GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Laaa nima Maryama wallahi nima naje rannan suna maganar suna maganar randa na tafi shan iska ni daya banda ke Sadiya, har Mino tace man wancen satin har magani Lanto ta kawo asa mashi abinci, wai yana ci zai mutu, ke wani abunma bai faduwa makircin da asirin da suke yi ma yaya…

“Kunga duk kuyi man shuru da wannan surutun naku na banza, koma maiye mufi karfinsu da Ayar Allah dan haka ku cigaba da neman tsarin Allah ba na mutun ba..

“To shikenan Fulani Allah ya tsaremu, “Amin Maryama..

“Dan Allah Kilishi dubarshi sai kace wani sarki, wannan idan aka bashi sarki shida uwarshi banzaye zasu maidamu cikin gidan nan, tun yanzun yana wannan mulkin Ina ga ya zama sarkin..

“Kyaleshi Gimbiya lokaci kawai nike jira, wallahi indan har lokaci yayi Hakim jama’ar zaria baki daya mantawa zasuyi da anyi wani mutun Hakim, duk san da suke yi mashi ko, ke harta wanann munafukan yan biyun kannan nashi sai na shafe da babun su, balle uwar tasu…

“To wai yaushe wannan lokacin zaiyi Kilishi?

“Nan ba da dadewa ba, kedai kisa ido kiyi kallo, “shikenan Kilishi..

Nan suka gama meeting dinsu na kullun, sannan suka tafi..

Sudai su Gimbiya Kilishi basu da magana sai ta Hakim????????‍♀️, laile ko suna da aiki wanann shi ake kira aikin burus inji tusa????????‍♀️..

Sai da suka gama sannan suka tashi..


“Allah yaja da ran uwar marayu ga abinci nan yana jiranki…

Kallon Bilkisu kawai tayi, sai ta shiga toilet ta zubo ruwa a roba ta kawo mata ta wanke hannunta..

Hakan na nufin yau bata san zuw parlour yin dinner dan haka shiyasa ta wanke hannunta, bayan ta gama wanke hannu, suka hada kayan suka kawo mata..

Ana cikin zuba mata ta Azima taji tace, “tsaya! Azima waya ce ku dafa man kus-kus?

“Allah ya ja da ra’n Gimbiya Hakima ai ba kus-kus kawai muka dafa maki ba, harda macaroni, sannan kuma ga coffee nan duk munyi maki..

“Uhmmm!

Nan Azima ta zuba ma Gimbiya Hakima macaroni, nan suka zauna suna bata labari taci har ta gama ci, sanan suka kwashe kayan suka je suka wanke, sannan suka dawo Lantana da Bilkisu suna tausa, ita kuma Azima tana karanta mata novel har tayi bacci sannan suka wuce suma suka kwanta..

By Jameelah Jameey✍????

Share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

(Yar mutan kankia????????)

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

19&20

Washe gari bayan Lantana ta gama shiryawa Hakima littafan ta, saboda karatun da Gimbiyar ta fara na dare dan cikin week din nan zasu fara tests din su dan haka shiyasa ta fara karatun ta..

“Lantana! “Allah ya taimakeki gani gabanki ina jiran umirninki..

“Maza kije kice ma Bala, ya fiddo mota yanzun dan ayi fixing din lecture yanzun nan, dan haka yayi maza ya fiddo mota, gani nan fitowa…

“Allah ya kara maki jaraja angama, “Amin, nan Lantana ta tafi wajen Bala…

“Malam Bala, ka tashi lafiya? “Lafiya lau Lantana, ya aiki? ”Aiki da godiya, “To Allah ya bamu ladar, “amin..

“Sako daga Gimbiya Hakima, “mai kuma nayi Lantana?

“Kwantar da hankalinka, ba abunda kayi, “Alhmdulh, kin san wallahi Lantana ban san abunda zai hadani da Gimbiya Hakima da girmanka da mutuncinka, amman Gimbiya Hakima sai ta taci maka mutunci cikin mutane..

“Hakane gaskiya, Allah ya kara tsaremu daga cin mutuncin ta, “Amin Lantana, mai ita Gimbiya Hakima tace maki?

