GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Aiko Hamad ya dunga masifa, dan ba haka yaso ba, ya so Hakim ya biye mashi..

Yarima Hakim zuwa fada, ya mike gaisawa wajen sarki, sannan fadawa suka mike mashi gaisuwa cikin mutuntawa, domin suna jin dadi huddarsu da sarkin nasu mai jiran gado..

“Gimbiya, wallahi raina ya baci, sai na kashe Hakim..

“Kai Hamad wai sai yaushe zaka gane kashe Hakim sai anbi a sannu, eye?

“Wani abi a sannu ni ki barni na dauke kanshi da wuka a gaban uban kowa..

“Kana san wahalar da mukayi a baya ta zama a banza? Ko kuma kana san na haukace?

“To Gimbiya ni na gaji da ganin Hakim cikin masarautarnan, wallahi na tsaneshi, yanzun haka yana fada fa..

“Duk da ka tsaneshi hakuri zakayi mu kasheshi a sannu,,dan idan ka kashe Hakim gaban mutane kai ma kashe ka za’ayi Hamad gaban kowa, kaga kenan mulki zai tashi daga hannunmu ya koma wajen Kilishi dan Humad kawai za’aba mulki, ina bani fatan ganin wannan bakar rana..

“Dan haka kabar komai a hannuna Hamad, wannan maganar ta zamu ta karshe tsakaninmu..

“To naji Gimbiya, ni na wuce, “ka biya shashen Kilishi ka gaidata, “to na barki lafiya..

Haka Yarima Hamad ya fito shashen Gimbiya Zulaha ranshi bace, dan yaso ta bashi goyan bayan kashe Hakim, Amman ya fidda hannu kamar yanda ta bukata shi dai yana jiran mulki…

Bayan ya gaida Gimbiya Kilishi ya wucewarshi hidimar gabanshi, dan su da sake ganinshi sai hali kuma..

“Ranki yadad’e Gimbiya Kilishi, Gimbiya Zulaha tana san magana da ke, tana bakin kofa, “Mariya je ki shigo da sakarai, “to angama Ranki yadad’e..

Nan Gimbiya Zulaha ta shigo bayan sun gama gaisawa su ka fara magana..

“Kin san mai ya kawo ni Kilishi? “Aa Gimbiya, “yauwa nazo nace maki ya aka tsaya wajen aikin Maimartaba tunda naga duk aikin da muke kanshi ba ta siri..

“Ai wannan aiki ne mai sauki, dan ban dauki kashe Maimartaba wani aiki ba..

“To shikenan, Amman duk da haka sai mun gyara shirin mu, “to Gimbiya insha Allah, “ni na wuce, sai sa safe..

To fa kunji wata sabuwa kuma, Ashe harda maimartaba ake shirin aikawa barzahu, Allah ya mare zuciyoyinmu daga aikata aikin da na sani ko wani kallar ne Amin????????????

By Jameelah Jameey✍????

Share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

17&18

Yau karfe biyu Gimbiya Hakima take da lectures sai da su Lantana suka ji kamar su fasa ihu…

“Lantana baki da hankali? Wai dan Allah har sai yaushe zakiyi hankali?ke duk yanda aka nuna maki baki gane sai kace mai kwakwalwar kifi..

“Allah ya huci zuciyarki, wallahi akasi ne aka samu..

“Akasi! Akasi kikace Lantana, to yau zan nuna maki ni Hakima ban yarda da wannan kalma mai suna akashi ba..

“Allah ya taimakeki, Ina neman sausauci, insha Allah banzan sa….. Tas!! Kake ji Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana nuna ta da yatsa sannan ta fara cewa, “ke wata kallar kidahuma ce? Inba kina kidahuma ba daga goge riga saboda sakarci irin naki kinbi ki toya, ni dallah can tashi kibani waje tsohuwar banza…

“Godiya nike Allah yaja da tsawanci kwana uwar marayu, nan Inna Lantana taja yan kafafunta ta tafi, tana hawaye saboda tunda take da Gimbiya Hakima bata taba yi mata wani abu da taji haushi kalar wanna, dan ko ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha Mari a wajen Gimbiya Hakima Amman yau taji haushin abun sosai..

“Azima, “Naam Allah ya taimakeki, “tashi ki sake goge man takalmin nan, dan nasan wacer mahaukaciyar hauka kawai tayi man..

