GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Dole ni Hakim na koya ma kaina san wanan baiwar Allah da Abba ya hada ni da ita, sannan dole na cire tunanin wanna stupid girl din cikin zuciyata dan ba anfani na kama tunaninki Hakima, I hate you too Hakima ki fita daga rayuwata.”

Abunda yace kenan ya cigaba da driving dinshi da yaga abun ba mai ƙarewa bane sai ya kunna ƙira’ar Ahmed Sulaiman yana sauraron, sanan ya fara dawowa dai-dai.


×KANO×

Bayi aiki suke tukuru dan tun Hakima tana lisafa kalar abunda ake haɗama bakon nata har ta daina dan gani take abun ya wuce misali sai kace wanda za’ayi ma biki.

Ruwan wanka mai rai da lafiya Lantana ta haɗa mata dan har sun fara yi ma uwargijiyar tasu shiri na musaman saboda kowa yasan bikin saura wata ɗaya shiyasa suka tashi tsaye wajen ganin su shirya ta yanda dace.

Bayan ta gama haɗa mata ruwan wankan sannan Hakima ta shiga, ita kuma Azima ta fiddo mata kaya nagani na faɗa, dan already Azima taje ta ɗauko mai make-up Hakima kawai suke jira ta fito wanka su fara aikinsu.

Sai da Gimbiya Hakima tayi kusan minti talatin a toilet sanann ta fito ta zauna aka fara tsara mata kwaliya mai rai da lafiya, bayan angama tasa kaya aka ɗaura mata dan-kwali ɗaurin Zara Buhari akayi mata amman ya fidda shapes sosai.

Bayan Hakim ya iso Yarima Annas yayi mashi jagora shashen Maimartaba ya fara gaidashi sannan ya wuce shashen Gimbiya Yakumbo itama ya gaidata sanann shashen Fulani itama ya gaidata, tun anan Yarima Hakim yasan yazo gidan sarauta kuma gidan sarauta masu mutunta mutane suka jarajar dan adam nan take yaji dadi dan da alamu masarautar kano ba’a tungun da akeyi a masarautar su, bayan sun fito daga shashen Gimbiya Fulani bayi suka kama gaidashi suna yi mashi barka da zuwa masarauta mai albarka, kuma yaga alama, shashen Yarima Annas suka koma sannan Yarima Annas ya kira Gimbiya Hakima yace tazo shashen shi bakonta yana jiranta.

Abinci aka fara jerama Hakim gabanshi kala-kala dan har Hakim sai da yayi mamakin karanci irin na wanan masarauta gaskiya suna da karanci da sanin mutuncin mutane, dan yaga yanda bayinsu suke walwala kamar ba bayi ba bayan sun gama ajiye mashi abinci suka fita.

Yarima Annas ya matsama abokin nashi yaci abinci sosai dan sai da yaga yaci sosai sanann ya kyaleshi nan suka ƙara gaisawa ya tafiyarshi ya bar Hakim yana zaman jiran isowar Gimbiya Hakima.

Wooow! Masha Allah tafiya take cikin natsuwa da ɗaukar hankalin duk wani ɗ’a Namiji mai lafiya, lace ne purple a jikinta ɗinkin riga da siket ba karamin kyau kayan sukayi mata ba alkalbarta black ce sanan takalminta ma black ne agogonta yar company Gucci itama black ce, ba wata kwaliyar hauka akayi mata ba dab sai ka rantse kace ba a shafama Hakima poder a fuska ba dan pure skin Hakima ke gareta, take mata baya bayinta ke take mata baya sun ɗagemata alkalbarta dan karta share kasa, sai ka rantse kace yau ake ɗaura ma Hakima aure zabar kyaun da tayi.

Har cikin parlourn Yarima Annas bayinta suka rakota sune ɗage da alkalbarta daga ita har Hakim ɗin basu gane juna ba dan shi Hakim ba ita yake kyalo ba yana mamakin kalar mulki na amaryar tashi ne dan tafiyar ta kawai zai shedda maka da tanada mulki, bayan su Lantana sun gama gaisheshi hannu kawai ta ɗaga masu sannan suka tashi suka fita baki ɗayansu.

