GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan sun sunka gidan da aka kama mata, sannan suka dawo gida..

Gidane flat house, babban parlour ne da bedroom guda uku, sannan boys coters, nan masu gadi da direba zasu ringa kwana, Gimbiya Hakima da su Lantana kuma zasu ringa kwana cikin gida, amman bedroom din Gimbiya Hakima daban…

By jameelah Jameey????

Share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

13&14

Washe gari tun da asuba Inna Lantana ta tashi ta hadawa Gimbiya Hakima ruwan wanka..

“Allah ya da tsawancin kwanan Gimbiya Hakima uwar marayu, ga ruwan wanka nan ya jiranki..

“Ina Bilkisu take? “Ranki ya dad’e ai Bilkisu suna madafa suna nema maki abunda zaki karya kummallo kafin ki wuce bokon..

“Maza kije kice mata, ta sallami Azima ta taho ta taya ki fiddo man kayan sawa, dan ita Azima tafi ku sanann kyau…

“Angama yar’sarki, matar Sarki da yardar mai duka, “zaki tashi kije ki ban waje ko tsayawa zakiyi ki isheni da wannan maganganun naki, wanda basu da dadin sauraro?

“Tuba nike uwargijiyata, “maza tashi ki ban waje kije ki kirata ko kun dawo…

Nan Gimbiya Hakima ta shiga wanka da suna da eight, Lantana tayi mamakin yanda Gimbiya Hakima tayi mata yau, wai yau Gimbiya Hakima bata zageta ba da tace mata matar Sarki, bayan Gimbiya Hakima bata san ace mata haka tunda ita bata da niyar yin aure, tafi san ta zauna gida tana zuba mulkinta yanda ta gadama, Gimbiya Hakima kenan..

“Harma kun gama kenan? “Wallahi kin san halin Gimbiya Hakima, bata cin abu mai nauyi da safe shiyasa muka soya mata biredi sai dankali da Tea..

“Sannun ku to, ke Azima taso muje fidda mata kayan sawa har ta shiga wanka..

“Wai Inna Lantana kina nufin Gimbiya Hakima ce ta tashi tun karfe bakwai saura?

“Nima nayi mamaki, dan tun ina gyara cikin dakin baccinta naga ashema idonta biyu, kawai dai tana wasa da waya sai da na gama hada mata ruwan wanka sannnan nayi mata magana..

“Ku har mamaki kuke kenan?

“Ai abun mamaki ne Ba’ba Bilkisu,”to ku daina Mamaki ke Lantana kin manta yanda Gimbiya Hakima ke da san karatu? “Aah nasan tana da san karatu mana ban manta ba..

“To Azima bari na gaya maki wani hali mai kyau na Gimbiya Hakima, “to Ba’ba Bilkisu ina sauraranki, Amman bari muje my m fiddo mata kayan sawa kafin ta fito…

“To shikenan nima kafin ku gama na gama jera mata abinci, “to mun tafi, nan su Lantana suka tafi fiddo ma Gimbiya Hakima kaya, ita kuma Bilkisu ta jera mata abinci, bayan sun fiddo sanann suka dawo…

“Ba’ba Bilkisu na dawo ina sauraranki wallahi ni kasa fiddo kayan nayi sabo da zumidin naji kyan halin da Gimbiya Hakima take shi, matar da nasan bata da kirki da tausayi..

“Tabbas Azima maganarki dutsi, Gimbiya Hakima bata da tausayi Amman tana da hali mai kyau, kin san maiyasa nace maki haka?

“Aah Ba’ba Bilkisu sai kin fadi, “To bari kiji, Gimbiya Hakima tana san karatu quri’ani dan hadda ma gareta, idan dare yayi lokacin da ina kwana wajenta kafin ta ida girma, wallahi karfe biyun dare take tashi sallahr dare bata kwanta sai bayan ta gama azkar din safiya sannaan take kwantawa bacci…

“Wai Gimbiya Hakima jiya kenan sallahr dare ta tashi da naga haske a dakinta..

“Kwarai kuwa, ai duk daren duniya Gimbiya Hakima bata bacci, shiyasa zakiga karfe taran dare ta kwanta bacci..

“Ni sai nai ta mamaki, nace ita ta riga kowa kwanta bacci, Amman itace karshen tashi bacci, Ashe saboda da sallahr dare take kwantawa tun tara?

