GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Lantana!

“Naam Allah ya taimakeki, kije kice ma Barde a shirya man dawakai yau zani shakatawa da karfe biyun rana…

“Angama, Allah ya ja da tsawancin kwana..

Nan Inna Lantana ta tafi wajen Barde..

Nan Gimbiya Hakima ta shiga ciki, su Bilkisu suka fara yi mata tausa, azima tana karanta mata novel, kafin anjima su shirya mata zuwa shan iska…


“Lanto, “Naam Allah ya taimaki Gimbiya Zulaha, “ya kukayi da bokan Lawali?

“Cewa yayi ya zama dole sai ansa ma Yarima Hakim wannan maganin cikin abinci yaci yana ci zai mutu, amman sai in zai kwata bacci za’a bashi abincin yace, yanda ana wayar gari a tashi da gawarshi…

“Da kyau aikinki na kyau Lanto, Allah yasa wannan karan karda ya bata mana aiki, kinsan shi wani kalar mutun ne uwarshi ta batashi da rashin kunya..

“Gimbiya kibar komai a hannuna wannan aikin nawane, yanzun ma zan tashi naje na kai ma Mino kinsan tana daya daga cikin masu dafama Yarima Hakim abinci, na san zata yi aikin yanda muke bukata…

“Hakane Lanto, ni na manta da Mino bangaren Hakim take dafuwa, to tashi ki kai mata amman kice ta kiyaye dan Hakim wayau gareshi, sannan ta kula da idanun mutane..

“Angama ranki ya dade, na barki Lafiya..

Nan Lanto ta tafi shashen Yarima Hakim, wajen masu girki..

“Ranki yadade Gimbiya Zulaha, Yarima Hamid yana san magana dake, “ace mashi ya shigo..

“Allah ya taimakike, “Hamid sai yau ka gadamar dawowa cikin masarauta? “Haba Gimbiya to mai zan tsaya nayi cikin masarautarnan basu mata babu abun sha sai lemu da tufa..

“Wai Hamid sai yaushe zaka daina neman matan banza da wannan shaye-shayen da kake yi?

“Gimbiya very Soon na kusa daina, “haka kake san abaka sarauta kana wanann halin, ai kasan Maimartaba ba zai yarda da haka ba, shiyasa yafi san Hakim sama da kai..

“Shi Hakim din kunsan abunda yake aikatawa indan ya fita waje? Ai gwara ni na fito da halina kowa ya gani, kuma dole na zama SARKIN ZARIA ko suna so ko basu so..

“Kai dallah can matsa, muna yin abun mu cikin natsuwa da kwanciyar hankali zaka yi man hauka, waya gaya maka zakayi mulki mundun Hakim yana numfashi a doran kasa to baka ba mulkin kasar Zaria..

“To ni ki barni na wuka na tafiyar mashi da kai uban kowa ma ya huta…

“Rufaman asari Hamid, ba ruwanka kai dai kawai ka samana ido, ni nasan abunda nike yi, indai Mulkine sai kayi shi indai ina numfashi a doran kasa, dan haka kaje kayi hidimarka nima ka barni da tawa..

“To shikenan, na barki da hidimarki ni na wuce marace yayi zan hadu da wata baby yau ta shigo gari, kin san yan university sun fara dawowa..

“Wuce ka tafi, Amman Hamid ka kiyaye, saboda makiya, “na barki lafiya..

“Mariya! “Naam Allah ya taimakeki Gimbiya Kilishi..

“Ya kukayi da boka, “eh yace Yarima Hakim abashi kwana biyu zai fara aiki kanshi saboda yana da rikon addini da wuya aljanu su je wajenshi, kuma bai zina balle ko wajen zina suzo su shigeshi suyi aikin domin dole aikin da za’a yi sai da aljanu za’a yi shi…

“Naji, to shi wannan sakaran fa shida sakaran uwarshi..

“Eh Yarima Hamad yace anbarshi da wannan halin na shaye-shaye da bin mata, ita kuma Gimbiya Zulaha yace abarta ta gama bin bokayen sannan zaiyi aikinsu ita da Hamid bayan ya gama mai wahala aikin Hakim..

“To shikenan Mariya gaskiya naji labari mai dadi da marar dadi , taya za’a yi mu hana Yarima Hakim yawan wannan ibadar da ya daukarma kanshi?

“Shine abun dubawa, ki kwantar da hankalinki uwargijiyata ko da masifa sai YARIMA HUMAD yayi sarautar masarautar Zaria, sai kin zama uwar sarki kema wannan alkwarin boka ne..

