GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Haba Fulani, taya za’ayi Baffah yayi man haka?

“Yanzun kamar ni HAKIMA ace a rasa inda zani university sai a Nigeria, Nigeriar ma wai wata A. B. U. Zaria, salon tallkawa su rai nani su dauka matsayin mu daya dasu Fulani..

“Ke wacece inda mutun ba kamar su? Wai Hakima maiyasa baki san tallakawa? Basan ina kika dauki wannan mugun halin ba, shi tallaka ba mutun bane?

“Ke ba kowa bace face Gimbiya Hakima, daga nan baki wuce komai ba, kuma ya zamai maki dole kije karatu kasar zauzau, ni naji dadi da Maimartaba yace baki fita kasar waje..

“Ya zama dole ki koyi huda da tallakawa , dan baku da banbanci a wajen Allah nidai ina gaya maki gaskiya Hakima..

“Amman gaskiya Fulani ni bani zama hostel, “wanna kuma, ni na wuce, “to a huta lafiya..

Haka Fulani ta baro Gimbiya cikin bakin ciki da bacin rai dan Gimbiya tasa Maimartaba wasa yake da yace bai fidda data kasar waje karatu..

“Kash ni Hakima wai maiyasa Maimartaba yake san yana hadani da tallakawa, bayan ni ya san na tsani tallaka amman yanzun wai a rasa school din da ni GIMBIYA HAKIMA zani sai wai ABU ZARIA , amman shikenan..

Haka dai Gimbiya Hakima ta kama yan maganganun ta..

“Bilkisu!

“Naam Allah yaja da ran uwargijiyata, gani ina jiran umirninki na aiwatar..

Sai da Bilkisu tayi kusan minti goma tsugune tana jiran umirnin Gimbiya Hakima sannan tace..

“Ni kike jira naje na hada ruwan wankan da kaina kena?

“Tuba nike ranki ya dade..

“Yi man shiru duk baku da wani anfani a wajen, da zaran na hukuntaku ace ban yi maku adalci ba, bayan duk baku san aikin ku ba..

“Allah ya huci zuciyarki, ina neman sausaci rainki ya dade, anyi man afuwa insha Allah haka ba zai sake faruwa ba..

“Yi man shiru wawiya kawai dake, ku baku kama girmanku kurkure har na nawa kuke yi man cikin gidan nan, dan haka tashi kiyi aikinki kice ma yan uwanki gobe ina san ganinku dan tashi ki bani waje..

Nan Bilkisu ta tashi jikinta na rawa tana godema Allah da hukuncin Gimbiya Hakima ya tsaya iyakar zagi da bata yi mata hukuci irin na Lantana ba..

Haka ta shiga toilet ta hada mata ruwan wanka..

“Ranki ya dade, na gama hada ruwan, haka Bilkisu tayi tsaye tana jiran tashin Gimbiya, tana jin ina ace tana cikin masu yi ma Gimbiya girki ko gyaran gida da yanzun ta can ta na hutawa, amman yanzun su ke hadama Gimbiya ruwan wanka da kuma bata labari har sai tayi bacci ita da Lantana, sai da Gimbiya ta gadama sannan ta tashi ya shiga wanka, kafin ta fito Bilkisu ta gyara gado ya fiddo mata kayan sawa.

“Je ki hado mani tea ki taho man da tufa..

“Angama ranki ya dade, Bilkisu ta tafi jikin na bari ta hado ma Gimbiya Tea mai kyau da dauko mata tufa harda ayaba ta kawo mata, nan ta bare mata ayaba ta miko mata, sannan ta zuba mata Tea din a cup ta mika mata..

Kawai sai Bilkisu taji an watsa mata ruwan zafi a fuska cikin bacin rai Gimbiya ta fara magana..

“Dan mai zaki hado man Tea ki sa man sugar?

“Allah ya huci zuciyarki, naga haka kika ce adinga samaki sugar in za’a hado maki shayi..

Tas! Tas!! Tas!!! Gimbiya Hakima ta wankama Bilkisu mari tana wurga nata ayaba a jiki da sauran Tea din da ya rage tana ce mata..

“Dan nace ku ringa sa man sugar sai nace maku kullun ko?

“Aa Allah ya huci zuciyarki, ina neman sausacin hukunci gurin uwargijiyata uwar Marayun masarautar Kano..

“To ubanwa zai gyara maki wajen? “Ina neman afuwarki yar masu gida, yanzun nike jiran umirnin tashi Gimbiya..