“Cewa tayi ka fiddo mota yanzun dan an maido masu da koyarwa yanzun da safen nan, shine tace ki fiddo mota ga tanan fitowa..

“To shikenan, ai yanzun kuwa zan fiddo ta, “ni na wuce Bala na barma lafiya..

Nan Lantana taje tagayama Gimbiya Hakima an fiddo mota..

“To ni zan wuce Bilkisu yau ki san kuyi man dambun masara, ku samu zagole kusa a cikin dan yau da bakuwa zamu dawo kuma tana san dambu…

“Angama uwargijiyarmu, Allah yabada sa’a, “Uhmmm, sannan ta gama gaban tana saurin dan yanzun seven thirty tayi gashi lecture din eight yayi fixed dinta, bayan basu da wata lecture sai two amman dan mugunta ya maidota eight…

“Bala kayi sauri, ban san na makara ka sani, dan haka kasan yanda zakayi kafin eight na ganin acikin lecture hall..

“To Gimbiya uwar marayu, Gimbiya diyar sarki uwar sarki insha Allah..

Nan Bala ya kama bankama mota wuta, Gimbiya Hakima sai da taji tsoron kalar gudun da Bala yake da ita cikin mota, to amman bata da choice din hana shi, dan idan sukayi wasa kan titin to zatayi late ne, kuma bata san wani abu yake hadata da Yarima Hakim, shiyasa tayi hakuri tana ganin rayuwa a iska.. (Lol sun Gimbiya Hakima ashe dai ana tsoro, kike iskanci????)

Cikin ikon Allah, karfe eight dai dai tayi ma Gimbiya Hakima cikin makaranta tana hango Yarima Hakim shima lokacin ya fito office din shi, dan haka tayi sauri ta shige warta ta zauna nan Maryam itama lokacin ta shigo ta zauna kusa da kawarta…

“Morning class,”Morning sir, “ok class listings attention, keep quite everbody, and get of a sit and sitdown pls, I said all of you keep quite…

Yarima Hakim ya fada cikin fada, sakamokon hango Hakima da Maryam da yayi suna ta surutu hankalinsu kwace..

Ba su san da shigowarshi ba sai da suka ji yayi tsawa sannan suka juyo lokaci guda, nan take Gimbiya Hakima taji bata dadi ba, dan tasan yanzun zai wulakantasu..

“Maryam, wannana idiot din kin san yanzun zai fidda mu waje, baki ga irin kallon da yake mana ba? Ta fada ma Maryam a hankali dan bata yarda lips dinta suka matsaba ma ba, balle yace tayi laifi dan Hakima tana san chemistry bata san ta ringa losing din lecture din shi, gashi ya iya koyarwa tana gane wa sosai..

“Mu boni Hakima gashi nan ya taho, “Uhmmm, abinda tace ma Maryam kenan, Ni kuwa nace yan mulkin sun taso kenan tun kan ya iso????.

“Hey you again? And you also? Kin biye ma wanann yarinyar zaki fara wasa da karatunki ko? Yace ma Maryam daya ke ba anan ba ya santa, ya santa kawarsu Gimbiya Maryama ce..

“Yaya Hakim dan Allah kayi hakuri, wallahi bamuji shigowarka ba..

“Saboda an koya maki jikkanci shiyasa baki shigowata ba, ita dai Hakima inda suke bata kalla ba dai da tana jin cin kashin da Hakim yake yi mata cikin class kowa na jinsu amman bata kyalesu har ya fidda Maryam waje sai ji tayi yace, “lock at you, stupid girl kawai, kina jiran nace maki get out ne? Oyaaa get out of my class idiot..

Gimbiya Hakima tsayawa tayi kallonshi, tana mamakin yanda yake san wulakanta ta cikin mutane, amman daga yau ba zai sake ba tace cikin zuciyarta, ta hada bag dinta ta fita ta baimar class dinshi, ga shi harda Maryam yau ya kora balle tayi mata tutorials din abinda ya kowa ya…

Bayan ya yi waje dasu Hakima ya cigaba da lecture din shi hankali kwance, dan shi ma kanshi yana mamakin yanda ya tsani yarinyar ce sosai, tunda yake bai taba tsanar wani mutun ba kamar ta, dan baya santa baya kaunarta ya tsaneta sosai…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button