa Kai tsaye gidansu Hanifan ta sauka Koda ta iso jikin yadan qara tsanantawa Hanifan Dan Haka kamar dai koyaushe itace tareda ita,itace tasan ciwonta da damuwarta da kulawa da ita bayan hajjo wadda itakuma tsufa yazo Mata bazata iya wani abun ba.,
Tun suna secondary Naj tasaba da kulawa da Hanifa sbd duk gata da tarin dibbin dukiyardasu Hanifan suke dashi basa tareda kulawa ta wani Dan uwa,
Masu aiki sune komai nasu sai hajjo wadda itama dai komai masu aikin ne keyi idan har Hanifa na buqatan kulawa da soyayya irin ta uwa to agurin umman Naj ne take samunta sbd umman da mahaifiyarsu aminai ne Suma tun yarinta shiyasa ma Suma suka taso Kamar umman ce uwarsu,
Umma na tsananin qaunar Hanifa Wanda yasama Hanifan kejin qarancin rashin uwa fiyeda DEEN Wanda shi asalima ko uwar tasa Bai saniba sbd gurin haihuwarsa ta rasu shiyasa ta taso a wani irin miskilallan mutum na qarshe sbd bai taso cikin hayaniyar taron mutane ba tun fara high school dinsa yabar qasar Yana Hawaii acan yayi karatunsa acan yake rayuwarsa ta matsayin babban Navy marshal Wanda zallan iliminsa da yakaisa acikin shekarunsa da basuyi yawa ba hakan Kuma yasa da yawa manyan mutanen Nigeria dake can harma Dana wasu qasar suna kawo sha’awan son hada zuria dashi saidai haryanzu kaman Shirin aure baya gabansa Dan baitaba sha’awan aure yanzu ba duk da hajjo da Hanifa sun fara nuna damuwarsu akan hakan Amma Yana dakatar dasu baya buqatan su takurawa junansu shiyasa ma basa matsa Masa sosai da maganar Dan sanin bayason yawan nanata zance.
Umman Naj itace ta raini Deen din tun bayan rasuwar mahaifiyarsu har Saida ya girma yakai shekaru biyar kafin yafara kwana gidansu ahaka ahaka harya koma gidansu gabaki daya sbd lokacin dad dinsu yayo aure shiyasa a duniyarsa bayan hajjo da Hanifa da dad dinsa umma itace uwa wadda tabashi so da qauna ta uwa duk da itama umman ta Saba sosai da halinsa na ko inkulan tun Yana yaronsa saidai duk yadawo Yana zuwa har cikin dakinta ya zauna tayita kulawa dashi danma yanzu sbd yawan gidan nasu yasa ya daina Shiga idan yazo saidai tayi girkin abincin dayafi so ta aika Masa daga baya taje har palon hajjo acan suke Yar firarsu ta uwa da ‘da.
No din Dr sa’id Naj takira saidai Bai daga ba Dan Haka tayi tunanin Yana aikine kokuma yashiga CS Dan yawanci hakan kesashi barin waya office Dan Haka Bata Bata lokaciba tasake hada ruwan dumi ta gasawa Hanifan jikinta tareda sake Bata magani gashi duk yanda taso Hanifan taci abinci takasaci qrshe dai da kanta ta hado Mata ruwan dumi da Madara da Zuma tasamu ta iya Sha tayi bacci.
Saida Hanifan tayi baccin tasamu ta tube tafada toilet tayi wanka tayi sallah tafito palon hajjo ta nufi dining ta zubo spaghetti kadan da salad tadawo ta zauna gurin hajjo suna Yar firarsu akan rashin lafiyan Hanifan da tuni Dad dinta yafara Kira sbd hajjon data fada Masa
Shima Isma’eel mijinta tun Naj na office yake Kira sbd Hanifa Bata daukan wayan kowa.
Tana Gama cin abincin kicin kenan saiga ummanta tashigo tareda zainab Yar gaban goshinta ayanzu kenan ‘yar anty Amina.
Zama umma tayi ita Kuma zainab Naj ta miqa Mata plate din hannunta tana cewa”
Ki Kai kitchen.
Sosai umma ke girmama hajjo tamkar mahaifiyarta Dan Haka firarsu suka Dora daga nan Naj na gefe tana aiki a laptop dinta saiga Kiran Abaas yashigo wayarta ta dauke ido daga kan wayar tana cigaba da aikinta yasake Kira Bata daukaba har so uku ko kallon wayar Bata sake yiba.
Sai yamma sosai bayan ma Hanifa ta farka su umma suka tafi Takoma gurin Hanifan wadda video call din marshal yashigo wayarta daidai shigowan Naj din.
Qarasowa tayi gurinta tana Kiran sunanta cikin taushin muryarta tana cewa”
Yaya wuyan?
Nuna tayi Mata da wayarta ahankali tana cewa”
Please ki amsa mun Kiran.
Kallon wayar Naj tayi taga sunansa baro baro ajiki takai hannunta ta dauka wayar tana dawowa gefen Hanifan ta zauna ahankali tareda daukan Kiran ahankali kyakkyawar fuskarsa ta bayyana akan wayar Yana zaune palon gidansa dake Honolulu Hawaii US sanye cikin black three quarter da black armless shirt dasuka matuqar bayyanarda hasken fatarsa data Gama renuwa acikin hutu da lafiya sai daukan ido fatar jikinsa takeyi sbd yanayin kayan dake jikinsa dauke Kai Naj tayi tareda miqawa Hanifa wayar tana tashi daga gurin Dan gidansu takeson Shiga Dan Haka Kai tsaye ta fice.
Wayarta ce kawai a hannunta ta fito daga gidan ta nufi kofar gidansu ta shige ta nufi sashensu Kai tsaye saidai tana Shiga ta tadda Dattijo tsaye ga Dadah a zaune hakama ummanta dukkaninsu suka zubo Mata ido Banda ummanta da abun duniya ya taru yayi Mata yawa idanuwanta sun kada sunyi jajir da alama dai ba lafiya ba.
Qarasowa tayi cikin nutsuwa tace”
Dattijo Ina wuni,
Dadah barka da yamma.
Ko kallonta dadan bataiba sbd wannan karon tsaf tagama shirya duk wani rashin arziki da Naj din Bata tunani akan wannan maganar.
Kallonta Dattijo yayi da kyau Yana gyara tsayuwa da gyaran murya yace”
Ki saurareni da kyau kiji abinda Zan fada Miki sbd nafadawa mahaifiyarki kalma bayan kalma Amma Naga kamar ke din kinason watsar da maganar Kamar yanda kike watsi da masu neman aurenki,
Nafada naqara fada wallahi tallahi wannan karon kika Kori abbas da halinki yace yafasa auren Nan wallahi duk Wanda nasamu aura Miki zanyi bazaki maida wata a gidan Nan ba,
Yafara gajiya da halinki yazo ya sameni dazu ransa amatuqar bace na bashi hakuri akan za’a matso da bikin Nanda wata daya ma ayi a huta Dan Haka acikin watan Nan daya Kikai Masa abin dayasa yafasa wannna auren keda mahaifiyarki ku shirya hukuncina dazai biyo baya.