GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Nagode Gimbiya, shiyasa nike sanki mahaifiya mai share hawayen ɗanta.”

“Tafiyarka Hamad Gobe zani nemaika kaji yanda mukayi da Turmurturs , “na barki lafiya Gimbiya.”

Haka Hamad ya tafi ya bar Gimbiya da tunani dan bata shirya rashin Hamad ba dan haka sai dai inda karfinta ya ƙare.

“Mariya ba zan bari ayi wannan aika-aikar ba, taya zan bari Hakim yayi aure muda muke san kasheshi.”

“Uwargiyata, Gimbiya Kilishi mai zai hana mu koma ma boka Dashshe nasan ba’a rasa yanda za’ayi ba.”

“Aa Mariya, bari kiga ba tafi wajen Gimbiya Zulaha mun san yanda za’ayi, “To adawo lafiya ranki ya daɗ’e.”

Nan Gimbiya Kilishi ta tafi shashen Gimbiya Zulaha hankali tashe dan batada wata mafita hankalinta ya fita jikinta bayan ta shiga dan yau ko iso bata aika nema ba wajen Gimbiya Zulaha ba sai dai kawai Gimbiya Zulaha taga Gimbiya Kilishi tsaye gabanta.

“Kilishi kenan daman nasan zaki zo shiyasa ban zo ba ni.”

“Ba dole ba Gimbiya, kinji abunda wannan sakaran mijin namu yace wai aure zai yi ma Hakim mu da muke jiran ganin gawa nan da shekara biyu, salan ya ƙara aza mana wani aikin a kanmu.”

”Hmmmm! Ni bansan ya zanyi ba, kuma yarinyar Hamad yace yana sonta amman san zuciya yasa akace Hakim zai aure ta.”

Sai da Gimbiya Kilishi taji kamar fitsari zai kunce mata a wando dan batayi tunanin Hamad zaiyi yana san yarinyar ba , amman ita tasan yanda zatayi.

“Tashi mu tafi wajen Turmurturs ko ya share mana hawayenmu, dan nima abunda naso nace kenan ai Hamad shi ya dace ayi ma aure ba Hakim.”

“Aiko dai amman ai mu ba’asan mu sai su an so ko?, “rabu dasu mudai mu tafi.”

Haka suka ɗauki hanyar zuwa wajen Turmurturs dan ya share masu hawaye a cewarsu ba????.

Bayan sun je wajen Turmurturs nan Gimbiya Zulaha ta fara bayani.

“Turmurturs ina san ka share mana hawayenmu, kamar yanda ka saba, wata sabuwa wai Abdulmatalak zaiyi ma Hakim auren da yar’sarkin kano.”

“Hahhhha! Daman inasane da zuwan ku, ku dakata kuji aure ba fashi sai anyi shi sai dai ansa wata mafita bayan auren nasu, kuma Hamad hakuri zai yi ta aure Hakim har bayan mutuwar Hakim sai ya maida auren Hakima kanshi.”

“Turmurturs. “Da kata Gimbiya Zulaha haka abun yake kuma haka zakuyi aure ya zama dole sai dai bayan bikin Turmurturs ya san yanda zaiyi ya hana Hakima ɗaukar cikin Hakim, amman duk wanda ta matsa tace sai ta hana bikin nan to nidai ba ruwana.”

Haka suka ajiye mashi kudi suka taho biki sake, bayan sun koma gida Gimbiya Kilishi ta fara magana, “Gimbiya shawarar Turmurturs kawai za mu bi, indai zai hana Hakima haihuwa da Hakim lafiya lau suyi aurensu nan da shekara biyu sai shi Hamad ɗin ya auri Hakima kinga sai ta cigaba da haihuwarta.”

“To nima abunda na gani kenan, dan haka zanyi ma Hamad bayani yanda hankalinshi zai kwanta, “yauwa ni na barki lafiya.”

Bayan Gimbiya Kilishi ta koma shashen ta ta buga ma boka Turmurturs waya take ce mashi ya san yanda ya hanaa Hakima ɗaukar ciki yanda koda Hakim da Hamad sun mutu sai a ɗaura ma Humad Hakima.

Kunji wata sabuwa kuma my Fans, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyarmu Amin????????

