GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Excuss me Sir”…

Hakim yana jinta amman yayi banza da ita, dan tunda ya kalleta ya fahimcin fitsari ne ya kamata dan haka ya kudircin ma kanshi bai barinta fita sai dai tayi a wando, dan yanda ta cimai mutunci cikin mutu a join itama sai taga wulakanci yau din nan…

“Please Sir i beg Excuss me, “can you sit down or know? “…

“Sir i want to i.. “Shutup idiot i said sit down or cary your materials get out of my class”…

“Plea..se”…

Abunda Hakima tace kenan taji ruwan fitsari na bi mata kafafu, ba tasan lokacin da ta duƙe ba tana kukan bakin ciki dan tunda take ba’a taɓa ci mata mutunci ba kamar yau..

Ita dai Maryam da Yan class suna kallon ikon Allah, amman basu ji dadin abunda Hakim yayi ma Hakima ba dan cin fuskar yayi yawa ya wuce misali sosai…

Ko shi kanshi Hakim baiji dadin abunda yayi mata ba, dan tunda yake bai taɓa jin tausayinta ba kamar yau, amman dole ya rama abunda tayi mashi itama taji yanda yaji…

“Selient Class give me attension”..

Nan dai suka cigaba da lecture dinsu amman ba dadi dan gani suke yau cin mutunci Hakim yayi yawa dan ya cuce Hakima…

Itako Hakima tunda ta duƙe bata sake dago kanta ba, tana aikin kuka dan bata san wani kallar mataki zata ɗauka tsakaninta da Hakim, dan wata kallar wutar tsanarshi ke ruruwa a cikin zuciyarta…

Hakim bai fita ba sai da ya gama abunda ya kawo shi sannna fita amman duk jikinshi a sanyaye yake, da yake Hakim jarumine bai yarda aka gane mashi ba..

“Yi Hakuri Hakima tashi mu tafi ki chanza kaya dan Allah ma yaso na taho da wasu ɗinki da na anso wajen tarler na”..

“Na tsaneshi wallahi Maryam banda maƙiyi kamar Hakim insha Allah sai nayi mashi abunda bai mantawa dani”…

“Haba Hakima wai har sai yaushe zaku daina yar ramuwarnan? Nasan wallahi wani abu kika yi mashi shiyasa shima yayi maki haka”..

“Dan Allah kiyi hakuri ki ƙyaleshi ba dan ni ba, na roƙi wannan alfarma nidai yau a wajenki dan wallahi banjin dadin wanann faɗan da kuke yi, kudai baku taɓa haduwa waje ɗaya kamar annabi da kafiri? “

“Wallahi sai na rama Final na gama magana, ni gida zani muje kiƙa ni na chanza kaya kafin Dr Moha ya shigo”…

“Ok less go”..


Wanene Hakim..

Masarautar Zaria, Masarautace wanda tana ɗaya daga cikin Masarautun da ke babban a Nigeria..

Sarki Sulaiman Muhammd shine ya Haifi Sarki Muhammd Sulaiman, Sarki Muhammd Sulaiman shine ya Haifi Yarima Hakim, Yarima Hamad da Yarima Humad da Gimbiya Maryama da Gimbiya Sadiya su biyar ne Allah ya bashi a duniya…

Sarki Muhammd Sulaiman Gimbiya Zulaha ya fara aure ita yar’Sarkin Daura ce a kasar Katsina…

Allah ya daɗe bai ba Gimbiya Zulaha haihuwa ba, Gimbiya Zulaha ba karamin tashi hankalinta yayi ba, dan taga har sunyi shekara biyar da yin aure ita da Sarki Muhammd amman haihuwa shiru kake ji..

Ban inda Gimbiya Zulaha bata shiga ba dan ta samu taga ta haihu amman ba wani bayani tun tana zuwa asibiti har ta fara biye-biyen Malamai da bokaye itada baiwarta Lanto amman duk inda suke je kudin su ake ci a banza ba, dan ba wani chanji da Gimbiya Zulaha take gani..

Ana cikin haka Sarki Muhammd Sulaiman yazo mata da zancen karin aure, zai auri yar’sarkin Adamawa..

Tunda Gimbiya Zulaha taji Sarki Muhammd yayi mata maganar zai kara aure nan ta kara tashin hankalinta dan ba asirin da batayi ba dan karda Sarki yayi mata kishiya amman ina Allah ya kaddara sai anyi wannan aure, bayan sarki ya gaya mata bikin da wata ɗaya aka ɗaura mashi aure da Gimbiya Kubrah, suna kiranta da Fulani..

Bayan auren ba wahalar da Fulani Kubrah bata sha ba wajen Gimbiya Zulaha, dan magungunan hana haihuwa aka kama sa mata cikin abinci amman bata yarda tasha koda ruwa ba da ya fito daga shashen Gimbiya Zulaha ba..

