GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Shima haka takasance Hakim, tunda suka dawo kasa cin abinci yayi yana mamakin yanda Hakima ta tsaneshi da yawa har haka, yana san kasancewa da Hakima inuwa ɗaya koda ko zasuyi faɗan dasuka saba, duk da yasan cewa ba sonta yake ba amman yana san yaganta kusa dashi, sai yanzun ya ƙara amincewa da kunnunwanshi da idanuwanshi suna son Hakima, amman zuciyarshi bata son Hakima, yana taƙaicin yanda ita Hakimar batajin haka a taitare dashi, da tana jin haka da tayi kishi jiya da ya tura mata message zai mata kishiya amman a banza ko a jikinta, daɗinshi ɗaya ma shashe ɗaya zasu zauna ma dole ne zasu ringa ganin juna ko wani lokaci bacci kawai zai rabasu ko wane zaitafi ɗakin baccinshi, a haka dai ya kama tunaninshi yana hangon kyaun da Hakima tayi wajen al’adar bikin nasu, duk da yasan cewa Hakima kyaukyawace amman tayi mashi kyau sosoi haka har bacci ɓarawo ya kwasheshi.

Yau masarautar kano ta fara sanin zatayi hidimar biki, dan sarakuna da yan siyasa yan kasuwa da duk wani mai faɗa a ji a nigeria sai da ya hallaci kano dan kawai ɗaurin auren Gimbiya Hakima da Yarima Hakim, da yake ɗaurin auren 1pm za’ayi shiyasa jama’a suke samun damar zuwa ayi dasu tunda ɗaya ne za’a ɗaura auren.

“Haba Hakima dan Allah ki tashi ayi maki make-up ɗin nan kinsan one za’a ɗaura wannan auren naku kuma gashi yanzun 12 tayi amman kinƙi tashi ayi maki make-up haba please.”

Itadai Hakima bata ce ma Maryam komai ba, sai dai ido ta tabita dashi, kuma bata tashi ba, ji tayi an bugar mata cinya sannan tayi ajiyar zuciya tana cewa, “Maryam wallahi banson auren nan, banson Hakim kinfi kowa sani bansan ya zanyi ba.”

Ta sowa Maryam tayi ta zauna kusa da Hakima, tana zama su Maryama na shigowa suma direct wajen suka zauna dan sun san komai suma, dafa ƙafarta sukayi su duka ukkun sannan Sadiya ta fara magana, “Hakima munsan cewa baki san Yaya Hakim, amman kisani Yaya Hakim yana sonki yana kaunarki, Yaya Hakim yana yi maki so wanda har yanzun baisan adadinshi ba a cikin birnin zuciyarshi ba.”

“Ta…, “dakata Hakima mu gama gaya maki waye Hakim, da mai-da mai Hakim yake so da wanda bai so, koda baison ki idan kina yi mashi abubuwan da muka gaya maki wallahi zaki juya Yaya Hakim kamar ranwa, Hakim zai zama mijintane daki juyashi yanda kike bukata, domin zai soki kamar ranshi, amman idan kinbi shawarar da muka baki.”

“Yaya Hakim mutun ne maison a girmamashi, yana son kwaliya more expecially yaga kinsa jan baki, yana son yaga mace yar’kwaliya da kisisina da shagwaɓa, baya cin abincin bayi dan haka ki shiga da niyar ke zaki ringa yi ma mijinki sauwa , ki tabbbatar da ke gwanace wajen iya girki da kwaliya, Hakima tsafta tana gaba wajen sace zuciyar ɗ’a namiji yanga da jan aji ko yayake ko, dan kitson nan da kunshi zu zama abokanarki Hakima suma suna ƙarama mace martaba a wajen mijinta, ki rige Ibada da neman tsarin wajen ubangijinmu Allah, wallahi Hakima idan kika rige abubuwan da muka gaya maki sai kinzama zara a wajen Yaya Hakim, sannan naji watarana a lambu yana gaya ma Yaya Aliyu idan mace na cin chingum tana taso mashi da shi’awarshi dan haka sai ki tafi da kwalin chigum, wannan zaman da zakuyi ki kasance mai yawan cin chigum amman a gabanshi kina sa ƙananan kaya masu masifar ɗaukar hankalin ɗ’a namiji zaki sha mamakin yanda Yaya Hakim zai nemi ku sasanta kanku ku zauna lafiya mudai muna maraba dake muna kaunarki a matsayinmu na ƙannan Hakim.”

