GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ba inda zani kuma dole nayi maka tsawa Hakim dan wallahi banji dadin auren da Abba yake niyar yayi maka ba, gashi bamu san garin da Hakima take ba da nabita na nemo maka aurenta.”

“What are you said?Aliyu kana cikin hankalinka kuwa? To bari kaji zanyi biyaiya na auri wanda Abba ya bani kuma zan koya ma kaina sonta after that kasan bani da budurwa to tada hankali name? Karka kuskura ka sake haɗani da wannna idiot gril ɗin take note”.

“Hakim wallahi kana yaudarar zuciyarka, kayi kokari ko bayan aurenka ne kaje ka nemo garin da Hakima take ka aure ta dan nasan tuni kadaɗe da kamuwa da soyayyar Hakima itama haka Hakimar dan haka is ur on choice ni kaga tafiya ta office kayi tunani.”

Haka Aliyu ya tafi yabar Hakim dan tunani, “Tabbas Aliyu bai ƙarya ba idanuwana sun kamu da soyayyar Hakima amman zuciyata ba abunda ta tsana kamar haka, how comes taya haka zata kasance? No impossible i hate you Hakima.”

Abunda Hakim yace kenan ya tashi ya wuce shashen Fulani ko yaji saukin abunda yake ji a cikin zuciyarshi.

Tunda Gimbiya Zulaha ta kira Hamad waya ya ɗauko hanyar zuwa dan ji yanda zasuyi Hakima ta zama tashi dan abun bata samu mafita ba yana aikata komai mudun Hakima zata zamo tashi, dan ya ɗaukarma kanshi zai iya kashe koda Sarki Abdulmalak ne mudun ya hanashi auren Hakima.

(Wai Allah na wata sabuwa anya Hamad yana da hankali kuwa????, taya zai kashe ubanda ya haifeka saboda mace, macen da bata san da zamanshi ba, Allah yasa mudace ya bamu zuri’a ɗaiyaba????????).

Bayan ya shigo royal house ɗinsu direct shashen Gimbiya Zulaha ya wuce dan yaji abunda zata ce mashi, bayan anyi mashi iso ya shiga ya samu waje ya zauna yana saurarenta dan baki ɗaya hankalinshi wajen mahaifiyar tashi ya maida shi.

“Hamad kanaji na ko.”?

“Eh ina saurarenki Gimbiya, “yauwa munje wajen Turmurturs amman yace aure dole ya ɗauru ba yanda zaiyi ya hana auren.”

“To naji kinga tunda shi Turmurturs ya kasa, ni bari yanzun naje na sarema Hakim kai da man naga yana gida tunda naga motarshi”yana tashi tsaye yake maganganun dan da gaske yake zuwa zaiyi ya sarema Hakim kai tunda shi Turmurturs ya kasa.

“Na  shiga ukuna ni Zulaha, Hamad baka da hankali? Ko dai kayi shaye-shaye ne kafin ka shigo gidan nan”.?

“Ba abunda na sha da hankali na wallahi kashe Hakim zaiyi ba zan bari ba ya auri Gimbiya Hakima ba, wallahi zan iya kashe koda ubantane balle Hakim da daman na tsaneshi komai za’ayi cikin gidanan shi Abba yake sawa saboda shine ɗan so, to idan na kasheshi uban kowa sai ya huta.”

Tas! Tas! Tas!, Gimbiya Zulaha ta wanke Hamad da zafafan marika har guda uku dan gani tayi sai ta mareshi zai dawo cikin haiyacinshi.

“Gimbiya ni.. “Yi man shiru ko na ƙara wankeka da  mari wallahi sakaran banza sakaran wofi, zaka zauna ko sai raina ya ɓaci.”?

Haka Hamad ya zauna yana dafe da kuncinshi da ya sha mari, wata sabuwar tsana yaji yana yi ma Hakim dan saboda shi Gimbiya Zulaha ta mareshi abunda Gimbiya ba ta taɓa koda dungurinshi ba amman yau shine tasa hannu ta mara becouse of Hakim.

“Hamad yaushe ka zamo wawa wanda baya aiki da tunani.”?

“Amman Gimbiya, “Amman mai Hamad kasan bala’in da zaka ballo mana idan ka kashe Hakim”.?

“To tsaya kaji ni, mudun ka kashe Hakim, to kaima kasa a ranka sai ankashe ka, kaga mulkin da muke jira ya koma hannu Kilishi kenan munyi wahalar banza.”

