GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Zaman lafiyarku da Gimbiya Hakima shine ku ringa yin aiki kan lokaci, dan ita Gimbiya Hakima batasan taga mutun bai san abunda yake ba”..

“Hakane kuma Inna Lantana insha Allah zamu kiyaye duk abunda Gimbiya Hakima bata so, insha Allah zamu kiyaye”..

“Allah yasa, ni na wuce wajen Gimbiya tana jirana, “a fito lafiya”..

“Hutawarki lafiya ƴar’sarki matar sarki”.

“Lantana na fahimci bakisan ki dunga ganina cikin gidan nan ko? “..

“Allah ya huci zuciyarki, ai idan baki gidan nan muma ai barinshi zamuyi, dan kice gidan baki ɗaya zaman ki muke Allah ya taimakeki”..

“To maiyasa kike ceman matar sarki? “..

“Allah ya taimakeki, ai aure dole ne Gimbiya Hakima uwar marayu, muna fatan muga jininki a hannunmu”…

“Hmmmm! Naji yanzun dauko wannan tsarabar da mukayi ma bayin shashena ku raba kuba kowa kosan shi, sannnan ace ma su Ab’u yau su haɗa Liyafa mai kyau anjima zani ci abincin dare da kowace ma’aikaciyar shashen ni Hakima a babban parlour na”..

“Angama Gimbiya Hakima, Allah ya ƙara lafiya ya rabaki da murmushin mahassada”..

“Yanzun kinji matsalarki, kedai baki gajiya da fadanci tashi ku fara aikin da na saku, ke kuma Azima shiga toilet ki haɗa man ruwan wanka”…

“To Uwargijiyarmu, Allah ya ƙara girma”..

Nan Azima ta shiga toilet ta fara haɗama Gimbiya Hakima ruwan wanka, su kuma su Bilkisu suka fara rabon tsarabar da Gimbiya Hakima tayi masu..

“Allah ya taimakeki, nagama haɗa ruwan yana jiranki a bayi”..

“Ok! Nasan kinfisu sanin kaya masu kyau, dan su sun tsufa basu san zamani ba dan haka ki fiddo man kaya wanda ina gani zan yaba, inkin fiddo ku wucewarku kuma ku fara shiryawa kafin lokacin Liyafa”..

“Ranki yadaɗ’e angma, a fito lafiya uwar marayu, “, Allah yasa”..

Nan Azima ta fiddo ma Hakima kaya sannan suka kwashe tsarabar su suka wucewarsu..

“Sannunku mutanan madafa, “yauwa Aa ya mukaga iyayyen kaya a hannunku haka? “..

“Ga naku tsarabar Gimbiya Hakima ce tace a kawo maku, sannan kuyi abinci mai rai da lafiya tare da ita yau za’ayi Liyafa a babban parlour dinta anjima da dare dan haka sai kuyi sauri ku gama kuje ku shirya muma shiryawa zamuyi”…

“Alhmdulh! Alhmdulh!! Alhmdulh!!! “..

“Allah mun godema ka da ka anshi addu’armu da ka shiryar da wanann baiwa take Gimbiya Hakima “..

“Jama’a wai da gaske ne yau ɗin nan Gimbiya Hakima zatayi Liyafa damu? Bayan mu bayi ne wanda ta tsana take ƙama mune abun wulakantawarta a kullun”…

“Ai Allah kenan, kinga Gimbiya Hakima zatayi abunda ba’a taɓe yi ba a masarautar kano, dan shekarata asherin (twenty) ba wani ɗan Sarautar da ya taɓe cin abinci cikin bayin shi sai Gimbiya Hakima da zata fara a yau ɗin nan”..

“Gaskiya hakane Inna Lantana Allah yasa ta ɗaure a haka, “Amin mu mun wuce mukai ma sauran tsarabar su, kuma kuyi sauri ku gama dan Allah kafin lokaci yayi”..

“Insha Allah Ba’ba Bilkisu, daman mun kusa gamawa da yardar Allah”…

Nan su Bilkisu suka cigaba da rabama bayi tsaraba suna gaya masu su shirya zuwa anjima zasuyi Liyafa da Gimbiya Hakima cikin babban parlourn ta..

Nan take maganar ta gauraye masarautar baki ɗayanta kowa yana mamakin wai Gimbiya Hakima itace da ba bayinta tsaraba harda Liyafa zasuyi anjima..

“Ranki yadaɗ’e Gimbiya Fulani, yau nazo maki da labari mai daɗin saurare”..

“Ina saurarenki Zainabu Allah yasa naji daɗin da kike faɗi “..

“Zama kiji Uwargijiyata! Daman yau Gimbiya Hakima ta raba ma bayin ta tsarabar dawowa, sannan tace anjima su shirya zasuyi Liyafa tare a bangarenta da daren nan na yau”..

“Alhmdulh! Gaskiya ko Zainabu kin kowaman da labari mafi dadi cikin labarin da kike kawoman, dan haka kije na baki kyautar gold da murjani”…

“Godiya nike, uwar masu adalci Allah yasa Gimbiya Hakima ƴar’sarki ta ƙara koyi da ƙyaukwan hali irin naki”.

