BABU SO HAUSA NOVEL

DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA HAUSA NOVEL

haydar cikin salonsa na soyayya tuni ya mantar da sapna komai,

a daren kamar zasu cinye junansu domin sun nuna ma junansu k’auna zalla duk wani sirri da yake cikin zuciyoyinsu saida suka bayyana ma junansu, k”arshen wahala sapna ta Sha wajen haydar daurewa kawai tayi tanuna masa jarumtarta.

bayan komai ya lafa haydar rungumeta yayi yana ta shimata albarka, sapna sai alokacin takejin kunyar abinda ta aikata tura kanta kawai take acikin k’irjinsa tana shak’ar k’amshin jikinsa,

haydar murmushi kawai yake yana shafa bayanta chan sai yayi gyaran murya yace baby intambayeki?
Sapna muryarta chan k’asa tace eh
haydar k’ara gyara mata kwanciyarta yayi a jikinsa tare da k’ara jawo musu blanket yak’ara rufesu sannan yace ya akayi duk yadda kika kasance da su lubna a baya ammah kika kasa basu kanki?

murmushi sapna tayi tace yaya haydar nasha wahala sosai wajensu Aunty lubna nima kaina nasan Allah ne kawai yataimaka min har naku6uta daga hannunsu domin duk wata hanya da zasubi suga sun sameni sunbi ammah sun kasa hawayene suka shiga zarya daga idanunta tace yaya haydar nikaina nasan su Aunty lubna ne suke zuba min magani da yake sawa inajin feelings duk dan susamu biyan buk’atarsu ammah da taimakon Allah nake samu ina ku6uta daga hannunsu, saidai kuma deejah itace silar faruwar komai, tabbas ayanzu naga illar yin k’awayen da ba nakirki ba.

haydar k’ara rungumeta yayi sosai yace sapna kigode ma Allah dayaku6utar da ke daga sharrinsu, nai miki alk’awali zan zauna dake har k”arshen rayuwata wlh duk wani wulak’anci da kikaga ina miki duk kishinkine saboda soyayyarki da nadad’e tana d’awainiya da ni, sapna d’ago kai tayi takallesa har alokacin hawaye takeyi tace yaya haydar dagaske kana sona?

haydar gyad’a mata kai yayi yace tun lokacin da nafara ganinki kika shiga zuciyata tabbas sonki yawahalar da ni tsawon shekara da watanni, zaro ido sapna tayi tace yaya haydar daman ka sanni?

lakuce hancinta yayi yace nasanki mana kallo d’aya nayi miki nakamu da sonki, a lokacin nakusan aure ammah nasa ma raina ko bayan aurena kema sai kin shiga gidana a matsayin matata tabiyu, kallon sapba yayi da tatsaresa da ido, yace bakiyi mamakiba da kikaji nace nata6a aure?

sapna maida kanta tayi takwantar a k’irjinsa tana murmushi tace yaya haydar ai nasan kata6a aure daman, itama matarka irinace ka aura.

murmushi haydar shima yayi yace kidaina had’a kanki da khadija domin ita rayuwa irin tasu lubna tayi keko bahaka kikeba k’addara ce kawai da rashin bin maganar mahaifiyarki da kikayi alokacin da tanuna miki illar abota da mutanen banza domin akullum babu alkhairi acikin zuciyarsu burinsu kowa yayi irin rayuwar da sukeyi kinga kenan biye ma zuciyarkine da kikayi daman duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka kinga yanzu hakan yazama ishara agareki sai kisan kalar abokan da zaki dinga zama dasu domin duk wayonki bazai tseratar da ke ba, sai kinhad’a da addu’a.

supna gyad’a kai tashiga yi alamar gamsuwa da maganar haydar tace tabbas yaya haydar maganarka haka take nima nasan LAIFI NANE ammah insha Allahu ba zan k’ara tafka kuskure hakaba,

saidai yaya haydar ina tsoron wata rana idan bakanan sudawo min wlh nasan bazasu ta6a hak’ura da abinda kayi musuba domin lubna bata yafiya, ‘DAUKAR FANSA wajibine agareta

haydar shafa fuskarta yayi yace baby kidaina jin tsoronsu domin duk abinda zasuyi Allah yafisu kuma insha Allahu very soon zan maidake wancan gidan nawa kinga shikenan kinyi nisa da su,

sapna cike da jin dad’i tace nagode sosai yaya haydar Allah yabarmin kai, chan kuma sai tamarairaice fuska tace toh batun aurenka da zakayi fa?

