GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Maganar farko Hakima yin biyaiya ga iyaye yanada mahinmanci ga rayuwa dan Baffah yasan waye Yaya Hakim shiyasa ya bashi aurenki.”

“Amman Maryam tsakani da Allah kin san bansan Hakim shima baya sona dan bakiji kallar maganganun da ya gayaman ba yau da sai na baki tausayi, NO Maryam Impossible ba banzan iya zama da Hakim ba please help me.”

“Keko zaki iya zama da Hakim, Hakima sai kace ba mace ba? Ke fa mace ce kinsan yanda zakiyi ki shawo kan Namiji ko waye shi wallahi, dan ba abunda Allah ya rageki dashi duk da ance mutun tara yake bai cika goma ba amman ke daban ce cikin mata.”

“Allah yayi maki kyau ga Ilimi, ke ɓata lokacine tsawa baiyana maki kallar baiwar da Allah yayi maki, kuma wallahi daga ke har Yaya Hakim ɗin kuna san junanku kawai san zuciya ya hanaku ku fahimci haka, amman very soon nan gaba zaku gane.”

“Gashi ance masarautar su bata da daɗin zama saboda maƙirci yayi yawa a cikinta Maryam.”

“Hakima ina wasu wanda muka taɓa gaisawa dasu su biyu lokacin da muna 300lvl.”?

“Wasu yan-biyu ko.”?

“Yauwa su, Maryama da Sadiya ko.”?

“Hakane na tunasu, maiya samaisu.”?

“Ai ƙannan Yaya Hakim ne, ta dalilinsu muke zuminci da Fulani Kubrah itace mamansu ni kuma makaranta ɗaya mukayi dasu tun nusery har university shiyasa nike cewa Yaya Hakim gunsu na sanshi, Yaya Hakim mutune mai mutunci da sauƙin hali ba zan tsaya gaya maki ba amman nasan nan gaba da ƙanki zaki gayaman halayen Yaya Hakim masu kyau ne shima da ƙanshi zai gane Gimbiya Hakima tana da hali mai kyau.”

“Kena nufin yan-matan nan ƙannan shi ne wanda mukaita labari randa n a rakaki wajensu.”?

“Kwarai kuwa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, labarin faɗanki dashi nike basu shiyasa suka ce suna san watarana su ganki shiyasa na janyo ki suka ganki.”

“Har naji sanyi wallahi Maryam ko ba komai na samu ƙawaye nadan ji sauki watarana.”

“Aiko kedai kiyi biyaiya Hakima watarana zaki san iyayenki sun maki zaɓin kwarai, “nagode Maryam wallahi ba ƙaramin kyautarman da hankali kikayi ba, ni zani shashen Gimbiya Yakumbo sai mun haɗu a Jameey Novel Fans anjima.”

“Ok shikenan, kin san ko yau akwai chapter sosai, “aikuwa sai mu haɗu dai dan yau ban kunna data ba nasan tayi posting ɗin A HAKA NIKE SONTA da YAN MATAN ZAMANI nasan yau za’a sha comment.”

“Idan kin dawo daga shashen Gimbiya Yakumbo kin karanta dan yau Fatima ba ƙaramin tausayi ta banta hmm gaskiya A HAKA NIKE SONTA ba ƙaramin dadi yayi ba Fatima tana ban tausayi.”

“Gaskiya nima Fatima tana bani tausayi, sanan Hafsat tana burgeni sosai dan tafi Zainab da Sadiya hankali wallahi, “nima Hafsat tafi burgeni a YAN MATAN ZAMANI dan ita tafisu sanin abunda take, amman su kawai sunce burinsu sai ya cika ta kowace hanya, “aiko kinsan ko haka yan matan zamanin nan suke, Allah yasa mu dace dai ni zan tafi sai mun haɗa a Jameey Novel fans ɗin.”

Sister idan baki karanta wannan litaitafin ki nemaisu dan karda a barki a baya A HAKA NIKE SONTA & YAN MATAN ZAMANI Hmmm ni ba zan ce komai ba sai dai indan kin karanta ke/kai zakuce komai????.

Bayan Hakima ta gama waya da Maryam ta tafi shashen Gimbiya Yakumbo.

YAN MATAN ZAMANI YANA HANYA MASOYAN MU, MUNAJIN KORAFE KORAFENKU NA HAR YANZUN MUNBAR YI MAKU POSTING TO ALBISHIRINKU YAN MATAN ZAMANI YANA HANYA DAN BAMU MANCE DA KU BA MASOYAN MU????????????????????????????????

