GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

75&76


Tunda Hakim ya tashi ya ansa kiran da Maimartaba Abdulmalak yake yi mashi, duk da yaji dadin yanda ya bashi umirnin ya shirya yaje Kano ayi duk wata al’ada da akeyi dashi amman kuma sai yaji ba dadi tunda Hakima ba sonshi take ba kuma bata ɗaukin zuwan nashi tunda ya dawo daga gidansu Hakima bata kirashi waya ba duk da yasan bata da numbers ɗinshi, amman ai ba zasu yi mata wahalar samuba tunda Maryam ƙawartace kuma Maryam tanada numbers ɗinshi kamar yanda su Maryama suke da duka numbers dinshi.

Bayan ya koma shashen shi ya ɗauki waya ya kira Aliyu yake gaya mashi ya shirya zasu biki, dan basu dawowa sai da Amarya, bai damu da duk saigantakar da Aliyu yake yi mashi ba ya tsinke wayarshi ya kira Maryam yace ta turo mashi number ɗin Hakima, Maryam taji dadi sosai da Hakim ya tambaye ta number ɗin Hakima,tasan cewa ko sunyi aure Hakim ba zai biye ma Hakima ba suyi ƙarantar da sukayi ba a school.

Tura mashi number din tayi sannan yace ta shirya zasu kano biki itada su Maryama amman kar ta kuskura tace dasu Maryama zatazo balle shi, haka ko akayi Maryam tace mata zasuzo biki amman itada wasu course mate ɗinsu zasuzo, tunda maryam ta gaya ma Hakima take murna dan itaji dadi sosai ta samu kawar shawara da ita ɗaya da Azima kawai take shirinta tunda babu age mate ɗinta a masarautar baki ɗaya.

Haka suka gama shiri suka ɗauko hanyar kano shida su Maryam.


Yau tun safe bayi ke aiki tukuru saboda yau ake hawan daba, shiyasa kowa da yake masarautar ba zaune yake ba yana aikin da shuwagabannin bayi suka bashi.

Harta Hakima bata gida tana wajen make_up, kwaliya ake yi mata tana gani ta faɗa dan da ka ganka sai kasan kudi sunyi kuka bisa fuskar nan tata, yau su Maryam da wasu friends ɗinsu zasujo bikin, shiyasa tun safe bakin Hakima yake bude ta kasa kulleshi dan batayi tunanin Maryam zatazo mata biki ba, amman abun yayi mata dadi sosai.

bayan angama shiryata ta fito Amaryarta sak,marron material aka sa mata sai alkalbarta itama marron takalminta marron color ne dan kyai ko Hakima tayi shi dan ɓata lokacine wajen tsayawa na gaya maku kallar kyaun da Hakima tayi sai dai kuyi imaging da kanku ????.

Angama haɗa komai yanda ya dace dan su Hakim su iso har abinci sunci a shashen Yarima Annas Hakim da Aliyu suka sauka dan nan zasu zauna har agama hidimar bikin baki ɗaya sanann, Yarima Annas da kanshi ya kai su Maryam Shashen Hakima sunce abinci sanan sukayi wanka suka hau kwaliya suna cikin yin kwaliya Hakima ta shigo hauka ne kawai batayi ba san murnar ganinsu da tayi, bayan sun gama kwaliya suka jera suka fito da amarya dan kowa ya hallara banda Amarya.

Tun daga nisa Hakim yake kallon Hakima yana gaya ma Allah, dan tunda yake a duniya bai taɓa ganin mace mai kyau ba kamar Hakima, dan komai nata daban yake dana sauran, haka dai har suka iso wajen da zasu hau dokuna ita da Hakim suyi yar rere.

Hakima keda farin doki Hakim yanada bakin doki, kasa hawan dokin Hakima tayi, tayi kokarin taga ta hau amman ta kasa, Koda Hakim yaga ta kasa hawa sai ya sauko daga bisan nashi dokin ya je wajen Hakima dai dai setin kunnanta yace mata, “Idan kinsan baki iya hawa ba ai sai kice a taimakamaki yan mata, ba sai kinyi nukunuku ba.”yace yana kashe mata ido ɗaya.

Bata ankara ba taji mutun ya ɗagata sama ya ɗaurata bisa dokin yana ɗage mata gira ɗaya yana mata nuni da shine boss, wata kunya da takaici ya turnike Hakima wai ita Hakim zai ɗauka, sai kace wata ƙawarshi da zai ɗauketa kuma gaban su Yarima Annas da Maryam dan ya kama rainata, ita bama ɗaukarma dariyar da suke yi tafi bata haushi dan suka ƙara koɗa mashi kai, bayan ya ɗaurata shima ya sake hawan nashi sannan akayi masu counting one-three sannan suka ba dawakansu wuta.

