GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Kilishi kema ko? To tunda abun ya zama haka ku tashi ku ban waje ban zuwa da kowa baki ɗayansu daga ni sai waziri zamu tafi.”

“Allah ya huci. “Ya isa haka ku tashi ku ban waje.”

Haka suka fita ana hararar juna tsakanin Gimbiya Kilishi da Gimbiya Zulaha, ita dai Gimbiya Fulani Kubrah bata tanka ba nata ido duk abunda akace shi zatayi..

Bayan ta fiyarsu Sarki ya shirya ya sa aka kira mashi Hamad suka tafi tare ba dan yaso ba, amman ba yanda zaiyi dan shi da Hakim yaso zuwa amman haka Allah ya so.

Haka suka ɗauki hanyar kano, shi ko Hakim direct shashen shi ya wuce dan ya lura kwana biyu bai da aiki sai tunanin Hakima gashi ta tafi shi ko garinta bai sani ba, “maiye amfanin tunaninta!?? Wai mai ke damuna ni Hakim, ina no gaskiya ba haka bane ni Hakim zan so wannnan useless girl ɗin Allah ya tsari kakana da asara, kawai dai dan mun saba faɗa da ita shiyasa banjin daɗin gamawar da suka yi.”

Haka Hakim ya kama yan surutanshi har ya samu ya ɗauro alwallar wal’ha ya fara sallolinshi yana neman tsarin ubangiji Allah dan ya lura maƙiyanshi ba kyaleshi suke ba, shiyasa ya miƙama Allah lamarinshi shida ƙannanshi da kuma mahaifiyarshi.

Bayan ya gama sallahrshi ya tafiyarshi school ya fara marking ɗin papers din su Hakima..

Ko da yazo wajen paper ɗin Hakima yayi mamaki sosai dan yanda yaga waje ɗaya ta faɗi shima wajen final answer ne ta rubuta ba dai -dai ba.

“Uhmmm! Gaskiya yarinyar nan tana da koƙari shiyasa wani time ɗin take bugerni.”

Hakim ya faɗa yana ajiye paper ɗin Hakima wajen da yayi marking sai da yayi da yawa ba laifi sannan ya ɗauki hanyar Join domin yana bukatar refresh ɗin brain ɗin shi, saboda hayaniyar da su Gimbiya Zulaha su kayi ɗazun ba ƙaramin ciwon kai take sa shi ba.

Anya Hakim hayaniyar su Gimbiya Kilishi ta saka ciwon kai????, nidai babu ruwa na ????, Team Hakima ina jiran ansarku.

A gaskiya masoyana bani da bakin da zani yi maku godiya sai dai nace Allah ya bar kauna masoyana❤️????????

Tabbas naga masoya, da wanda nasani da wanda ma ban sani ba, ina ganin ruwan comments da ma fatan alkhari da masoyana suke yi man duk suna isowa gareni dan haka ba abunda zance sai Allah ya barman ku my Fans much love❤️????

*Yan wattapad kuma ba’a barku a baya ba, kuna nuna man iyakar kaunarku kuma inayin ku over and over kudia ku cigaba da comments and vote ni kuma na cigaba da surbudu mako da zafafan litaitafai da litafin na suna hanya very soon kudai cigaplease

biyoni ????????????????????????*

Yan facebook ban san mai Zance ba aiku sai dai kwando godiya da miko zuwa ga duk wani masoyana da suke facebook inajin dadin ganin comments ɗin ku kuma????

By Jameelah Jameey✍????

JameelarhSadiq

Share

Comments

Vote

Like

please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

59&60

“Ranki ya daɗ’e, asa maki eyeshadow ne.”?

“Azima kyalenni sosai kinga ya nayi idan ya dace a saman eyeshadow ɗin sai ta saman.”

“To Allah ya taimakeki.”

Masha Allah ba ƙaramin kyau Gimbiya Hakima tayi ba abunka da farar fata sai abun ya wuce masali, dan tsayawa na gaya maku irin kyaun da Hakima tayi ɓata lokacine dan haka Team Hakima wanan aikin naku ne sai ku gaya man kalar kyaun da Hakima tayi ????.

“Allah ya taimakeki gskiya ko ba’asa eyeshadow ba kinyi kyau a haka, amman a sanya maki dan ƙara ma kwaliyar armashi.”

“Uhmmm.”

