GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Hakima kin fito kenan? “Eh Maryam ba dole ba na fito, wallahi na tsani Hakim bani kaunar mai kaunarshi, ya gode ma Allah ni dalibarshi ce, shiyasa nike jure duk wani wulakancinshi amman wallahi Maryam banda na yau sai na rama..

“Haba Hakima sau nawa zan gaya maki mai hakuri yana da riba? Kuma malaminkine duk kowa yasan yana wulakantaki amman hakuri zaki yi tunda keke nema wajenshi kinga dole mu ringa hakuri da malamanmu komai ko suka yi mana..

“Maryam kinga ina sauraran wa’azinki ko? “Eh gaskiya kuma ina jin dadin ka, “to dan haka tashi mu tafi samu abunda zamuci dan ni ko breakfast banyi ba na fito..

“Ok mu tafi nadai naci cake cikin mota, kafin na iso, “ai ni banyi wanna hausar ba ai da nasa Azima tayi mani cake, amman zansa tayi mani cake ko dan saboda da kallar wanann bakar lecture din tashi na kamaka rabona da bacci wallahi tun karfe biyun dare Maryam..

“Gaskiya kina kokari Hakima, nan dai suka shiga restaurant suka samu abinci suka ci, bayan sun gama, Hakima tace aka wo mata chip exotic chivita na watermelon..

“Hakima mai zakiyi da chivita bayan nasan baki shan exotic ke kika fadamn da bakin ki kin fi san ayi maki juice nan take dan baki shan chemical?

“To yau ina bukatar sha, ji nayi kawai ya burgeni da naga wannan guy din yana sha, “to ai sai ki sha mu tashi mu tafi wata lecture din..

“Aa ba yanzun zan sha shi ba, kiyi gaba gani nan tafe zan biya wajen Bala na bashi kudi ya samu abunda zaici dan shima baiyi breakfast ba muka taho..

“Ok sai kin iso, ni na wuce amman dan Allah kiyi sauri kinsan bansan zama ni daya sai naji duk ba dadi..

“Ok yanzun ko zan taho ai ba wani ajima zanyi ba..

Nan Maryam ta wuce lecture hall, ita kuma Gimbiya Hakima ta kama hanyar office din Yarima Hakim, tana zuwa tayi nocking..

“Yes, ya cigaba da aikin papers din gabanshi dan yayi ma level 2 test, kuma yasa ma Aliyu ne..

Nan Gimbiya Hakima ta shiga office din cikin takama da nuna ita watace dan harda taunar chigum take, bata san shi Hakim baya san yaga mace na tauna chigum sai yaji ya shiga cikin wani hali mai wuyar fassara..

Tashi yayi ya nuna mata kofar dan ko magana kasawa yayi tunda yaga tana cin chigum take felling dinshi ya taso more felling ma, shiyasa ya kasa magana dan idan yace zaiyi magana numfashinshi na iya daukewa shidai kawai ya narka mata narkarkin idanunan nashi da suka tashi daga fari suka koma ja dan tsananin azaba…

Sai da tayi kusan three minutes tana mashi kallon tsana dan ji take kamar ta zunduma mashi wuka a ciki ya muti ta huta da ganinshi..

Kawai Hakim ji yayi an watsa mashi abu mai sanyi ai take ya dawo cikin natsuwarshi, tsaya wa yayi yana kallon abunda Hakima tayi mashi, new gizina shaddarshi da yafara cewa a yau itace tayi ma haka gata fara ce sosai amman ta watsa mashi Jan abu a jikinta..

“This is a last warnings din da zai sake yi maka Hakim, ka fita a rayuwa hakanan karka sake shigarman rayuwa ni na fi karfin a wulakantani cikin mutane, kuma nace maka da man duk wanda yaci tuwo da Hakima miya yasha useless kawai ta kai, mtssssss.

Nan Gimbiya Hakima tayi tafiyarta class bayan ta gama yin abunda tayi niya…

Yarima Hakim kasa komai yayi, “wannan idiot girl din wai yar gidan uban wa ce, waye ubanta cikin zaria bama zaria ba duka kaduna da kewayanta, da ko zanga ubanki a gaban idonki zansa a yanke mai yatsan hannu dan dole na hukuntasu saboda basu baki tarbiya ba Hakima..

