GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Allah ya huci zuciyarki Gimbiya Hakima yar’sarkin kano jikar sarkin yola, muna neman sausaucin Gimbiya Hakima uwar adalci, uwar marayun kano baki dayan ta..
“Inba kuna banzaye ba… “Ya isa haka Hakima dan Allah, Maryam ta fada ta mai daga ma Hakima hannu ranta a bace dan taji haushin abunda Hakima tayi masu Lantana gasu sun fara manyanta..
“Mama tashi ki dauko mana abinci ki kawo mana cikin daki, “to godiya nike ranki yadad’e..
“Hakima mu shiga ciki mana, “maiyasa kika yi man haka a gaban bayi na?
“Shi ne nace mu shiga daga ciki magana zamuyi, “Uhmmm..
Nan su Lantana suka kawo ma Gimbiya Hakima abinci..
“Allah ya taimakeki, aci lafiya uwargijiyarmu Gimbiya Hakima uwar masu adalci..
“Dillah can tashi ki ban waje, zaki cika man kunne da surutun banza, kuma wa kika ajiye ya zuba abinci?
“Ina neman afuwarki, nan Lantana ta zuba masu abinci sannan ta wuce jiki ba dadi ..
“Hakima daman ke yar Sarki ce? Shiyasa kike yima prof Hakim abunda kika gadama, “Uhmmm! Ai ba sai na gaya maki ba Maryam, ni ban damu da ansa ko ni yar gidan waye ba..
“To shi Hakim din kin san ko waye? “Dakata Maryam indan muna tare ban san kina yi man maganar wannan useless boy din, dan na tsaneshi ban kaunarshi balle har na tsaya naji shi dan gidan uban waye bani bukatar wannnan..
“To shikenan Hakima, amman dan Allah ki daure ki ringa hakuri da wanann bayin Allah, wallahi Hakima su biyun sun haifi kamar har uku may be, gudarce dai bata isa haihuwar ki ba..
“Kinga bai kamata ba ace kina yi masu kallar wannan zagin ba, tunda iyayen wasu ne, kinga bai dace ba ina neman masu alfarma kawata..
“Ai laifin su ne Maryam, kinga ina yi ma Bala drive na haka? “Aa gaskiya ba kamar su ba, “yauwa kingansu nan baki daya basu da tunani balle hankali kuma, komai sai ance masu yi sannan zasu yi wallahi na gaji kawai zan ma Baffah magana a chanza man wasu bayin dan ni sukayi man sai nayi masu..
“Nidai bance kice a chanza maki wasu ba, a shawara ta amman kidai rage yi masu wani abun please mana..
“Tom naji, yanzun dai kici abinci, “tom mudai ci tare, “Uhmmmm..
Nan dai suka ci abinci, nan Maryam tayi ma Gimbiya Hakima wuni sannan ta wuce gida, itama tana jirin zuwan Hakima gidan su..
“Ranki yadad’e, Gimbiya Kilishi ga wannan maganin nan inji Boko yace a tabbatar da an barbadashi bisa gadon Yarima Hakim yana kwanciya zai samu ciwon mutuwar rabin jiki, kinga dole ya rage wanann bakar sallahr da yake yi har cikin dare sai a turo aljanu su ida nasu aikin…
Hahhahhahahaha”Mariya gaskiya aikin ki yana kyau sosai, yanzun wacece ki gyara shashen Hakim? Dan wanann aiki ne mai sauki boka ya bada…
“Eh Hasiya yace take gyara ma Hakim shashe, “Hasiya da kyau kice tamu mace take mashi, “eh ranki yadad’e..
“To Mariya yanzun aiki ya rage naki, “angama Amaryar Sarki kuma uwar sarkin gaba, na barki lafiya…
“Fulani sannu da hutawa, “yauwa Hakim har an dawo kenan? “Allah ya yarda, “Sadiya tashi ki dauko mashi abinci, “to Fulani..
“Fulani nifa a koshe nike, “ai nasani Hakim, ai kai kullun a koshe kake, kai dai har yanzun baka san cin abinci ko Hakim?
“Aa Fulani ina cin abinci sosai ma, “Allah yasa da gaske kake, “yaya Hakim ga abincin nan..
Kallonta kawai Hakim yayi Gimbiya Sadiya ta tashi ta barma masu waje, dan daman ita Gimbiya Maryama bata fito ba tana dakin ta..