Ana cikin wanann hali tsakanin Fulani Kubrah da Gimbiya Zulaha sai ga ciki a jikin Fulani Kubrah, tunda Gimbiya Zulaha ta lura da Fulani Kubrah tana dauke da ƙaramin ciki ba ƙaramin shiga tashin hankali tayi ba..

Dan batasan iya adadin kudin da ta kashe ba, wajen neman Malamai da Bokaye amman a banza dan bakin duk Zakaran da Allah ya nufa da cera kona mazuru a na shaho sai yayi shi..

Gimbiya Zulaha tana cikin neman Malamai sai itama ga ciki ya fito a jikinta, ba ƙaramin murna tayi ba, dan harta Sarki Muhammd Sulaiman sai da yayi murna yana godema Allah da ya bashi kyauta biyu cikin shekara guda..

Haka suka cigaba da rainon cikin su, amman duk da haka Gimbiya Zulaha bata ƙyale Fulani Kubrah da cikin ta ba, dan tayi alwashin bata haihoshi duniya sai ta kaudasu..

Hak dai Fulani Kubrah tai ta hakuri tana neman tsarin Allah daga sharin Gimbiya Zulaha dan tunda take ko sau ɗaya bata taɓa gayama sarki irin zaman da suke da Gimbiya Zulaha ba..

Duk da yana sane da duk abunda ke faruwa tsakanin iyalinshi amman ya samusu ido, dan yasan gidan sarauta ya gaji haka…

Cikin Fulani Kubrah ya isa haihuwa dan ta haiho santalelen ɗanta Namiji mai kama da ubanshi aka sama yaro suna HAKIM..

Da Gimbiya Zulaha taji labarin haihuwar Fulani Kubrah kuma ɗa Namiji ta haifa ba dan ƙaramin yaki tayi cikin ɗakinta ba ita ɗaya, haka ta baza amintatun bayin ta bin Bokaye dan ganin mutuwar ɗan da Fulani Kubrah ta haifa amman asiri bai tashiri kanshi tunda Allah ya tsareshi..

Bayan haihuwar Fulani Kubrah da wata biyar itama Gimbiya Zulaha ta haifi ɗanta Namiji shima yana kama da ubanshi dan shi yana da duhu ba kamar Hakim ba…

Ranar suna yaro yaci suna HAMAD, bayan Gimbiya Zulaha ta gama wanka ta cigaba da neman sa’a dan taci alwashin sai Hamad ya zama sarkin zauzau, ko ta wani hali..

Tare suke yin komai shida Hakim, ba ƙaramin kaunar juna suke ba haka suka taso komai nasu iri daya ne…

Suna da shekara biyar Sarki Muhammd ya auro Gimbiya Kilishi yar’Sarkin Suleja..

Ba yand Gimbiya Zulaha batayi ba dan karda Sarki yayi mata kishiya ta biyu amman ba yanda ta iya sai dai tasa ido yayi aurenshi..

Ita ko Gimbiya Fulani bata wani damuba ita dai tasa Allah gaba tana neman tsari daga masu sheri dan ba dare ba rana haka take wuni ibada da roƙan Allah..

Gimbiya Kilishi daga auren ta da shekara ɗaya itama ta haiho ɗanta Namiji mai bala’in kyau dashi masha Allah, yaro yaci sunan HUMAD..

Tunda Gimbiya Zulaha ta lura da Gimbiya Kilishi itama ba daga baya ba wajen bin Bokaye da Malamai dan sau biyu suna haduwa wajen Boka daban-daban shiyasa suka kulla Aminta ba dan ransu yaso ba..

Gimbiya Kilishi ta sama ranta ko ta halin ƙaƙa sai Humad yayi sarkin zaria, shiyasa itama ta hana kanta bacci take bin Bokaye..

Amman a gaban Gimbiya Zulaha nunawa take Humad bai isa ya riƙe mulkin zauzau ba tunda ga Hamad..

Soyayya sosai ke tsakanin Hakim da Hamad da kuma ƙaninsu Humad dan basu yarda ko ƙuda ya taɓa shi ba..

Tunda su Gimbiya Zulaha suka lura da shakuwa na shiga tsakanin yaransu sai suka kama hure ma yaransu ƙunne..

Haka Gimbiya Zulaha ta kama cusa ma Hamad san mulki, a hankali Hamad shima yaji yana san mulki tun yana yaro dan shekara goma.

Shi ko Yarima Humad bai yarda ya biye ma hudubar Mamanshi ba dan bai yarda ya hudɗa da Yarima Hakim ba..

Humad yana da shekara goma a duniya Fulani Kubrah ta haifi yaranta yan biyu duka mata, ranar suna yara sukaci sunan Maryama da Sadiya , lokacin Hakim yana da shekara goma sha biyar a duniya..

Gimbiya Kilishi da ta lura Hamad yana san mulki sai tayi mashi asiri tasa aka tusa mashi ƙiyaiyar Hakim cikin zuciyarshi sannan aka sa mashi shiririta da rashin san yin ibada..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button