Abunda Hakim yace kenan ya tuna da papers din students dinshi Allah ma yaso basu jike ba, nan ya tartarasu a jiye ya kira Aliyu waya yazo ya daukeshi ya taho mashi da wasu kaya…

“Hakima ina kika je? “Lafiya wanann question din ka bayan kinsan nace maki zan ba ma Bala kudin abinci..

“Hakima ba wajen Bala kika je ba, dan yanzun na ba Bala kudin abinci dan yazo neman ki bashi izini yana san ya koma gida yace abinci har ya kowa maki naki inkina bukata..

“To uwata naji ba wajen Bala naje ba, shi kenan ko? “Wajen prof Hakim kika je ko Hakima? “Eh wajenshi naje wani abu?

“Haba Hakima maiyasa kika biyema zuciya eyeh? Hakima ya kamata ki sani ba komai ake biyema zuciya ba dan sai kazo kayi da na sani daga baya, kin ko san ki waye Hakim a garin nan ba ko?

“Da kata dallah Maryam bani bukatar nasan waye wani Hakim can, NI KINSAN KO WACECE HAKIMA A GARIN KANO?..

“Duk da haka ya kamata kiringa ragi ko yaya ne Hakima, ina san mutun mai sausauci da ragi Hakima, yanzun wanann Balan baki daya baki raga mashi ko kadan kuma shima mutun ne kamar ke yana bukatar hutu, haba Kawayata pls ki dan ringa rigi..

“Naji, amman indan Hakim yayi mani wallahi sai na rama, “to wai maikika yi ma Hakim din?

“Maifa zanyi mashi tunda ban iya dambe dashi? Kawai chivita naje na watsa mashi a jikin wannan tsunman shaddar tashi daya sa yau..

“Yanzun gizinarshi kika watsama chivita Hakima? “Kwarai kuwa Maryam take dubu dari shidda? Ni shadda inba ta kai million ba ban dauke ta shadda ba ke harda atamfa dasu laces dan haka take note..

“Uhmm gaskiya ne Hakima Allah yasa mudace, “Amin dai Maryam, ya naga har yanzun bai zo ba? “Eh ba wani abu yayi ba area of concentrate ya bada kawai..

“Ok shikenan, tashi mu tafi gida, dan nasa su Lantana sunyi maki dambu fa, “woow like uh Hakima gaskiya naji dadi sosai..

By jameelah jameey ✍????

Share and comment

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

(Yar mutan kankia????????)

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

21&22

“Hakim mai yasa mai kayan haka?

“Hmmm! Aliyu kaidai kawai ni banma ya san ya zance maka ba, amman wallahi Aliyu na tsaneta..

“Ka tsaneta? Wacece mai kuma ya hadaku? Kai da baka damu da mutane ba..

“Ban qaunarta I hate her wallahi, Hmmm Ammn, “gaya man wai wacece Hakim?

“Hakima wai ita sunan ta, bani san ta wallahi Aliyu, ko ganinta bani san yi..

Nan dai Hakim ya gaya ma Aliyu yanda sukayi da Hakima..

“Bala’i ko wacece wannan bata san ko kai waye ba shiya take yi maka haka, dan haka ka nuna mata kawace ajinta ta ko ina…

“Kyaleta Aliyu zanyi magana ninta ai tace duk wanda yaci tuwo da ita miya ya sha, to zata gane kurenta bani rigarnan nasa..

Nan Hakim ya sa rigar da Aliyu ya kawo mashi sannan suka wuce gida…

“Sannu da zuwa Maryam yau dai gaki temporary gidan Hakima..

“Gaskiya ko gani gidan Hakima, amman ita Hakima ko maganar zuwa namu gidan bata yi..

“Karki damu kisa a ranki Hakima tazo gidanku har angama, “to Allah yasa ita Hakima da gaske take, “da ma gaske take..

“Lantana! “Allah ya taimakeki gani gabanki ina jiran umirninki, “sai nace kuke wo ma bakuwata abin sha da abinci?

“Muna neman sausaucin uwargijiyarmu , “mtsss! Wai ku dan Allah wasu kalar jahilai ne mararsa gwalkwalwa baki daya har yanzun baku da lissafi, komai sai kunsa mutun magana..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button