GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka Gimbiya Hakima ta tashi zata fita, yanda ta shigo cikin isa da takama, haka tazo fita ba ta yarda ta nuna taji haushi ba, tazo dai dai fita tace yace”lock at you, useless girl stupid kawai…

Wanna abun shi ya kara ba Gimbiya Hakima haushi na ta fito ta tsaya wani waje tana jiran fitowarshi dan sai ya gaya mata shi DAN GIDAN UBAN WAYE a cikin garin Zaria da zai ce mata useless, bayan duk korarta da yayi bai isheshi ba, ita shiyasa bata san harka cikin talakawa, dan talaka bai iya cin arziki ba dan ya samu yana lecturer shine yake san gaya mata maganar, “ina kamar ni GIMBIYA HAKIMA wani banzan talaka bai isa ya gaya man magana..

Haka Gimbiya Hakima ta kama magana tana jiran fitowar YARIMA HAKIM ta sauke mashi kwadon rashin mutunci????..

Muje zuwa my fan, Team Hakima kun dai ba Hakima shawara karta janyo maku August nidai babu ruwa na lol☺️????.. .

By Jameelah Jameey✍????

Share and comments pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

15&16

Shi kuma Yarima Hakim, tunda ya kora Gimbiya Hakima waje, sai kowa ya kara shiga taitayinshi a class din, dan sun lura da alama baya daukar nonsense, dan haka sai ko wace mace mai shirin shigarmai rayuwa sai gwiwoyin su suka yi sanyi, Amman duk da haka wasu daga cikin su suna kan bakarsu..

Yana mamakin rashin tarbiya da kunya da Wannan yarinyar da ya kora, dan ga dunkan alamu yarinyar bata da kunya dan ya ga zahiri a cikin idanunta, aiko bamu shiryawa da ita, dan ko wacece ita ba zan dauke nonsense ba..

Haka Yarima Hakim yaita mamaki, sannnan ya cigaba da yi ma yan class darasi, bayan ya gama ya hada takardunshi ya fito yayi hanyar office din shi..

Tunda ya fito Gimbiya Hakima ke bin bayanshi, bai lura da ita ba dan shi har ya manta da ya kori wata yau a class din shi..

Yana bude office din shi ya shiga ya zauna, yana zama ko suit din shi bai cire ba, saboda anfara yin zafi shiyasa yake san ya rage suits din jikinshi..

Sai kawai ya ji an bankado door din office din shi, dagowar da zaiyi sai ya ga yarinyar da ya kora a class tana nuna shi da yatsa tana cewa..

“Kai dan gidan uban waye cikin garin zaria da zaka koreni a class har kana ceman useless?

Yarima Hakim tsayawa yayi kwallon Gimbiya Hakima yana mamakin furincinta, wai shi Hakim take mana question na shi dan gidan uban waye, cikin zafin nama Hakim yace.

“Indan baki barman office ba sai kinyi danasin shigowarki office din na, ke bama danasin shigowarki office dina ba, sai kinyi danasanin haihuwarki duniya, wawiya marar tarbiya..

“Kai harka isa kace man zanyi da na sani, ni Hakima ba wanda ya isa yace man zanyi da na sanin haihuwata duniya, balle Kai,ji baika dan Allah kamar wani almajiri, sannnan kaine baka da tarbiya ba dai ni ba..

Kafin Hakim ya tashi yayi ma Gimbiya Hakima wani abu, har tayi ficewarta, dan daman a tsorace take dashi tana kallon idonshi da ta shigo office din shi taji tsoranshi ya kamata, kawai dakewa tayi ta mayarmai da ansa, dan bata iya daukar bakin ciki ita daya kwara suyi two two, daga office din Hakim wata lecture din ta wuce, Allah ya sota lecturer din bai Kai da shigowa ba, ta samu waje ta zauna taci kunu.

(Gaskiya Gimbiya Hakima baki da sauki, ya kamata ki gyara fa, dan Yarima Hakim ba kyaleki zanyi ba! Nidai gaskiya na gaya maki nida yan Team Hakim????????)..

“Hmm! Mai zanyi ma yarinyar nan naji dadi”

Yarima Hakim ya ke fadin haka yana ta zagaye cikin office din shi, dan tunda yake bai taba ganin wanda taci mashi mutunci ba kamar Hakima..