A HAKA NIKE SONTA KUMA MUNA SANE DAKU ZAMU CIGABA DA YI MAKU POSTING AMMAN SAI KUN GYARA KUNA YI MANA COMMENTS YANDA YA DACE WANANN ALBISHIRNE NA BAKU MASOYAN BUK ƊIN A HAKA NIKE SONTA KARKU MANTA DR MUBARAK YANA SO DEEN MA YANA SO TO CIKIN WA FATIMA ZATA SO????????


×ZARIA×

Tunda Hakim ya koma gida yake mamakin yanda Hakima take furta bata Sonshi bata kaunar shi wannan kalma tana yi mashi ciwo bayan shi yasan idanuwanshi da kunnuwanshi ba abunda suke san ji da gani inba Hakima ba, amman zuciyarshi bata san Hakima, amman ita Hakima baiga haka tartare da itaba inba tsanarshi da yagani zallah a cikin kwayar idanunta taya zai zauna da Hakima bayan bata sanshi ta tsaneshi? {wannan answer team Hakima ku zaku ba Hakim ita ba dai ni ba????}

Da yaga abun bamai ƙarewa bane sai ya kira Aliyu yazo ya dawo amman su haɗu a shashen Gimbiya Fulani Kubrah sai su wuce Lambu.”

Bayan yaje wajen Gimbiya Fulani Kubrah nan yake gaya mata yaje yaga Hakima kuma tayi mashi ɗari bisa ɗari, Gimbiya Fulani Kubrah tayi farin ciki sosai dan daman bata da gurin da ya wuce da taga auren Hakim kuma gashi cikin ikon Allah lokaci ya kusa.

Bayan sun gama magana da Gimbiya Fulani, ya tafi Lambu shida Aliyu su kuma su Gimbiya Maryama da Sadiya suka hau Murna dasukaji yace tayi mashi dan daman sun san Gimbiya Hakima ce Abba ya nema mashi aure tunda sun santa kuma gidansu su biyune ita da Yayanta Yarima Annas.

Bayan sunje Lambu Hakim ya fara magana yana cewa, “Aliyu Hakima ce.”

“Bangane Hakima ce ba? Kodai kafara sub’batu Hakim.”?

Hmmm! “Ba sub’batun da nake Aliyu,Hakima ashe y’ar Sarki ce Aliyu.”

“Kana nufi Hakima itace wanda Abba ya nema maka auren ta.”?

“Tabbas Aliyu, Hakima itace wanda za’ayi mana aure wannan watan amman matsalar ɗaya Hakima ta tsaneni bata sona ko kaɗan, ni kuma zuciyata bata san Hakima amman kunuwana idanuwana suna san ganin Hakima da jin amon muryar Hakima.”

“Kaima karya kake wallahi zuciyar ka tana san Hakima yaudarar kanka kake Hakim, itama Hakimar tana sanka duk kuna yaudarar kanku nan gaba zakace na gaya maka amman shashen za’abudema Hakima sabo ko kuma shashenka zata zauna.”?

“Mun ma gama wannan maganar da Abba, shashena zata zauna tunda babba ne part ukune a cikin shashena to ba idan zata tana shashena ina lura da duk wani motsin ta, kuma banda matsala wajen mutanan gidanan dan Hakima bata kyale ta kwana nasan bazata shirya dasu Gimbiya Zulaha ba.”

“Nima harda haka na matsa ka auri Gimbiya Hakima dan nasan su Gimbiya Zulaha ba zasu samu fuskar da suce zasuyi wani aminci da ita dan ita Hakima kallo ɗaya zakayi mata sai kaji shaskarta ta shigeka haka Allah yayi ta.”

“Hakane Allah dai yasa mu dace, amman idan Hakima tace muyi zaman lafiya zamuyi mudun tace zaman rashin mutunci zamuyi wallahi zan biye mata daga baya mun sasanta, “Aa ban goyi bayanka ba Hakim, “saboda mai.”?

“Saboda nasan ka baka iya hakuri, “ko? Da da babu Hakima na mutu.”?

“Ai lokacin baka sama ranka ba, sanan ba ka ganin mace sai ka fita waje amman yanzun shashenka fa zaku zauna tare ai kai ba Sahabi bane da zakace bazakaji kana san ta baka haƙinka ba.”

Uhmmm! “Zanko baka mamaki, “Allah yasa tashi mu tafi sallah lokaci yayi, “ok.”

Bayan sum dawo daga sallah tea kawai Hakim yasha ya kwanta bayan ya tofe jikin da ayatul-kurshiyu da dai-dai addu’oi kala-kala sannan ya kwanta, kafin uku tayi ya tashi ya fara sallahr dare kuma sai asuba.

By Jameelah Jameey✍????

JameelarhSadiq@wattpad

Share

Comments

Vote

Like

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button