GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Koda Gimbiya Hakima ta koma ɗaki wanka tayi sanann ta kwanata ta fara waya da Maryam bayan sun gama waya ta kwanata bacci dan zata tashi sallahr dare…

Washe gari bayan Gimbiya Hakima ta gama duk abunda take ta wuce shashen Gimbiya Fulani, bayan anyi mata iso ta shiga..

“Fulani ina kwana?, “lafiya lau Hakima ya kika tashi?, “Alhmdulh “…

“Daman kiran da nayi maki shine kyauta zan baki dan naji dadin abunda kika yi ma bayinki jiya, dan haka na baki kyautar zinari da azurfa sai kudi million ɗaya”..

“Fulani basuyi yawa ba?, “basuyi ba Hakima dan jiya ƙin farantaman sosai, “nagode Fulani”..

Sanann kije shashen Baffahn ki shima yana neman ki, anjima zakiji kuɗin sun shigo a asusunki, ga zinarin da azufarnan wuce dasu Allah yayi maki albarka”..

“Amin ya Allah Fulani, na barki lafiya “..

Nan Gimbiya Hakima ta wuce Shashen maimartaba bayan anyi mata iso ta shiga..

“Momy ina kwana?, “lafiya lau Daughter, ya kika tashi?, “Lafia lau, Baffah ina kwana?, “lafiya lau Mamana”..

“Naji dadin abunda kikayi jiya Allah yasa ki ɗaure haka, sanann anshi wannan makulin motane ki dauka na baki”..

“Baffah! TOYATA A M G MERCEDES 2020 ka bani fa?, “eh Hakima na sani, “wow! Nagode sosai Baffah Allah yaƙara girma, “Amin Hakima”.. pls

“Ni Hakima zan turo maki million ɗaya ta account ɗinki anjima, “nagode Momy, ina sonku sosai iyayena, na barku lafiya..

Nan Hakima ta tafi tana farin cikin kyautar da iyayenta suka yi mata, tana zuwa shashenta ta kira Maryam waya ta gaya mata..

By Jameelah Jameey ✍????

Share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

(Yar mutan kankia????????)

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

39&40

“Kilishi ya kamata ki tashi mu tafi wajen Bokan nan tunda ƙafafu sun ɗaga”..

“To Gimbiya yanzun daman nike shirin aiko maki Mariya naji ko kin shirya”..

“Amman kifara fita sanann na biyo bayanki duk da munyi ɓata kama amman mu kiyaye”..

“To mu hadu ta baya, dan yau sai naji abunda yasa Hakim bai mutu ba har wata hudun yayi”..

Niko nace da alamu Gimbiya Zulaha ta manta da Allah, dan naga kominta a boka ta miƙa shi ba ga Allah ba ☹️????

“To shikenan! Nima yanzun zan biyo bayanki, “kidai yi sauri dan nasanki da nawa sosai”..

Bayan fitar Gimbiya Zulaha, Gimbiya Kilishi ta fara magana kamar haka.

“Sakara ai ko bakice ba dole na biki wajen bokan nan naga idan yake nima na ringa zuwa dan da alamu aikinshi yana aiki”..

“Dole naga bayan Hamad, ke kuma Zulaha zan barki kiga bakin ciki, kina kallo Humad zai mulka masarautar Zaria, kina ji kina gani zan zama uwar sarki, shashasha kawai marar wayau kin ɗauki yarda kin ɗauraman”…

Haka Gimbiya Kilishi ta kama surutunta har ta gama shiryawa suka ɗauki hanyar zuwa wajen boka..

Wani ƙauyene cikin Zaria tafiya ce mai nisa amman ba sosai ba, dan wani dajin Allah suka kama ketawa suna shiga cikinshi ko tsoro basuji..

Dan a bakin tati aka ajiyesu saboda mota bata shiga cikin dajin, amman su Gimbiya Zulaha suka fidda tsoron komai suka kama zurma kai cikin wannnan gurmin dajin da bakajin kukan komai sai na tsubtsaye..

“Wai Gimbiya har yanzun bamu ida isowa ba?, “ai da nisa ƙadan ma mun kusa isowa, karki damu Kilishi wanann bokan aikinshi na kyau shiyasa bani aiko kowa nike zuwa da ƙafaffuna…

“Wai hakane kuma, kinsan ance zuwa da kai yafi aiki, “yauwa kinga ga bukarshi can mun iso..