“Naji, tashi ki tafi bakin aikin ki, ki kula sosai da abunda fulani dake ciki ita da wannan banzan yaranya nata, “insha Allah ranki yadade..

“Allah ya taimakeki Gimbiya Kilishi na neman iso, “ace mata ta shigo..

“An wuni lafiya Gimbiya Zulaha, “lafiya Gimbiya Kilishi, “ya Lanto ta dawo daga wajen bokan? “eh tadawo harma anyi sa’a, “anyi sa’a fa kika ce Gimbiya Zulaha,”eh anti sa’a gobe da safe ki tashi da shirin zaman makokin YARIMA HAKIM, “taya haka ta kasance?

Nan Gimbiya Zulaha ta gaya ma Gimbiya Kilishi yanda akayi da boka yace masu, ba karamin farinciki tayi ba, dan tana ganin cikin sauki zata ida kauda Gimbiya Zulaha da YARIMA HAMAD cikin lokaci kadan tunda sun kauda mata Yarima Hakim, “dole sai Humad yayi mulki, Gimbiya Kilishi ta fada cikin zuciyarta tana murmushin farinciki tace, “gaskiya Gimbiya Zulaha aji tsoranki aikin ki yana kyau, “Hmm Kilishi kenan angaya maki ni ta wasa ce, sai dai ba sunana ZULAHA ba..

Haka suka gama maganarsu sai da dare ya fara sannan Gimbiya Kilishi ta wuce shashenta cikin farin ciki..


“Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima, Barde yace angama komai fitowarki yake jira..

“Uhmmm! Abunda Gimbiya Hakima tace kenan..

Gimbiya Hakima ta cigaba da abunda take saida ta sha iska tayi ma Lantana nuni da alkaibarta, nan Lantana ta tashi ta sanya mata sannna Azima ta dauki wayoyinta da post dinta suka fito, da yake lokacin sanyi ne Gimbiya Hakima rigar sanyi ta dogan wando ta sanya dan maganin sanyi, ga kuma alkaibarta da aka daura mata, Gimbiya Hakima ba karamin kyau tayi ba, sannan suka fito ta hau doki su Lantana suna kasa suna take mata baya har suka isa wajen shakatawar Gimbiya Hakima..

“Azima, “Naam Allah ya taimakeki, “miko man wayata wanda nike chatting da ita, “angama uwar marayu, nan Azima ta mika ma Gimbiya Hakima waya, nan Gimbiya ta cigaba da chatting sai da taji duk bakin cikin da Maimartaba ya cusa mata shida Fulani ya gushe sannan suka dawo gida….

Bayan sun dawo wanka tayi tasa kaya mararsa nauyi ta kwanta aka cigaba da yi mata tausa ita kuma tana chatting, sai da dare yayi sannan aka kawo mata Tea da chaps taci sannan ta kwanta aka cigaba da yi mata tausa Azima nayi mata karatu sai da tayi bacci sanann suka dawo suma suka kwanta dan su huta…


“Kina jina ko Mino? “Eh Lanto ina sauraranki..

“Anshi wannan maganin ki tambatar kinsa ma Yarima Hakim abinci yanzun na dare nan ba sai gobe ba..

“Aiki mai sauki mana, yanzun a gabanki zan sanyashi ba sai kin matsa ba, “yauwa Mino shiyasa nike san aiki dake, “aiko bari ki gani, kinga na sa ko baki daya na juye shi ma..

“Na gani kinyi kokari, na na wuce, “to mu kwana lafiya..

Lanto na lafiya, Mino ta dauki abincin da tasa ma Yarima magani ta juye shi a shara ta zubdo shi ba Wanda ya sani, sannan tace ma wanda suke aiki tare ita daya ta kaima Yarima Hakim abinci yau ta hutar dasu, bayan sun tafi tayi sauri ta dafa mashi wani sabon abincin sanann ta kai mashi..

Su Lanto nacen suna jiran gobe da safe suyi zamab makoki????

Bayan Yarima Hakim ya dawo daga massallaci sai da ya biya yayi ma Fulani sai da safe sanann ya wuce shashenshi, bayan ya sha tea da yake hadawa da kanshi, dan da man shi baya cin abincin masu girki sai na Fulani, kuma bai cin abinci dare daman yana hada ruwan zafi da kanshi ya sha sanann ya cigaba da ibadodinshi yana neman tsari daga sharin makiya..

By jameelah jameey????

Share and comment pls
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button