#JameelarhSadiq

Share

Comment

Like

Vote

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

63&64

×KANO×

Washe gari Gimbiya Hakima ta ɗauki hanyar shashen Maimartaba itada su Lantana suna take mata baya suna labari dan yanzun Gimbiya Hakima ta yarda da maganar Fulani da tace mata inma bata fiddo Lantana ba matsalarta, ta yarda da wanann maganar dan yanzun bata san abunda zai ɓatama su Lantana rai saboda suma basu san suga ɓacin ranta.

A bakin shashen Maimartaba suka haɗo da Yarima Annas na suka shiga tare su kuma Lantana suka tsaya suna gaisawa da dogarawan Annas.

“Yaya Annas wai neman mai Baffah yake yi mana.”?

“Hakima nima ban sani ba, amman may be maganar Aure zai yi mana da man wannan ranar tana nan zuwa tunda mun gama karatu.”

“Maganar Auren kuma Yaya Annas.”?

“Eh, amman ai ce maki nayi may be ko.”?

“Wai har naji hankalina ya kwanta, insha Allah ba maganar auren zai yi mana ba dan miko ban shirya aure yanzun ba.”

“Allah ko Hakima.”?

“Sosai ma Yaya Annas, “Ok Hakima Allah ya bamu sa’a dai, “Amin ya Allah Yayana.”

Haka suka shiga parlourn Maimartaba amman Annas yana mamakin yanda Hakima take furta bata shirya aure yanzun ba bayan tasan Maimartaba ba ƙyaleta zaiyi ba, ko shi Maimartaba ya ƙyaleta to shi ba zai ƙyaleta ba haka suka shiga suka samu waje a kasa suka zauna shi kuma Maimartaba shida su Yakumbo suna bisa three siter suna kallon yaran nasu yanda suka haɗa kansu hakan yana yi masu dadi, bayan sun gama gaidasu sannan Maimartaba ya fara magana.

“Mamana.”

Sai da gaban Gimbiya Hakima ya tashi da taji da sunan ta Baffah ya fara kira bana Yarima Annas ba, kasa magana tayi sai dai ɗago kanta da tayi tana kallon Baffah jira take kawai taji abunda zai gaya mata, koda Maimartaba ya fahimci sarautar har ta hau kanta ba ansawa zatayi ba amman hankalinta baki ɗaya yana wajen shi sai ya cigaba da maganar shi.

“Hakima na fidda maki mijin aure nan da kwana biyu zai zo kuga juna sai ayi biki ɗan sarkin Zaria ne.”

“Nagode Baffah, Allah ya saka da Alkhari, nasan ba zaka zaɓe man abunda zai cutar dani kuma ya zama dole na bi Umirninka dan kaine mahaifina kafi kowa iko da ni, ina godiya Baffah Allah ya ƙara girma da ɗaukaka.”

“Allah yayi maki albarka Mamana,nasan bazakiyi kuka ba akan zaɓin da nayi maki Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri’a ɗaiyaba wanda zasu taimaki al’umma baki ɗaya.”

“Amin.”

Baki ɗaya parlourn suka ansa banda Hakima ta da duƙe kanta kasa tana wasa da zoben zinarin dake maƙale a hannunta bata damu ba dan Baffah ya fidda mata miji ba ita dai fatanta Allah ya basu zaman lafiya.

“Allah yayi maki albarka Daughter, nasan Baffahnki ba zai zaɓa maki abunda zakiyi kuka ba.”

Ita dai Gimbiya Hakima ba tace komai ba, amman tana mamakin wai ita za’ayi ma aure yarinya da ita.

{hahahha! Team Hakim kunji wai Hakima bata isa aure ba????}

“Sai kuma kai Annas kaima ka zama cikin shiri dan aurer da kai zanyi ina nema maka mata dai-dai dakai, dan haka ka zama cikin shiri.”

“To Baffah godiya muke, Allah yaja da tsawancin kwana, “Amin zaku iya tafiya Mamana ki fara shirin zuwan baƙon naki, “To Baffah insha Allah mun barka lafiya.”

Bayan sun fito suka wuce shashen Gimbiya Yakumbo baki ɗayansu, bayan sun zauna Yakumbo ta fara magana.”

“Daughter Allah yayi maki albarka, gaskiya kin burgeni Daughter kuma nasan Hakim yaron ƙirkine bazai cuceki ba, sannan mahaifiyarshi mutuniyar ƙirkice sai dai kun kula dan masarautar zaria ana tungu da surkule dan haka sai kin kula da hannunki.”

“Momy da man Yarima Hakim Baffah zai ba auren Hakima.”?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button