“Ni wanann yarinyar zata cema dan gidan uban waye cikin garin zaria, to ita waye ubanta? Ko waye ubanta cikin garin zaria sai na gyara mata zama, ta koyi yanda ake iya magana da mutunta na gaba da ita, dan na fahimci uwarta da manta da wannan aikin, tunda ta manta ni zan koya mata..

Haka Yarima Hakim ya gama tunanin wulakancin da zaiyi ma Gimbiya Hakima, sanann ya hada komai shin ya tafiyarshi gida..

Itako Gimbiya Hakima ranta tas, dan ta rama abunda Hakim yayi mata, shiyasa ta maida hankalinta wajen lecture din da akeyi..

Alhmdulh Gimbiya Hakima taba yan class din su mamaki, dan duk question din da malamin nan yayi Gimbiya tana daga farko wajen tashi ta bada amsa, Amman cikin isa da takama da kuma nuna mulki take bada amsa..

Ba yan class kawai ba harta malamin yana mamakin halin Gimbiya Hakima, dan ya lura yarinyar zatayi ji da kai sosai, sai dai inda ta burgeshi tana da ilimi dan ya ga alama ta san abunda takeyi..

Bayan ya fita wata tazo ta zauna kusa da Gimbiya Hakima, tace mata, “sannu fa, Gimbiya Hakima kallonta kawai tayi bata sake kallonta ba, sai da tayi kusan minti biyar sannan tace “Yauwa..

“Sunana Maryam Bello, Babana ne V. C din makarantar nan, sai da Gimbiya Hakima ta gama danna waya sannan ta juyo tace mata, “you are welcome, “thank You, kefa ya sunanki?

“Hakima Abdulhadi Abdulsamad,”wow nice name, kema yar nan zaria ce, “Aa kano, wani abu? “Aa bakomai kawai dai naga kinyi man shiyasa, ina san mu zama friend inba matsala…

Sai da Gimbiya Hakima ta gama yi ma Maryam kallon raini sannan tace, “ur wclme, “thank You Hakima..

Nan suka zauna ba wata magana sai ita Maryam take jan Hakima da labari, amsa daya ce take samu wajen Hakima daga Uhmm sai Aa.

Haka dai har sukayi exchange digits sannan suka yi Sallama, Maryam ta shiga motar ta, tana kallon yanda Bala drive yake budema Gimbiya Hakima mota, kamar zan duga mata da yanda take yi sai da tayi mamaki,amman ita dai Gimbiya Hakima tayi mata duk da taga ba halinsu daya ba, Amman zatayi hakurin zama da ita, har Allah yasa taga ta chanza mata hali, dan wannan ba hali bane mai kyau na wulakanta mutane..

Bayan Gimbiya Hakima sun koma gida wanka tayi sannan ta fito parlour ta zauna, su Lantana suka fara yi mata tausa(messaging), bayan sun gama ta ci abinci sannan suka fara bata labari…


“Sannu da hutawa, Ranki yadad’e, “yauwa Hakim, har andawo? “Eh Allah ya yarda, wallahi duk na gaji Fulani sosai…

“Ai dole ka gaji, tunda ka daukarma kanka aiki, “Fulani nidai kisa albarka, “ai Hakim kullun ita muke sawa..

“Yaya sannu da zuwa, “yauwa Maryama ina Sadiya take maiyasa bakuje school ba?

“Bamu da lectures yau sai gobe, “ok, Fulani ni zan wuce na gaida Maimartaba, “to adawo lafiya, ka dai ci abinci ko? “Eh naci, “karka kuskura kaci abincin gidan nan ina kara maimaita maka Hakim..

“To ina kokarin kiyaye wa Fulani, na barki lafiya..

Nan Yarima Hakim ya wuce Fada dan ya gaida Maimartaba yana cikin tafiya yaji an ingijeshi, waiga war da zaiyi sai yaga Yarima Hamad yana yi mashi wani kallo…

“Hamad ina wuni? “Ban ganshi ba, da ban wuni ba da ka ganni? “Uhmm, abunda Hakim yace ma Hamad kenan ya wuce ya barshi tsaye..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button