haydar dariya yayi tare da kallon agogo yace baby taso muje muyi wanka muzo muyi bacci kinga har tym yad’anja yanzu har 1am ta yi,

sapna turo baki tayi tare da mirginawa gefensa takwanta tace kaje kayi ni idan kafito zanyi, haydar dariya yayi yace baki isaba yarinya dole ki aje kunyarnan taki, mik’ewa haydar yayi yaye mata bargon da tayi rufa da shi, d’aukarta yayi kamar jaririya yanufi toilet da ita tana ta wulla-walla da k’afa, haydar yana ta mata dariya.

haydar dakansa yayi mata wanka sannan shima yayi wanka yanad’ota da towel suka fito,
shi yashiryata dakansa sannan yarungumeta suka kwanta bacci cike da k’aunar juna…….

Comments
nd
Share

Sis Nerja’art✍????_
????????????????

_*DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA..*_

              ????????????????

(BASE ON TRUE LIFE STORY)

Written By ~ Sis Nerja’art

DEDICATED TO ~ MY SIS AUFANA ND SAINAH UMMUN MEENAL

INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ®
[onward together]
{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }
THE PEN OF LOVE. ???? HEART TORCHING ❤ TEAR OF SORROWS ???? CURDLES ???? GIGGLES ???? AND MARRIEGE THINK????
JUST GIVE US FOLLOW….

Wannan page d’in nakune intelligent writer’s ku nadaban ne acikin zuciyata basirarku tana burgeni Allah yabarmu a tare I heart you all????????

Page 4⃣0⃣

lubna koda suka samu suka fito dagudu motarsu suka shiga cikin sauri tatayar da motar tabar anguwarsu sapna, saida taga tabar anguwar sannan tayi parking d’in motar tare da kife kanta a steering tana maida numfashi

amfah kallonta tayi bakinta duk jini tace lubna yau mun d’ebo ruwan dafa kanmu, kiduba kiga cin mutun da guy d’innan yayi mana har fa fashemin baki yayi,

lubna d’ago kanta tayi fuskarta duk a kumbure tace ai wlh ba zan ta6a kyalesaba dolene ind’au k’ak’waran mataki akansa sai yasan ya ta6ani,

amfah zaro ido tayi tace a’a k’ara dai muhak’ura domin wannan daga ganinsa babu abinda zamu iya tsinta agaresa bakamar sauran da muke ci ma mutunci yakeba.

harara lubna tawurga mata tace matsoraciyar banza to wlh idan ke tsoro kikeji to ni bana tsoronsa kuma sai yayi nadamar abinda ya aikata min domin ni bana yafiya ‘DAUKAR FANSA dolene inyisa, dan yanzu haka daga nan gidan malamina zamu wuce.

amfah dai shuru tayi tana goge jinin da yake fita daga bakinta.

lubna giya tafiddo daga cikin jakkarta sannan tad’auko wata k’waya tazuba a ciki tagirgiza, amfah tana ganin haka tazaro ido atsorace tace badai sha zakiyi yanzu ba tunda driving zakiyi?

lubna shuru tayi tare da bud’e kwalbar tafara kwankwad’a saida tasha fiye da rabi sannan tajanye Kwalbar kallon amfah tayi da tatsareta da ido cikin muryar maye tace kekuma sai kallona kikeyi inzakisha gashi,

amfah cike da tsoro tace anya lubna zaki iya driving ahaka?

dariya lubna tayi tace eh idan kuma kinji bakya iya bina toh kisafka kihau mashin, amfah kallon titin tayi taga babu abin hawan da yake giftawa ganin kafin tasamu abun hawa sai takai kusan rabin awa, dan haka takar6i kwalbar giyan tace a’a muje kawai,

lubna dariya tayi tace matsoraciya kawai sannan tatayar da motar tahau titi, gudu takeyi sosai tuni giya tafara aiki nan tafara gani bibiyu ammah takasa hak’ura da driving d’in, tana lumshe ido tana bud’ewa wani irin tuk’i take tana komawa hannun da ba nataba saidai mutum yakauce yabata hanya ita kanta batasan yanayin da takeba gani take komai daidai take yinsa hatta ita kanta amfah tafita hayyacinta.

wata DAF ce data tafo dagudu duk yadda taso tagoce ma motar lubna ammah ta kasa nan tashiga yi mata horn, ita kuma lubna gani take kamar idanuwanta daidai suke nuna mata Daf d’in ba saitinsu takeba dan haka tacigaba driving d’inta, sai da tazo gab da motar sannan talura nan suka rikice duk yadda taso takauce ammah takasa arikice suka fara k’walah ihu,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button