GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Mu kwana lafiya.”


“Hakima gida ya ansheki sosai, “ba dole ba Maryam wanann karan Fulani da Maimartaba kamar su goyani dan kawai naci abincin dare da bayina.”

“Allah sarki, gaskiya nima naji dadi sosai dan Allah Hakima ki ƙara jan bayin nan naki a jiki please ƙawata.”

“Ai ina iyakar bakin ƙokarina naga ina bin shawarki sosai, “nagode Hakima, yanzun tashi mu shiga class Yaya Hakim ya shigo school tun eight kuma munada shi.”

Mtsssss”wai har level 2 ɗin ma sai Hakim ya koya mana ina dalili ina murnar na rabu da Hakim ashe mayen yana nan ya biyonu har 200 level sai da ya biyomu ina anfani.”

“Yanzun Hakima Yaya Hakim kike cema maye? Kuma a gabana bayan na gaya maki Yayana ne.”

“Naji mai Yaya, kedai wallahi kin bani da janye janyen wallahi ni taso mu shiga karda ya wulakantamu cikin mutane dan ba ƙaramin aikinshi bane.”

Nan suka shiga cikin class suka zauna, suna labari amman ita Hakima ranta ke ɓace dan ba karamin haushi take ji ba suna zaune Hakim ya shigo..

Ido cikin ido suka yi da Gimbiya Hakima, sai da gaban shi ya faɗi dan ba karamin kyau tayi ba, “yarinya har yarinya amman batada tarbiya bata san darajar na gaba da ita ba.”

Hakim yace haka cikin zuciyarshi dan yau ba karamin kyau Hakima tayi mashi ba, haka dai ya kama kanshi ya fara abunda ya kawo shi..

Class din shiru baka jin komai sai muryar Hakim, dan Hakim koyawa yake cikin kwanciyar hankali da natsuwa dan Hakim bai cika san hayaniya ba, shiyasa idan ya shigo class duk wani mai waya sai ya maidata swichoff ko kuma silent amman baya daukar yana cikin, lecture yaji wayar student dinshi tana ringing ko kuma yaga student yana wasa ko wani abu daban…

Dan shi Hakim yana san yaga student ɗinshi ya zama serious baya san yaga student un-serious ko koɗan a rayuwarshi kuma bai san marar kunya shi idan yaga mutun baida kunya to basu zama inuwa ɗaya dashi tsanar mutun yake shiyasa Hakim yayi hating din Gimbiya Hakima dan tunda ya lura bata da kunya ko ɗaya..

Suna cikin lecture, domin lecture ɗin ba ƙaramin dadi tayi masu ba baki ɗayansu more especially ma Hakima da baki ɗaya hankalinta yana wajen Hakim dan ba ƙaramin dadi lecture ɗin tayi mata ba..

Tana mamakin yanda Hakim ya iya koyarwa dan dun rashin ganewarka indai Hakim ya koya maka sai ka gane shiyasa take san lecture ɗin shi, sai dai bata iya daukar cin fuskar da Hakim ke yi mata cikin mutane..

Wayar Hakima ce ta dauki ringing baki ɗaya attendance ɗin class ya koma wajen Hakima dan kowa yasan roles ɗin Hakim baya san yaji ringing ɗin waya a class amman ga wayar Hakima nan tana ta neman agaji a dauketa..

Baki ɗaya jikin Hakima ƙarma yake, dan batasan ya akayi ba haka ta kasance ba ita dai tasan ta maida wayarta silent amman gashi taga akashin haka, duk bata ji dadi ba dan tasan conform sai Hakim ya wulakantata cikin class tana cikin tunani taji Hakim yana cewa..

“Tashi ki fita kibarman class kiyi wayarki, baki ɗaya baki ganewa balle rabawa inba kina donkey ba taya zaki shigo lecture hall da wayarki normal baki sata silent ba.”?

“Oya! Get out useless girl wanda batasan komai ba sai rashin wayau da rashin kunya monkey.”