“Nagode sosai Sadiya, kuma insha Allah zanyi duk abunda kuka gaya man, amman mai Hakim yafi so wajen abinci.”?

“Yafi son tuwon shinkafa miyar kuka, sannan kuma yanason dambu sosai, “nagode Allah ya bar zuminci, “Amin ya Allah Hakima, ku taho ayi make-up ɗin sha-biyu da rabi har tayi fa.”

Nan aka yi ma Hakima kwaliya, wata atamfa tasa mai ratsin ja da baƙi atamfar tayi mata kyau sosai, sannan ta ɗaura alkarba sama ana ɗaura aure za’a tafi da amarya gidan mijinta, shiyasa ta shirya.

Kutsawa nike cikin mutune dan na kwaso maku rahota wata kallar kwaliya ango Hakim yayi, wai na samu na ganoshi shida friends ɗinshi, farar shidda yasa tasha aiki masha Allah ga babbar riga duk ya ɗaura a bisa rigar aikin ɓakin zare aka yima atamfar abundai masha Allah kawai zamuce.

Da kaga Hakim kaga ango dan bakinshi yaƙe kullewa dan murna, dan koshi kanshi yana mamakin yanda yake farin ciki har haka sai kace wanda zaiyi auren soyayya, amman shi yasan yau babbar ranace a wajenshi, ya rasa yanda zaisa kanshi dan murna duk da tsokanarshi da Aliyu yake amman bai damu ba shidai ya kosa ma a ɗaura auren bak ɗaya, dan ji yake inama ya matso da time ɗin.

Hausawa sunce rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya, to haka ta kasance dan yau aka ɗaura auren YARIMA HAKIM ABDULMALAK DA AMARYARSHI GIMBIYA HAKIMA ABDULHADI a kan sadaki naira dubu ɗari biyar, mutane da dama suka shida wannan ɗaurin aure, bayan angama ɗaura auren aka fara taya Hakim murna shidai kawai kallon mutane yake dan abun mamaki yake bashi wai shi yau aka ɗaurama auren da kuma Hakima, abunda yana bashi tsoro da mamaki, haka dai haka gama komai aka fara shirya ma amarya dan kanta gidan mijinta.

Wa’azi tasheshi wajen iyayenta guda uku, tasha kuka kamar ba gobe da Lantana da Bilkisu da Azima kawai ta tafi gidan miji, haka suka ɗauki hanyar Zaria domin kai amarya gidan mijinta.

By Jameelah Jameey✍????

Share

Comment

Vote

Like

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

77&78

Tun daga farkon masarautar Zaria ake yin busa anayi ma Hakima lalai da zuwa masarauta mai albarka, itadai Hakima kanta yana cikin alkarba bata ganinsu sai dai jinsu, shashenta aka kaita da addu’oi ta shigo gidan masarautar haka ma da addu’oi ta shiga shashenta da addu’oi ta shiga room din da aka saka ta, bayan tayi addu’oi ta zauna bisa gadon da yake mallakinta, ita dai Hakima abun mamaki yake ba wai yau itace a gidan miji, mijinma ba wani bane face Hakim makiyinta.

Bayan sun huta aka kawo masu abincin saukar Amarya sannan fa aka shiryama Gimbiya Hakima dan zataje gaida mutanan gida, kwaliya akayi mata mai kyau sannan aka fito da ita shima Hakim ya shirya ya fito tuni ita suke jira dan haka su kuma al’adarsu take idan aka kawo amarya zata je gaida iyaye ita da ango bisa doki, Hakim da kanshi ya ɗauketa ya ɗaura ta bisa doki sannan shima ya hau, direct shashen Gimbiya Zulaha suka dosa daga ita sai shi sai dogarawa masu lura da dokin da suke sama, suna isa ya sauko ya sauko da ita da, sanan yaje saitin kunnanta yace mata sai ta kula sosai kuma komai Gimbiya Zulaha zata ce mata karta ce mata komai iyaka kawai ta gaisheta sai da Hakima taji tsoro dan batasan lokacin da tayi addu’oi ba, hakan da tayi ya burge Hakim sosai riƙe mata hannu yayi sannan yace “kwantar da hankalinki ba abunda zai faru, kedai kawai kiyi abunda nace maki.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button