“Kace abincin ko, “to Fulani, nidai Fulani ina mamakin ina Hamad ya koya wanann hali..
“Mai kuma Hamad din ya sake yi? “Wallahi ina hanyar dawowa naganshi shida wata yarinya cikin mota sun shiga wani hotel..
“Allah ya shirya shi, sai ka cigaba da neman ma dan’uwanka shiryar Allah, kuma ina sake maimai ta maka dole sai kayi hakuri dan kaine Babba, duk da dan watan nine tsakaninku ya zam dole kayi hakuri da yan’uwanka tunda jininka ne..
“Insha Allah Fulani, nan Hakim ya cigaba da cin abincin shi yana mamakin halin kanin nashi, dan daman tuni ya lura da Hamad yana neman mata…
“Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha, “Lanto da magana a bikin ki, gaya man ko Hakim ya mutune?
“Ko daya Gimbiya,Hakim ba mutuwa yayi ba, amman kinga wanann magani to shine ajalin Hakim, dan yanzun daga Niger nike wajen boka yanka daya..
“Maiyace ayi dashi maganin? “Eh cewa yayi kisa ma Hakim shi cikin shayi da hannunki sannan sai kije ki bashi yasha to yana sha zai mutu…
“Taya haka zata faru Lanto, bayan kinsan Hakim bai yarda dani ba, balle na bashi abu ya sha?
“Abu mai sauki ne Gimbiya, sai ki hada mashi ki kai mai, kice kinji ance bai lafiya kwana biyu, daman kinga ya bar zuwa gaisheki, kinga ba yanda za’ayi yake shan shayin da kika kawo mashi da hannunki…
“Hakane fa Lanto bari na tashi naje na hada mashi kinga dare nayi..
“Na manta yace sai kin baryin sallahr asuba kuma, “na baryin sallahr asuba Lanto, bayan ya hanani yin sallahr la’asar yanzun ya dawo yace ta asuba…
“To ranki yadad’e duka na sati nawane, ai kedai ba bukatarki kike san biya ba, ai nasa komai zaki iya yi Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha..
“Hakane Lanto, tashi muje muyi mashi sanyin nan, dan da zafi-zafi kan buga karfe…
“Kina jina ko Hasiya? “Eh Mariya, “anshi wannan maganin inji Gimbiya Kilishi ki tabbarta da kin barba ba dashi a bisa gadon Yarima Hakim..
“Wanann ai kinsan aiki ne mai sauki a wajena, “ai shiyasa Gimbiya Kilishi tace ke take so kiyi mata wannan aikin dan tasan baki da wasa wajen kallar wanann aikin..
“To kije kice mata ni Hasiya nace aikin ta anyi angama, to ni na wuce ki huta lafiya..
Nan take Hasiya ta barbadema Yarima Hakim magani nisa gado sannan ta cigaba da hidimar gabanta..
Gimbiya Zulaha ta gama hada ma Hakim shayi ta juya magani, sannan itama ta dauki hanyar shashen Yarima Hakim..
By jameelah jameey ✍????
Share and comment pls
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
*M. W. A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
STORY AND WRITING BY
_Jameelah jameey ????_
(Yar mutan kankia????????)
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????
23&24
“Ranka yadad’e, Gimbiya Zulaha ta kawo maka ziyara, “ziyara yanzun cikin daren nan? “Eh tana bakin kofa ma tana jiran ayi mata iso, “je kice mata ta shigo…
“Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha, Yarima Hakim yace ki shigo..
Nan Gimbiya Zulaha ta shigo, Lanto na biye da butun shayi a bayanta..
“Allah ya kara maki lafiya yau kice da kanki wajen da’nki? “Ba dole ba Hakim nayi kusan sati uku ban saka a idona ba, ko gaisuwarma mu bar cin arzikinta..
“Ba haka bane Gimbiya, aiki ne yayi man yawa, kin san zaman banza ba aikin yi sai sakaran namiji, shine zai kwanta yace komai sai dai ayi mashi, dan yana dan wani, shi kiga basu komai sai bin matan banza da sheye sheye…
Gimbiya Zulaha taji haushin maganar da Hakim ya gaya mata, dan tasan da Hamad Hakim yake, magana ce ya gaya mata a takaice, Amman sai ta nuna bata gane da ita yake ba, ita dai burin ta yasha tea, dan yana sha ya gama aiki..