“Eh, sannan kinsan maiyasa aka bata uwar marayu? “Aa nidai ina mamaki ace Gimbiya Hakima itace uwar marayun kano..

“Tana bala’in tausayin marayu, dan Gimbiya Hakima tana da gidan Marayu ko ni kaina ban san adadinsu ba a cikin garin Kano, kuma ita take ciyar dasu, ta kuma yi masu dinkin sallah, sannan kuma ta sasu makarantar arabi da boko..

“Allah ya saka mata da alkhari, Amman maiyasa bata tausayin mu bayinta?

“Wannan kuma a jininta yake, haka Allah ya hallinceta da iszar mulki, jinin sarautar kenan, dan ma iyayenta suna yi mata wa’azi, nan ai haka Gimbiya tayi sauki tunda har take bude baki tace yi kaza..

“Wai kina nufin Gimbiya Hakima da bata yin magana?

“Eh haka nike nufi, da in zata saki aiki da ido take kallonki kin san abunda take nufi, kuma indan zata sa ayi horo sai anwatsa maka ruwanzafi ko na sanyi sannan ake yi maka bulala, bayan angama yi maka bulala tasa a daureka jikin wani abu sai kawuni sannan a kanka gida ladabi har na tsawon wata, sai da Maimartaba yayi tsaye sannan ta chanza hali.

“Wai Allah mun gode maka, “ku ga Gimbiya Hakima nan fitowa..

“Takawarki lafiya uwar marayu, “Bilkisu mai kuka dafa?

“Soyayyan biredi sai dankali da tea..

“Uhmm, nan Gimbiya ta zauna tayi breakfast, sannan suka rakota ta shiga mota sai A. B. U. ZARIA..

“Ranki yadad’e antashi lafiya?

“Lafiya da man kaine driver din da Baffah ya bani?

“Eh nine uwargijiyata, “ok Uhmm, nan ya bude mata back sit ta zauna, sannan ya zaga ya mazaunin drive ya tada motar, nan yayi horn masu gadi daman already sun wangale gate nan GIMBIYA HAKIMA suka dauki hanyar makaranta…

“Kana jina Bala? “Allah ya taimakeki ina jinki..

“Bance ka tafi ba indan ka ajine, ka tsaya har sai nagama lectures sanann zani mutafi gida tare..

“Angama Ranki yadad’e, Allah ya baku sa’ar karatu..

“Uhmmm! Abunda Gimbiya Hakima tace kenan ta cigaba da chatting dinta, gashi ta makara dan yanzun har takwais da minti talatin, Amman hankalinta kwance..


Woow wani santalelen handsome guy ne wadda Aqqalah ba zai wuce shekara 26 ba, dugone Amman ba irin sosai ba, farine ba,mai matsakaitan idanu Samanshi dauke yake da dogayen gashin idanu, girarshi a ciki take ta kwanta lufff, fuskarshi dauke take da dogon Hanci yayin da pink din bakinshi ya kasance karami dashi, Fuskarshi manne take da glass Amman class din na kara lafiyar idanu wato medical glass..

Lecture yake cikin natsuwa da kwaciyar hankali, Wanda duk rashin ganewar mutun idan prof HAKIM ABDULMATALAK ya koya maka sai ka gane saboda yana da method of teaching…

Ajin shiru kake jinshi kowa ya na ba’a ya baida hankalinshi waje prof Hakim, ana sauraran lecture ga shi kuma lecture din ta dauki dadi, har ma wasu daga cikin student din basu san lokaci yayi ace ya gama, wasu daga cikinsu yan matane, wasu kuma serious student ne wanda suka abunda ya barosu daga gidan iyayensu gaba…

Ji suke tashi kas! Kas!! Kas!!! Na tashi baki daya aji kowa waiga yayi yaga wace yar hutuce Wanan da take shigowa lecture yanzun anyi awa daya da fara lecture Amman ita sai yanzun take shigowa, kuma hankalinta kwace tana tafiya kamar bata makara ba, ta nuna bata san da akwai malami a cikin ajinba balle ya samu alfarma tambayar excuse..

Tafiya take cikin mulki da isa, sai busar iska take tana bada fadi, har ta isa wajen wani sit zata zauna sai kawai taji ance”Hey get out of my class, Gimbiya Hakima yi tayi kamar ba da ita yake ba, sai ji tayi ya sake cewa”I said get out of my class, you am talk to you..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button