“A shigo da baya-baya bamu bukatar Sallama wajen nan, karku cire takalminmu”..

Haka suka shiga da baya baya basu tsoran komai sudai burinsu bukatarsu ta biya shikenan..

“Gafara dai ubanmu, mai taimakonmu mai share hawayenmu”..

Kallon su yake da jaijayen idanuwanshi wanda basuda banbanci da manya nan take ya kalli Kilishi take yaji yana sha’awar kusantarta, dan tunda yake bai taɓe ganin macen da dayi mashi ba kamar Kilishi..

To fa Jama'a kunga fa Gimbiya Kilishi takai kanta da kafaffunta????

“Ku zauna”! ya faɗi yana zara masu idanuwa kamar na aljanu..

Nan suka zauna suka fara miƙe gaisuwa wajen boka.

“Gimbiya Zulaha yau kece da sabon jini?”.

“boko mai share hawayenmu wannan kishiyatace Gimbiya Kilishi itama bada burin taga gawar Hakim”..

“Amman ka bamu wata hudu kace zanga gawar Hakim boka shiru nikeji har anyi wata biyar, shine nazo naji ko lafiya?”..

Hahahhahha! “Ai daman Gimbiya nasan zaki dawo, angayaman zaki dawo keda Kilishi daman tambayarki nayi naji ko zaki yi man karya”..

“Ai aljanu sunce ba za’a kashe Hakim ba sai nan da Shekara biyar”..

“Shekara biyar boka? “..

“Haka kika ji nace Zulaha, nima sako aka bani na gaya maki dan sun fara aikin ma kawai dai zai kaisu shekara biyar shiyasa”…

“Boka amman ba za’a tambayesu su rike ba, domin shekara biyar tayi yawa, har fa Sallah baki ɗaya boka sun hanani kuma har Shekara biyara ban sake sallah? “..

“Dakata! Wata kallar tsawa boka ya bugama Zulaha sai da Gimbiya Kilishi tashi zata ruga Gimbiya Zulaha ta riko ta????..

“Turmurturs baya magana ya chanza, ko kin manta Zulaha? “..

“Ina neman afuwa boka hankalina ne ya tashi naji yace shekara biyar, Amman aneman afuwarshi na barmai wuƙa da nama baki ɗaya a hannunshi”…

“Yayi hakuri yace zaku iya tafiya, ki dawo nan da shekara biyar godia zakizo yi mashi dan gawar Hakim kawai zaku gani”..

“Godiya muke boka, ga wanann anbaTurmurturs ina godiya, “…

“A fita da gefe gefe a fidda takalmi”..

Nan su Gimbiya Zulaha suka fita ta gefe da takalminsu a hannu suka shiga mota sai gida ba wanda yayi ma wani magana a cikinsu har suka isa gida kowace tayi shashenta..

Washe gari bayan Gimbiya Kilishi ta gama abunda take ta wuce shashen Gimbiya Zulaha ta shiga bayan an mata iso..

“Gimbiya sannun da hutu”..

“Yauwa Kilishi! Ina nan abun duniya ya ishe ni Turmurturs yace sai nan da shekara biyar zai kashe Hakim, kuma baka da ikon neman raki sai kayi laifi”..

“Hmmm! Niko banga wani abuba ga shekara biyar, shekara nawa mukayi muna kashe kuɗin mu a banza amman bamu ganin cigaba? “..

“Hakane gaskiya, dan ni tun kafin a haifin Hakim ya duniya nike san na kasheshi”…

“Kinga dan Turmurturs yace nan da shekara biyar ai sai mu zuba ido, mu koma muga taya zamu kashe ubanshi kafin shekara biyar”..

“Shikenan! Kema kin kawo shawara mai kyau Kilishi, zamu san yanda zamuyi da ubanshi kafin shekara biyar ɗin..

Nan dai suka gama tautaunawa yanda zasu kashe sarki sanann Kilishi ta koma shashenta ta kosa dare yayi ko taje wajen Turmurturs itama ya kashe mata Hamad kafin nan da shekara biyar yana kashe mata Hamad daman ya kashe Hakim maimartaba ya mutu sai kawai aba Humad sarauta ita wannan abu yayi mata dadi zata jefi tsuntsubiyu da tarko ɗaya…

Niko nace ayya Kilishi tana san gaskiya kuwa, ace mutun burin yaga wani ya mutu wai harda mijinka saboda da duniya☹️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button