“Tashi maza ki goge wajen ki ban waje ki sheda ma shashasun masu Aiki bangareni irinki gobe karfe shiddan safe ina bukatar ganinku kafin kowace ta fara Aiki..

“To insha Allah, godiya muke Gimbiya uwar-adalci ga tallakawanta, nan ta tashi tayi mopping din wajen sannan ta wuce tana godema Allah da ya kubutar da ita daga mumunan hukunci Gimbiya Hakima..

By jameelah jameey ????_

Share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY
Jameelah jameey ????

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

03&04

Tunda Asuba su Bilkisu suke tsaye jiran Gimbiya Hakima, hankalinsu duk a tashe yake baki dayan su suna tsoron hukuncin da zata zartar a kansu..

“Wai Ba’ba Bilkisu mai mukayi ma Gimbiya Hakima?

“Wallahi A’bu nima bansan mai mukayi ma Gimbiya Hakima ba, amman karki so kiga yanda jiya ranta ya baci, ko nima nan dakal nasha dan harda mari sai da na sha cikin daren nan..

“Yanzun Ba’ba Bilkisu ke din Gimbiya Hakima ta mara? “Yo sau nawa akayi Murja ai sai dai kar’asake indai marine munsha shi wurin Gimbiya Hakima nida Lantana yunzun kinga Lantana tana gidan hukunci dan ma Allah yaso ta yau za’a fiddo ta, da sati biyu ta yanke mata..

“Wai dan Allah maiyasa Gimbiya Hakima bata biyo halin iyayenta ba, baki daya Gimbiya Hakima bata da tausayi balle imani, da tana da tausayi da bata mari kamar su Ba’ba Bilkisu ba..

“Hakane gaskiya Ladi, shiyasa na godema Allah da nike wajen dahuwa kawai, shiyasa kullun nike kiyaye wulakancin Gimbiya Hakima, domin bata gani girman kowa cikin masarautar nan..

“Aiko Larai, kinga yanzun har karfe goma na safiya yayi amman har yanzun bata yi lokacin mu, itada tace tun shiddan safe take san ganinmu, amman shiru kuke jinta..

“To ya zamuyi Ba’ba Bilkisu, ai hakuri zamuyi tunda haka Allah ya kaddari rayuwarmu, “aiko dai ai hakuri ya zama dole Larai..

Su Ba’ba Bilkisu suna can tsaye tun asuba, amman Gimbiya ta gyalesu kuma sarai ta san da tsayuwarsu a bakin shashenta saboda tun takwas din safe take ido biyu tanata chatting dinta sai da goma tayi sannan ta shiga wanka, bayan ta fito wanka ta shirya cikin wata purple din doguwar riga sannan ta fito tana tafiya cikin isa da mulki irin na sarauta..

“Sai yanzun kuka gadamar zuwa kenan?

“Muna neman afuwar Gimbiya, uwar Marayu, tun dazun muke nan muna jiran isowarki..

“To maiyasa bakuje kuka yi man magana ba?

“Allah ya huci zuciyarki, ai bamu da ikon zuwa turakarki batare da wani dalili ba, kuma ai kina bacci shiyasa..

“Matsalarku ce wannan, kuna jina?

“Eh muna ji uwargijiyarmu, muna jiran umarni daga gareki..

“Mtssss, wai ku wasu kallar jahilai ne dabobi wanda basu da gwakwalwa basu da lisafi da basu san inda yake yi masu ciwo ba…

“Allah ya huci zuciyarki, suka fada kansu a duge suna tsugune a kasa suna sauraren cin fuska da wulakancin da Gimbiya Hakima take yi masu..

“In ba kuna wawaye ba mararsa Ilimi ba, Wanda basu san daidai ba, yo ina anfanin zama da wanda basu da Ilimi, taya zakusan ya kamata bayan bakuda Ilimi..

“Afuwan uwar Marayu, Gimbiya Hakima diyar sarki jikar sarki uwar sarki insha Allah, muna neman sausaci ran Gimbiya Hakima, matar sarki insha Allah..

“Maiyasa baku san aikinku ba? Ku fi san kullun na kama yi maku magana daya sai kace wasu dokuna?

Su dai basu ce komai ba, dan yanzun su sunbar Mamakin halin Gimbiya Hakima, dan inda sabo sun saba da zagin wulakancin da Gimbiya Hakima take yi masu..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button