Ɗagowar da Hakima zatayi suka haɗa ido da Hakim, su duka suka miƙe lokaci guda suna nuna junansu da hannu nan Hakima ta fara magana tana nuna nashi da yatsa tana cewa…

“Waya ka woka gidanmu, ubanme kazo yi mana.. “Hakima enough ya isa haka.”… Yana dakatar da ita ranshi ɓace.

Hakim ya faɗa kamar zai ɗauke Hakima da mari, ita kanta Hakima sai da ta tsorata dan tunda take da Hakim bata taɓa ganin ɓacin ranshi ba irin wanann.

“Lock at you, ni nafi karfin nazo nace inasanki dan kawai biyaiya zanyi ga mahaifina da ba abunda zanyi dake sann… “Hakim karya kake wallahi baka isa kace man haka ba, kayi yanda kayi ka iko mahaifinka wajen Baffah dan a ɗaura maka aurena ko? To tsaya kaji kayi maza-maza kace ma Babanka ka fasa aure na dan wallahi Hakim da ka aureni gwara karkayi aure a rayuwarka har ka mutu dan ni GIMBIYA HAKIMA na tsaneka bani kaunar dan haka bala’i da masifa zaka auro ma kanka gwara tun wuri kaje kace ka fasa Auren nan tun kafin dare yayi maka.”

“Ke ɗin banza, ke har kin isa kice naje nace ma Abba na fasa aurenki to bari kije na gaya maki ni YARIMA HAKIM yanzun nayi niyar aurenki Hakima, zan aureki ba dan inasanki ba, zan aureki dan na koya maki hankali da tarbiya dan yanzun muka fara wasan nida ke Hakima useless girl.”

“Aiko zaka ɗauro ma kanka wutar dafa kanka Hakim, “as we wish kina iya gaya ma mahaifinki bazaki aureni ba tunda daman ke ba kunya gareki ba, amman ni Hakim ba zan iya yin jayaiya da mahinfina ba dan nasan darajar iyaye, amm..” Dallah shut up ur darting mouse, har kai kake cema wani baiyin bayaiya ga iyayenshi, kamar yanda kayi biyaiya nima ita zanyi amman kasani bakai ba zaman lafiya a gidanka dan ni dai Hakima ba kaunar ka nike ba idiot wanda baisan mutuncin matune ba, ka godema Hakim haduwarmu tayi kyau amman haduwarmu ta gaba sorry to said.”

Nan Hakima ta tafi tabar Hakim tsaye da mamaki baiyi mamakin rashin kunyar da tayi mashi ba dan ya san da man ba Kunya ke gareta ba, mamakinshi ɗayane daman ashe yar’sarkice? Shine yake mamaki ba rashin kunyar ba, bayan ya fito sukayi Sallama da Yarima Annas sannan ya wuto gida dan sakon Gimbiya Fulani daman already yaba Gimbiya Yakumbo ta ba Hakima.

By Jameelah Jameey✍????

JameelarhSadiq@wattpad

Share

Comments

Vote

Like

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

69&70

Hakima direct shashenta ta wuce ta ɗauki waya ta kira Maryam, “Hello Maryam kina jina.”?

“Eh ina jinki Hakima, lafiya maike mafaruwa naji kamar baki cikin hankalinki.”?

“Na shiga ukuna Maryam, bansan ya zanyi ba Baffah zaiyi man aure cikin watan nan.”

“Aure kuma Hakima.”?

“Eh aure kinsan ma da wa zai haɗani Maryam.”?

“Aa ina saurarenki dai Hakima, da wa Baffah zai haɗa ki.”?

“Wai prof Hakim, “Alhmdulh Allah na gode maka wallahi bakiji yanda hankali na ya tashi ba amman yanzun Alhmdulh komai namu wanan shine tuwo.. ” shut up, haba Maryam ya ina gaya maki problem ɗin na amman kina wata maganar daban.”?

“Cool down mana ƙawata, wallahi kasa boye farincikina nayi domin maganar gaskiya Hakima Allah ne ya cika mana burinmu nida su Maryama to taya zaƙi yin farinciki.”?

“Ok thank you ni zan kashe waya ta da man na kiraki ne ki kagayaman yanda zanyi amman kin ƙara ɓataman rai kin kyaunta Maryam.”

“Wait Hakima karki kashe wayar zan gaya maki iyakar gaskiya a matsayina na aminiyarki Hakima, “Uhmmm! Am watting ina jinki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button