“Angama ranki yadad’e, nan Azima ta sake goge ma Gimbiya Hakima takalmi, duk ba abunda takalmin yayi, Amman haka ta sake goge mata shi..

Gimbiya Hakima ba ta tashi tafiya makaranta ba sai karfe daya dai-dai gashi tana da dan nisa tsaka ninta da makaranta gashi lecture din karfe biyu gareta..

“Bala kayi sauri bansan na makara, “angama Gimbiya, haka Gimbiya haka ta kama azalzalar Bala yayi sauri, haka suka samu suka isa, karfe biyu saura suka yi parking a bakin depertiment dinsu..

Sauri sauri Gimbiya Hakima take saboda hango Yarima Hakim da tayi yana tafiya cikin natsuwa yana shirin shiga lecture..

Duk tasan yana ganinta hakan bai yana Gimbiya Hakima sauri ba, ita acewarta sauri take, Amman Yarima Hakim gani yake kamar bata san taka kasa, dan danan ranshi ya baci sosai Amman zai barta ta shiga dan shi kad’a yasan abunda zaiyi mata..

Gimbiya Hakima na shiga taje wajen Maryam ta zauna, gaisawa kawai suka yi Yarima Hakim ya shigo..

Kowa ya natsu ya maida hankalinshi waje Hakim, dan suna jin dadin koyawarshi, dan prof Hakim ba daga baya ba wajen iya lesson, dan haka shiyasa kowa ya kama kanshi ya naba’a dan ya samu abunda ya samu..

Baki daya hankalin Gimbiya Hakima yana kan lesson din da Hakim yake dan harga Allah taji dadin koyawarshi dan ba karamin ganewa take ba..

“Hey stand up yayi pointing din Gimbiya Hakima, Amman sai tayi kamar ba da ita yake ba, dan ta lura malamin nan yana da san raini ita kuma ba daukar raini zata yi ba…

“Ke! Ke wata kallar kidahuma ce? KO baki jin turanci? Babanki yayi asarar kudin registration, dallah can stand up idiot nonsense stupid girl..

Haka Gimbiya Hakima ta mike ji take kamar ta tsiga kasa ta nitse dan kunya, dan ba karamin kunya taji ba ta yanda taga kowa a ajin ita yake kallo kamar wanda tati sata…

Sai da Hakim yayi kusan minti ashirin sanan yayi time din Hakima…

Duk tayi laushi ta gaji, Amman ta daure dan bata san yan ajin suga gazawarta..

Questions masu wahala Hakim ya fara jefo ma Gimbiya Hakima, Amman ga mamakinshi yaga tana bashi amsa, sai kawai yayi mata wani question nan ta kasa bashi nan yace mata…

“Get out of my class, nan Hakima ta tashi ta wuce tazo dai dai fita Hakim yace meet me in my office, classrest ka anshin man matrix number dinta ka kawo man office dina.

“Ok sir, class captain yace, sannan ya cigaba da yi masu lecture, bayan ya gama ya Kama gabanshi..

Ita ko Gimbiya Hakima direct gida ta wuce ranta bace..

“Allah ya taimakeki, Allah yasa lafiya dan ban saba ganin uwargijiyata cikin s
Wannan yana yin ba?

“Azima so nike na san waye shi, waye ubanshi a cikin Nigeria, da har zai ci man mutunci a cikin mutane Azima?

“Tabbas ya tabka babban kuskure, dan bai san dawa yake magana ba shiyasa da baiyi maki abunda ya san ranki zai baci ba ranki ya dade….

“Kyale shi Azima, yanda yasa na zubda hawaye ta dalilin shi, shima sai na sashi zubda hawaye da idonshi, sai ya san ni GIMBIYA HAKIMA duk wanda yaci tuwo dani miya ya sha…

Haka dai su Lantana suka Kama fadanci sannan suka samu Gimbiya Hakima ta sauko daga dokin fushi, sannan suma hankalinshu ya kwanta haka har tayi bacci..


Hakim bayan ya koma gida wanka yayi yasa kayan shan iska ya tafi bayan gida domin shakatawa..

“Fulani,wai kinji abunda naji su Gimbiya Kilishi suna cewa, wai ko da bala’i sai sun kashe yaya Hakim…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button