BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

Comment
nd
Share

Sis Nerja’art✍????
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-350771435465066/insights/?section=likecount&referrer=home_page_panel

Congratulations my beebah cute for completing ur amazing nd brilliant novel MAFARKINA more grace to ur golden elbow
keep d fire burning dear, so much love you????

Page 3⃣0⃣

Tunda haydar yafita daga d’akin sapna cike da takaici tabi k’ofar da kallo ji take kamar tad’aura hannu bisa kai tafasa k’ara , dasauri tafito tanufi d’akin ummah cike da tashin hankali ko sallama batayiba, wajen ummah tanufa, kallonta ummah take tace lafiya sapna naganki haka? Sapna kwallah ce tacika mata ido tace ummah wai dagaske aure zakiyi min kuma haydar zan aura? Murmurshi ummah tayi tace insha Allahu sapna kigode ma Allah domin kinyi sa’a haydar mutumin kirkine kuma na tabbata zai kula da ke ko bayan raina, sapna zabura tayi tamik’e tsaye tace ummah kirufa min asiri kibarni inza6i wanda nakeso wlh yaya haydar baya sona nima kuma bana sonsa, ummah cikin 6acin rai tace ke sapna ya isheki,ke har kinada bakin cewa baki sonsa ai taimaka miki zaiyi ya aureki domin idan ba shi ba bana tunanin akwai wanda zaiyi jihadi ya aureki, sapna fashewa tayi da kuka tace ummah dan Allah kar kiyi min haka wlh bana sonsa kibarni inza6i wanda nake…… marin da ummah tazabga matane yasa maganar talik’e a bakinta, cikin 6acin rai tace toh wlh bari kiji ni ba irin sakarkarun iyayen nan bane kuma ko kinso ko kink’i haydar shi zaki aura, shi yakamata yace baya son mai mugun hali irin naki ba wai ke kigujesaba, sapna girgiza kai tashiga yi tare da durk’usawa k’asa cikin kuka tace ummah dan Allah kitaimaka min na yarda kiza6a min kowa zan iya Zama da shi ammah banda haydar wlh baya sona, ummah daka mata tsawa tayi tace tashi kificce min daga d’aki wlh ko da zaki kashe kanki sai kin auri haydar inma ba kina butulu ba ai haydar shi yafi cancanta ki aura, sapna tace ummah kitaimaka min dan. ….
Nace kitashi kifitar min daga d’aki tun kan insa6a miki, dasauri sapna tatashi taficce daga d’akin takoma d’akinta tafad’a saman gado tacigaba da rusa kuka kamar wadda aka aikoma da sak’on mutuwa.

Saida taci kuka mai isarta sannan tayi shuru, a ranar kasa cin komai tayi daga kwanciya sai sallah kawai take tadata, ummah batabi ta kantaba tashareta,
A ranar sapna bata samu tarintsaba juyi kawai take saman gadonta maganganun haydar suna mata yawo a k’walwa.

Haydar yana komawa gida tun kan ya ida parking d’in motarsa saiga k’anwarsa hafsat ta fito dagudu, Saida yafito daga motar sannan taje tarungumesa shima haydar rungumeta yayi cike da k’aunar k’anwartasa, cikin jin dad’i hafsat tace yayana sannu da dawowa, murmushi haydar yayi yace yauwa my dear ashe kina nan?
Cikin shagwa6a tace tun d’azun fa nazo ina ta sa ido inga dawowarka,
Dariya haydar yayi yace sorry my dear yanzu ai gani na dawo,
Hafsat d’agowa tayi daga jikinsa tace yaya ko Auntynmu ce tarik’e min kai? Murmushi haydar yayi har saida hak’oransa suka bayyana yace muje cikin gida,

Hafsat cikin jin dad’i tace yayana Allah yasa abinda nake tunani yazama gaskiya wlh ina da burin ganin matarka,
Haydar yace zaki ganta very soon insha Allahu,
Hafsat k’ara tasaki tare da ruk’unk’ume yayan nata tana Dariya cikin murna tace yayana dagaske kake?

Haydar murmushi yayi yace shikenan idan baki yardaba yanzu dai bari inshiga part d’ina inyi wanka idan nafito munyi magana ai su daddy suna nan ko?
Cike da jin dad’i hafsat tace eh sunanan.
Shafa fuskarta yayi yace ina zuwa, sannan yashige d’akinsa,
Tsaye hafsat tayi tabi k’ofar da kallo tana murmushi cike da jin dad’in abinda yayannata yafad’a mata sai daga baya tawuce tanufi part d’in ummah saidai sukaga tana ta murna ammah bata fad’a musu abinda yayannata yafad’a mataba tace wak’a bakin mai ita ta fi dad’i.