Haka Hakima ta fita class tana bakin cikin yanda Hakim yake ce mata donkey and monkey, dan ita bata damu da yace mata useless ba dan bashi bane farko ba, amman wallahi bazata kyale Hakim ba tunda har ya ce mata donkey and monkey cikin mutane bayan ita tasan tasa wayarta silent…

Bayan fitowar Hakima, Hakim ya gama yi masu lecture ya kama gabanshi dan baki ɗaya baiji daɗin abunda Hakima take yi mashi , dan tana rainashi cikin student dinshi, dan haka dole ya dauki mataki mai girma gaskiya…

“Hakima dan Allah kiyi hakuri, wallahi nice na fidda maki waya a silent ɗazun kafin Prof Hakim ya shigo please forgive me Hakima.”

“Maryam bakomai ya wuce a wajena har abada, amman wallahi Hakim sai yasan yace ma GIMBIYA HAKIMA donkey and monkey cikin mutane dan wallahi zan hakura da komai amman banda wulakancin Hakim.”

“Ibeg you! Please Hakima kiyi hakuri wallahi bansan that habit, bai da kyau ko ɗaya ba’asan ramuwa dan Allah kiyi hakuri kinga rashi ne ya ɓaci shiyasa yayi maki haka amman wallahi Yaya Hakim ba haka yake ba mutun ne mai sauki hali ga sanin darajar mutane.”

“Dakata haka! Taya zaki yiman kallar wanann maganar? Bakiga abunda yayi man ba na fahimci baki sona to as from today bani bake wallahi Maryam karki sake nuna kinyi friendship dani idiot.”

“Wallahi baki isa kicemab idiot ba, kece dai idiot wanda batasan mutunci mutane ba, sai mai Hakima dan kince baki ƙara abotaka dani ban damu ba kuma nagode.”

“Uhmmmm.”

A bunda Hakima tacema Maryam kenan ta wucewarta gida dan tana mamaki yanda Maryam kullun take goyan bayan Hakim dan takamar yana Yayan ƙawayenta, haka har ta isa gida..

Ta kuma Maryam direct gidan su Hakim ta wuce, dan baki ɗaya bataji dadin abunda ya hadasu da Hakima ba, dan tasan Hakima tanada kyaun hali da mutunci, kuma taga itace bata da gaskiya,”why! Why!! Why!!! Why Hakima zaki ceman idiot duk da ranki na ɓace bai dace kiceman idiot ba kuma wallahi ban daukar wanann mulkin naki Hakima gaskiya.”

Haka maryam tatai maganar har ta isa gidansu Maryama…

By Jameelah Jameey ✍????

Share
Comment
Vote
Like

pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
         GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

     M. W. A

”’Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta ta kuma Nishad’antar da masoyan ta. ????????”’


  STORY AND WRITING BY

    Jameelah jameey ????

   (Yar mutan kankia????????)

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

”’NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????”’

43&44

Tafiya take tana tunanin wannan halin na Hakima, bata san yanda zatayi taga ta koyama Hakima Son Hakim ba..

Dan itadai tana san Hakima ta aure Hakim amman gashi su duka basu da maƙiya kamar junansu, haka dai Maryam ta kama wanann tunanin har ta isa gidan su Hakim..

Bayan tayi parking ta fito nan suka hadu da Aliyu shima shigowarshi kenan gidan wajen aiki yaje..

“Aaaa! Maryam kice a gidan namu.”?

“Yaya Aliyu ina wuni? “Lafiya lau Maryam daman kamar kinsan inasan ganinki.”

“Sai kuma gani Yaya Aliyu ina jinka.”

“Aiko naji dadin ganinki Maryam, ko zamu zagaya lambu muyi maganar dan tanada tsawo gaskiya ba laifi.”

“Alright then, let go Yaya Aliyu bakomai,”ok Maryam,  thank you sister.”

Haka Maryam da Aliyu suka dauki hanyar Lambu, Maryam tana mamakin wata kalar magana Aliyu zaiyi mata haka wanda bata yuyuwa a bakin mota har sai anje Lambu…

“Have a sit Maryam, “ok thank Yaya Aliyu.”

Bayan Maryam ta zauna nan shima Aliyu ya zauna ya fara magana kamar haka..

“Maryam nasan kina mamakin maganar da zanyi dake ko.”?

“Gaskiya hakane Yaya Aliyu ina mamaki sosai dan haka bata taɓe kasancewa ba shiyasa nake jin tsoro.”

“Ok kwantar da hankalinki Maryam, ba wata magana bace bayan ta ƙawarki Hakima.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button