“Uhmmm! Abunda Gimbiya Fulani tace ma Zainabu sannan ta bata kyautar da tayi mata..

Rasa inda zata sa kanta tayi dan murna, dan ba ƙaramin dadi taji ba Hakima ta fara janyo bayinta a jiki ba, bata san sanda ta tashi ta dauki hanyar shashen Maimartaba dan tasan Gimbiya Yakumbo tana can shiyasa batasan abunda daughter dinta tayi ba…

“Ranki yadaɗ’e Gimbiya Yakumbo! Gimbiya Fulani tana neman ki bata iso tana san kuyi magana”..

“Maza kije kice mata ya shigo, “angama Allah ya ja da tsawancin kwana, Allah ya taimakeki Gimbiya Fulani! Gimbiya Yakumbo tace ki shigo, a fito lafiya”…

“Assalama Alaikum”..

“Amin wa’alaikumus Sallam”

“Fulani naji kince kina san magana dani?, “eh Yaya! Ina Maimartaba yake? “..

“Yana ciki yanzun zai fito, ga dunkan alamu yau kina cikin farin ciki Fulani, dan ga shi nan fuskarki ta nuna”…

“Sosai ma Yaya, sannu da fitowa Maimartaba, “yauwa Amaryata Fulanita, fatan lafiya dai ko? Ko kuma Yayartaki kika biyo? “..

“Aiko dai, kasan ban iya kwana banga Yaya ba, daman zuwa nayi nagaya maku yau Hakima tayi abunda ba’a taɓe yinshi ba amasarautarnan “..

“A’aa mai tayi kuma Hakimar?, “yau taba bayinta tsaraba sannan tace anjima su shiryasa tare zasuci abincin dare”..

“Alhmdulh! Kunga abunda nike nuna maku ko? Da kun kun nace a dole sai na fidda Hakima kasar waje karatu, ba kamar ke Yakumbota “..

“Hakane gaskiya mijinmu! Munga amfanin karatu cikin talkawa ko, dan tuni na fahimci Hakima ta chanza hali tun dawowarta ta farko”..

“Ai daman nace maku zaman da zatayi cikin talkawa tana ganin yanda suke rayuwa dole itama watarana ta chanza, balle nasan duk mulkin Hakima sai tayi ƙawa, shiyasa ban ajiyeta a nan BUK ba na kaita kasar zaria”..

“Gaskiya ko! Godiya muke sarki mai adalci, “Allah ya ƙara shige mana gaba, “Amin ya Allah ni na barku lafiya”..

“Fulanita gobe ki turoman Hakima dole nayi mata kyauta da wannnan halin da nuna mai kyau cikin masarautar nan”..

“Insha Allah, mu kwana lafiya, “Allah yasa”..

Nan Fulani ta koma shashenta tana jin daɗin yanda suke zaman lafiya itada Yakumbo kamar ba gidan sarauta ba..

“Zainabu kije kice ma Hakima gobe inasan ganinta, “angama ranki yadaɗ’e yanzun ancika umirninki..

Nan Zainabu ta tafi shashen Gimbiya Hakima ta gaya mata sakon Fulani sanann ta koma, ta gayama Fulani tace to..

Masha Allah laƙuwata ilabillah! Tafiya take cikin isa da mulki ga kuma uwa uba aji da kyau dasu ƙara sata jin tafi kowa a kano state baki ɗaya gata kuma ƴar’sarki kuma matar sarki..

Amman bani Jameey nace matar sarki ba, Inna Lantana ce babu ruwana ba'ajin mutuwar sarki bakina????

Wani Arnan black material ne jikinta, dinki doguwar riga akayi mata, dinki yabi jikinta yayi bala’in ya mata kyau, ga wata alkyaiba da ɗaura a bisa rigar sai ta ƙare fitowa GIMBIYA HAKIMA dan ko tafiya dakyal take yinta kamar tana tausayin taka kasa kawai mulki ne yake sa Gimbiya Hakima wanann tafiyar..

“Sannunki da fitowa Uwargijiyarmu “..

Bata kyalesu ba balle su sa ran ansawa, sai da ta zauna ta huta sannan ta kyalesu ɗaya bayan ɗaya sai tace, “yauwa sannunku kuma”…

“Fatan duk kuna lafiya ba mai bukatar wani abu kuma? “..

“Eh Alhmdulh Gimbiya bamu bukatar komai sai farincikinki uwar marayu”..

Kallon su Bilkisu kawai tayi suka tashi suka fara saving ɗinta, sanann sukayi na sauran baki ɗaya bayan sungama suma sukayi nasu suka zauna…

Gimbiya Hakima ta tashi tayi masu addu’ar cin abinci sannan kowa yayi bissimilla suka fara cin abinci..

Wajen shiru baka jin motsin komai sai na cokali, duk da Gimbiya Hakima ba cin abincin take sosai ba dan bata jin yunwa, amman taci yanda ya kamata suma bayin sunci dan harda masu ƙarawa sai da kowa ya koshi sannan suka kama gabansu, bayan sun gyara wajen..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button