“Amman idan kabi a hankali ba wanda yaji ba wanda ya gani zamu kashe Hakim cikin ruwan sanyi, ba wanda zaice kashe shi akayi, “taya haka zata kasance Gimbiya? Sannan sai yaushe zaku kashe Hakim.”?

“Yanzun Hakim zai aure Hakima, amman boka Turmurturs yace zasu hana Hakima haihuwa da Hakim, suna kashe Hakim kuma sai a maida aurenka da Hakima kaga shikenan mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya.”

“Amman ina kishin Hakim ya rigani sanin Hakima a matsayin mace, zanyi hakuri da shawararku Gimbiya ni zan koma aiki.”

“To shikenan, karka kuskura na sake jin kalma sai ka kashe Hakim , kajini ko”.? “Eh naji na barki lafiya.

Tunda Hakim ya tafi shashen Fulani ya kasa komai dan ko abinci kasa ci yayi shidai kagashi nan kamar ba shi ba haka yake jin kanshi.

“Hakim ko baka san zaɓin da Abbanku yayi maka.”?

“Aa Fulani wallahi inaso, in ban bi umirnin iyayena ba umirnin wa zan bi, kawai ji nike kamar bani ba yau ɗina.”

“Ka yawaita addu’a Allah yana tare dakai kaji yaron kirki.”?

“Eh naji Fulani, ni gobe zan tafi kano ni ɗaya zani ko na tafi da Aliyu.”?

“Aa ka tafi kai ɗaya ganin juna zakuyi kuma bikin saura wata ɗaya haka naji Abbanka yace.”

“To Allah ya kaimu, ni zan wuce massallaci na barki lafiya.”

Bayan Hakim ya dawo daga sallah Tea ya sha sannan yayi addu’oi sannan ya kwanta dan ya gaji sosai ga washe gari zashi kano.


Tunda Hakima taji gobe Hakim zaizo bata zauna ba dan shiri take duk da tanajin ba dadi a zuciyata amman haka take ɗaurewa dan taba mutanan gidansu mamaki.

Bayan sun gama wani shirin dan Hakima ƙara komawa tayi wajen gyaran jiki aka sake yi mata su dilka sannan ta dawo gida, har yanzun bata samu lokacin waya da Maryam ba balle ta gaya mata ba, amman tana ranta tana san gaya mata, bayan ta dawo wanka kawai tayi sai bacci.

Washe gari tunda safe su Lantana suka tashi suka fara aikin tarar bako dan suke kamar mai abinci ake kala-kala dan har abun ya fara ba Gimbiya Hakima tsoro dan gani take kamar yau ce ranar bikin dan hidimar da bayin gidan keyi duk dan tarbar bakon da zatayi a yau kawai.

Too My Fans wani kallar drama za’ayi idan Hakima da Hakim suka ga ashe junansu zasu aura? Am watting urs Answers????????

BY Jameelah Jameey✍????

JameelarhSadiq

Share

Comment

Vote

Like

Please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

*(Yar mutan kankia????????)*  

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

67&68

Bayan anfito daga sallar asuba, Hakim yaje wajen Maimartaba yake gaya mashi tunda safe zai ɗauki hanyar kano dan baisan yayi tafiyar dare, nan Maimartaba yasa mashi albarka da fatan zuwa lafiya da dawowa lafiya.

Daga wajen Maimartaba wajen Gimbiya Fulani Kubrah ya wuce nan itama tayi mashi fatan zuwa lafiya da dawowa lafiya, sannan ta bashi wata super aura da wani laces dan two million tace ya ba Hakima idan yaje haka ya ansa yana godiya ya fita.

Shashen shi ya wuce ya ajiye kayan, sannan ya shiga wanka bayan ya fito daga wanka ya fara shiryawa cikin wani black bowel da kaga wanan bowel ɗin kasan kudi sunyi kuka a wajen sayanshi balle Allah kaɗai yasan nawa ya bada wajen ɗinkinshi, takalminshi dan campany oriflame shida watch ɗin da ya manna a hannunshi ita kanta watch din abun kalloce balle azo ga hular da yasa ita black and red Infact Hakim ba karamin kyau yayi ba.

Bayan ya gama shiryawa ya dauki hanyar Kano, yana mamakin yau shine zashi wajen mace da sunan zance, macen ma da yanzun sauran one mouth bikinshi da ita.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button