Hakim abun mamaki ya bashi yanda Hakima ta zage tana san ta wuce ita a dole ta yo na ɗaya ba Hakim ba, shikuma Hakim daya ga haka sai ya ƙara ma dokinshi wuta in munite ya taddo Hakima kallon-kallon suke ma junanshi na Hakim yace mata, “Yarinya ke nemi alfarma a ɗaga maki ki wuce dan wannan wasan na jarumaine ba na ƙanannan kiyashi ba.”gwallo yayi mata sannan ya rage gudun nan Hakima ta wuce tayi na ɗaya, nan fa ƙawayen Hakima suka hau murna sunyi na ɗaya, bayan sun gama hawan dawakan akaci abinci kowa ya wuce masaukinshi.

Bayan Hakim ya huta ya ɗauko wayarshi ya lalubo number ɗin Hakima, ya daɗe yana kallon number sanann daga baya ya fara tura mata textmassege kamar haka????.

“Yarinya ki fara shirya zama da maƙiyinki, dan kinsan Yarima Hakim ba sonki nike ba kuma kinsan ke ba zaɓi na bace, nan gaba zaɓi na zata shigo ku zauna da ita dan haka take note.”

Tunda shigowar massege ɗin a wayar Hakima ta ɗauka ta karanta bada damu da abunda Hakim yace mata ba dan daman tasan ba son juna suke ba, dan haka itama ta mayar mashi da answer ɗinshi dan bata iya ɗaukar gaya magana marar dadi.

“mtssssss, daman wa ya gaya maka ana sonka, kaima ka shirya zama da maƙiyarka wanda bata sonka bata kaunarka kawai biyaiya zatayi ta aurenka, kuma in katashi ba ɗaya ba ka kawo uku bayan ni duk matsalar ko baka san sai ana son mutun akeyin kishinshi ba to ni bani sonka balle nayi kishinka take note, sannan kuma kayi gaugawar goge number ta cikin wayarka.”

Shigiwar massege ɗin Hakim ya karanta take yaji baiji dadi ba ,da man shi yasan Hakima bata taba sonshi, daman yayi message ne yaga ko zata damu amman ga abinda ta mayarmai da answer, shi dai Hakim gashi nan dai dan baiji dadin jikinshi tunda Hakima ta turo mashi answer, kwaciya yayi yana juye juye dan da ya kulle idonshi sai ya hango daukar da yayi ma Hakima ya daura ta kan doki, ko kuma da ya kulle idonshi sai ya tuno fadan da sukeyi a school, murmushi kawai yake dan abun yana yi mashi dadi sosai haka dai bacci ya daukeshi.

Itama Hakima bayan ta turama Hakim da answer suka cigaba da labarin duniya ita dasu Maryama dan daman can sun san juna shiyasa, sune basu kwanta ba sai wajen biyun dare sanan ko wancansu ta kwanta bacci.

Yau za’ayi wanki, wani program ne da ake gidan sarauta mai suna WANKI, wanki dai suna nufin wankin lailen da akayi ma Amarya, dan haka da wuri suka tashi suka shirya ba ƙaramin kyau Hakima da ƙawayenta sukayi ba, karfe hudun rana aka fara gudanar da wanki, gaskia ko Hakima taga gata wajen wanki dan ba ƙaramin kudi a zubda mata ba sai mangrid sannan a ka tashi.

Wanka kawai Hakima tayi ta kwanciyarta bacci, duk da ba baccin take ba tunanin zaman da zasuyi da Hakim Yanzun yake neman hanata bacci gashi gobe ne ɗaurin aurensu, tuna message ɗin da Hakim yayi mata ya tada ma hankali batasan sanda hawaye suka fara zuba a idonta ba, dan tasan zata sha wuya wajen Hakim dan ma saukinta gasu Maryama nan da Sadiya tana da abokan ɗebe kewa, gashi yan jere sunjr sunce a shashe ɗaya zasu zauna da Hakim, harda haka yake ƙara tada ma Hakima hankali, parlour ɗaya ne babba sai bedrooms da suka zagaye da parlourn kitchen kuma ɗayane toilet ne kawai basu haduwa da Hakim sai bedroom dan suma ance suna da yawa a shashen nasu, haka dai ta kama juyi tanajin su Maryam suna lissafa kudin da suka samu yau wajen Wanki, har suka gama laissafi suka kwanta bacci amman ita idonta biyu tana tunanin rayuwar da zata shiga daga gobe.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button