GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

87&88

Yau masarautar Zaria ta wayi gari da wani babban bako, dan tun safe Hakim take kitchen Maimartaba da kanshi ya aiko mata da sakon tayi ma bakonshi girki da kanta dan tunda yaci abincin ta yaji da dadi yace tayi ma abokinshi dan tare sukayi university tare shida Baffahn ta ,abinci mai rai da lafiya ta girka masu tasa aka kai shi fada bayan tagama ta shiga wanka ta shirya ta wuce shashen Gimbiya Fulani.

Bayan Sarki Abubakar ya gama cin abinci suka fara gaisawa da abokinshi sarki Abdulmalak, “abokina na samaiku lafiya.”?

“Lafiya lau Alhmdulh, ya ka baro kasar Katsina.”?

“Kasar katsina tana lafiya ita da mutunan cikin ta, “Alhmdulh haka akesan ji, Allah ya ƙara mana hakuri da talakawamu, “Amin ya Allah, ai abun dole sai da hakuri, dan shi daman zaman duniya ya gaji wannan abun guda biyu zo mu zauna zo mu saɓa, “Aiko dai hakane.”….. Sai da Sarki Abubakar ya numfasa ya kurbai ruwan inibi sannan ya fara magana,”abokina da farko dai ina tayaka murnar auren da kayi ma Hakim shida ɗiyata Hakima, tunda mu uku tare mukayi karatu nida kai da babanta, agaskiya naji dadi sosai, sai dai kash lokacin da akayi bikin bani lafiya sosai shiyasa na turo wakili.”

“Hakane ko, ai abokina nasan baka lafiya shiyasa baka hallaci ɗaurin auren ya’yanmu ba, kuma daga ni har Abdulhadi munyi maka uzuri babba, Allah dai ya baka lafiya, su kuma Allah ya basu zaman lafiya da zuri’a ɗaiyaba.”

“Amin ya Allah, sai magana ta biyu kuma, gani gaba abokina nazo da koƙan barata, wata alfarma nike so kayi man dan Allah ina fatan Allah yasa na samu.”?

“Haba abokina, ai ba abunda bakafi ƙarfi ba a wajena komai shi ko, ka gaya man ko wace alfarma ce insha Allah zaiyi maki mudun inadashi.”… Sarki Abubakar yaji dadi sosai duk da daman yasan yafi ƙarfin komai wajen Sarki Abdulmalak amman hakan kuma da ya nuna mashi ya ƙara mashi ƙarfin giwar gaya mashi bukatarshi.

“Masha Allah da man da wani abu bane illar na zauna nayi tunani inasan nima na haɗa zuri’a dakai, bi ma’ana inasan idan ba damu naba ɗana YARIMA HAKIM auren ɗiyata GIMBIYA HIKIMAT amman idan zai yuyu, duk nasan akwai su Hamad da Humad amman tarbiyar Hakim tafi kwantaman shiyasa nayi ma Hikimat shi’awar aurenshi.

MY FAN’S KUNJI WATA SABUWA DA SARKI ABUBAKAR YAZO DA ITA????

Numfasawa Sarki Abdulmalak yayi, dan baiyi tunanin abunda Sarki Abubakar yazo dashi kenan da baiyi mashi alkwarin zai yi mashi alfarma ba, wani nauyin Sarki Abubakar ya kama Sarki Abdulmalak, bai san lokacin da yace, “Alhmdulh, gaskiya naji dadi sosai da wannan haɗin da zakayi Abokina hakan ma yayi, fatan dai Allah ya basu zaman lafiya baki ɗayansu, kuma da kake maganar su Hamad lokacin auren ne nasu Allah baiyi ba, Allah ya ƙaddara sai Hakim ya rigasu fara aure kafin su suyi dan haka Abokina karka damu nan da wata ɗaya insha Allah zamu zo abamu auren Gimbiya Hikimatu insha Allah.”

“A gaskiya abokina bani da bakin da zani yi maka godiya sai dai nace Allah ya bar zuminci, insha Allah zamu shirya muma kafin nan da wata ɗaya.”

“To Allah ya kaimu, fatanmu mudai, Allah ya haɗa kansu ya basu zaman lafiya da zuri’a ɗaiyaba wanda zasu taimaki al’umma nan gaba.”

“Amin ya Allah.”…. Nan suka cigaba da tautanawarsu ta abokai da kuma yaushe rabon da su haɗu.