Abunda Gimbiya Hakima tace kenan, sannan mai make-up ta cigaba da aikin ta bayan ta gama yi mata kwaliya wata arniyar atamface black and red a Hakima tasa sanann aka murza mata ɗaurin dankwali mai kyau da aji bayan angama ɗaura dan-kwalin ta ɗaura alkaibarta bisa kayan sanann tasa takalimin viccin half-shop tasa sai ta sake fitowa Hakimarta yar’shekara 22,bayan sun gama shirya ta dubu ɗari hudu ta ba masu gyaran sannan suka wuto gida.

Bayan sun koma gida direct shashen Fulani ta wuce nan ta sake gyara idan ta ga ya dace ta gyara sannan ta wuce shashen Yarima Annas su Lantana na take mata baya.

Bayan ta isa bakin shashen shi aka yi mata iso ta shiga su kuma su Lantana suka tsaya bakin shashen suna gaisawa da sauran bayi yan uwansu.

“Yaya sannu da hutawa.”

“Yauwa Hakima, masha Allah gaskiya ƙanwar nan tawa tayi kyau sai kace wanda zataje kasar kyau.”

“Haba Yaya Annas karka fasa man kai fa, “Hakima ai gaskiya na faɗi amamn sirikin nawa zai hallaci wannan walimar ko.”?

“Rufan asiri Yayana ina Hakima ina kula saurayi? Kaganni nan bani da wani saurayi kawai dai kwaliya akayi man saboda wannan walimar.”

“Hakima kina aikin mai baki tsada miji ba? Bayan kin san Baffah aure zai yi maki tunda kin gama karatu.”

“Yaya Annas am still young fa, duka duka yanzun nike da 22yrs ban isa na fara kula samari ba.”

“Shut up Hakima, ke ɗince baki isa kula samari ba dan sakarci irin naki na banza.”?

“Yaya Annas, haba maiyasa ni ba’a sona cikin gidan nan inba ba’a sona ba taya za’a yiman aure inada wannan shekaru.”?

“Hakima kisa ranki anyi maki auren dole angama, dan wallahi nasan Baffah aure zai yi maki kuma laifin kine, kinga ni da man nasan Baffah zai fidda man mata shiyasa ban kula ko wace yarinyaba, amman ke dai Baffah ya baki chain ke kika yi wasa damarki tashi mu tafi naga am fara taruwa.”

“To shikenan, nasan insha Allah Baffah ba zai yi man haka ba, “kina da wanda ki fidda a matsayin miji.”?

“Aa babu, “kinga baki da magana ƙanwata tashi mu tafi naji ance Sarki Abdulmatalak da Sarki Abubakar Sadiq sun fara isowa.”

“Saraukunan ina ne su?, “da Sarkin Zaria da Sarkin Katsina, “ok shikenan mu tafi.”

suna fitowa waje kunyangen suka take masu baya suna kirari suna cewa, “takawarku lafiya ya’yan sarki jikokin sarki, Allah ya taimakeka Yarima Annas sarki mai jiran gado, Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima, Gimbiya uwar’sarki da yarda Allah, kunyi gaba maƙiyanku suna bayan ku ba mai ganin bayan ba dai maƙiyi ba”.

Haka suka kama kirari har suka isa wajen da aka tanadarnasu domin zamansu, tunda suka taho Yarima Hamad yake kyallon Gimbiya Hakima take ya ji shi duniya ba wanda yake sha’awar aure inba ita ba dan bai san da yace Masha Allah ba saboda da kyaun da tayi mashi son Gimbiya Hakima ya shiga cikin zuciyar Yarima Hamad ba tare da ya fargaba.

Tunda ake yi masu wanna kirari har suka zauna sannan suka tashi suka fara miƙa gaisuwa wajen sarakunar da su ka hallaci taron da ma wanda basu samu damar zuwa ba suka aiko da Waziransu, tafiya suke cikin natsuwa da man Gimbiya Hakima ba daga baya ba wajen iya tafiya shima Yarima Annas ba’a barshi a baya ba.

Sunje gun ko wani sarki sun kai gaisuwa, ki wani sarki da kyautar da yake basu har suka zo wajen Sarki Abdulmatalak shine ya ba Gimbiya Hakima kyautar Mota shi kuma Yarima Annas ya bashi kyautar mota da gida.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button