Haydar ko da yashiga d’akinsa saman gadonsa yafad’a yayi pillow da hannuwansa tunani yake yadda zai tuntu6i iyayensa akan maganar aurensa yake, chan kuma sai yayi murmushi.
Tunowa yayi da ganin sapna da yayi tare da lubna nan fara’arsa tagushe daga fuskaesa tsaki yaja yace wannan yarinyar ba zata ta6a shiryuwaba ammah zanyi maganinta,

tashi yayi yashiga wanka, bayan ya gama shiri fitowa yayi yanufi main parlour a chan yatadda iyayen nasa zaune, ganinsa yasa hafsat tataso tarungumesa, su mami dariya sukayi mata, daddy yace kedai kina ji da yayannan naki dayawa, haydar murmushi yayi yace nima inaji da ita dayawa rik’o hannunta yayi suka isa inda su mami suke nan yagaishe da iyayensa suka amsa masa cike da fara’a, kallon hafsat yayi yace kawomin lunch d’ina nan inci, bayan hafsat ta kawo masa abincinsa, nan yafara ci, daddy murmushi yayi yace my son ya kamata dai kazo kayi aure kaima kaci abincin matarka, murmushi haydar yayi yace daddy kuma abun harda gori? Mami tace yoh ai inba gorin akayi makaba toh bakada shirin yin aure mu kuma aurenka shine kwanciyar hankalinmu ya kamata kamance da abinda yafaru a baya. Murmushi haydar yayi tare da ture plate d’in da yake gabansa sannan yafuskanci iyayen nasa yace daman maganar da nakeso inyi muku kenan na samu matar da zan aura kuma inaso ayi aurenmu very soon, cikin jin dad’i gaba d’ayansu sukace dagaske kake?

Haydar murmushi yayi yace dagaske nake aure zanyi, hafsat cikin jin dad’i tafad’a jikin yayannata tace yayana naji dad’in wannan albishir d’in nima dai nafison ayi bikkinnan very soon, gaba d’ayansu sukasa mata dariya, daddy yace toh Alhmdllh gaskiya munji dad’i sosai, wacece zaka aura? Haydar sunkuyar da kansa yayi yatare da susa kai yace sunanta sapna kuma mahaifinta ya rasu saidai mahaifiyarta kuma ta ce ta bani ita duk lokacin da nashirya inturo magabatana, cike da jin dad’i iyayen suka sanya masa albarka tare da yi ma mahaifin sapna addu’a,

Hafsat saboda murna har da ‘yar kwallarta tace yayana yaushe zaka kaini inga Auntyntawa? Murmushi haydar yayi tare da jan hancinta yace kin cika zumud’i dear, dariya su mami sukayi sukace ina ruwan hafsat,
Haydar yace to daddy yanzu yaushe zakuje, daddy yace duk lokacin da kace my son, cikin jin dad’i haydar yace toh daddy jibi kuma dan Allah kar asa bikkin dawa, gaba d’ansu dariya sukayi masa mami tace wannan zumud’infa my son? Kabari abi komai a hankali kuma gidanka ai yana buk’atar gyara,

haydar marairaicewa yayi yace mami ai nan gidan nakeso mufara zama inyaso daga baya na gama gyaran gidana sai mukoma, mami tace a’a haydar hakan ba zai yuwuba, daddy yace a’a kibarshi kawai yadda yakeso hakan zamuyi tunda yanzu yakeson ayi auren ai mu abun farinciki ne agaremu fatanmu dai Allah yasa ayi damu, mami tace hakane, gaba d’ayansu suka amsa da Ameen, nan daddy yashiga tsokanar haydar saidai hafsat take tare masa shidai murmushi kawai yake yana danne abinda yake cikin zuciyarsa.

Wanshe kare bayan sallar azuhur haydar shiryawa yayi yaje gidansu sapna, bayan sun gaisa da ummah, sun kuyar da kai yayi yace ummah gobe su daddy zasuzo neman aurena a fad’ama kawu domin yasani, cikin jin dad’i ummah tace masha Allah,,Allah yakaimu goben Allah yabiyaka haydar, murmushi haydar yayi yace ummah dama… shuru yayi yakasa k’arasa maganar, murmushi itama ummah tayi tace daman me? Kayi magana mana haydar kadaina jin nauyina,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button