“wai Hakima lafiya najiki sukuku? Kamar baki lafiya kodai yayanmu ya bada ajiyane mu fara tara kayan ɗaki.”?…. Ta faɗa cikin wasa, “kedai kawai ki gani, amman wallahi yau gabana faduwa yake ji nike kamar wani abu ke damuna.”

“Ayya kita addu’a insha Allah ba komai,”Allah yasa matar Yaya.”

Dariya suka sa su duka ukun suka barke da labarin duniya, Hakima tana basu labarin makarantar, amman abun mamaki bata gaya masu kalar faɗan dasukayi da Hakim ba, suna cikin labarin Fulani ta shigo nan suka hadu su hudun suka cigaba da labarinsu dan Hakima kwantawa tayi bisa cinyar Fulani ta labarinsu, sai dariya suke dan Hakima ta ɗauki Fulani a matsayin uwa bata boye mata duk wata damuwarta haka suke rayuwarsu sun fahimci juna.

Tunda Hakim ya shigo yake tsaye yana kallonsu dan abun yana burgeshi sosai kuma yana jindadin yanda Hakima ta ɗauki mahaifiyarshi kamar mahaifiyarta, yakan godema Allah da ya bashi Hakima a matsayin matar aurenshi duk da ba wani zaman lafiya suke ba, amman tana daraja iyayenshi da yan uwanshi kuma hakan yana yi mashi dadi sosai da sosai, sai da ya gama kallonsu sannan ya shigo shima bisa cinyar Fulani ya ɗaura kanshi yana ture kan Hakima yana cewa, “wallahi ko Fulani yanzun kibar sona, tunda kika samu Hakima dan na fahimci baki damu yanzun ko na ci abinci ko ban ci ba.”

“Hakim badai rigima ba, yanzun inba neman magana ba kai da kake da mata tambayar mai zan maka na kaci abinci?da dani ke tambayar ka ma dan baka da mata shiyasa amman yanzun nasan Hakima bata barinka da yunwa.”

“Nidai duk da haka Fulani”, “kaji dashi dai, ku tashi ku tafi shashenku”,”Aa ba yanzun ba dare baiyi ba”,”ni tashi zanyi naje wajen Abbanku, kaga bakonshi ya tafi tun ɗazun amman banje ba”, “yauwa niko kamar naso na gane bakon Abba.”

“Sarki Abubakar ne fa, shine sarkin katsina, ai ke Hakima kin sanshi ko.”?

“Eh nasanshi, yaje walimar gama karatuna”, “yauwa kai Hakim mantashi kayi dai, kuma dan badakai akaje walimar ba da kaganshi da Hamad akaje nasan shi Hamad zai shidashi idan ya ganshi.”

“Hakane bari mu tashi mu tafi tunda wajen Abba zaki,mun barku lafiya, “to Allah ya kaimu.”

Haka suka jero suka taho bayi sai gaidasu suke suna yaba kyau da kyaun hali irin na Hakima da Hakim, suna shiga shashensu ko wane ya wuce room ɗinshi ya cigaba da hidimominshi.


“Gimbiya lafiya naga kina rawa ke ɗaya cikin ɗaki.”?

“Kilishi ai bansan kin shigo ba sai dai kawai naji maganarki.”

“To taya zakiji shigowata bayan kina da taka rawa kece ta samu amman ba a nemaimu ba, to gani gaya man lafiya.”

“Ai maganar gizo bata wuce ta koƙi inji hausawa, kawai ina farincikin saura wata hudu mutuwar Hakim, kuma har yanzun wannan yar’neman bata ɗauki ciki ba, shiyasa kikaga inata murna.”

“Hakane fa, amman baki san maimartaba yana neman kowa da kowa a shashenshi bayan sallahr isha’i.”?

“Aa ban sani ba gaskiya, bari na kira Hamad yazo ayi dashi wa ya sani ko aure ya nema mashi shima.”

“Hmmmm, ni ko na tafi sai mun haɗa a taron.”

“To shikenan.”


“Ki shirya anjima zamu shashen Abba yana san magana da damu.”

“To shikenan, Allah ya kaimu lafiya Amin.”

Bayan sallahr isha’a kowa da kowa iyalen sarki Abdulmalak sun hadu a babban parlournshi suna jiran isowarshi suji kiran mai yake yi masu………….

MY FAN'S YA KUKE GANIN NEXT PAGE ZAI KASANCE, KUDAI KU BIYONI DANJIN YANDA ZATA KASANCE????

By Jameelah Jameey✍????

Share

Comment

Vote

LIke

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button