GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Aiko dai Hakim ai kasan babu maraya sai raigo, Allah dai yayi maku albarka baki dayanku kai da kannanka..
“Amin Gimbiya…
“Da man Hakim jina nayi ance baka ji dadi ba kwana biyu shiyasa nace bari dai nima nazo duba lafiyar sarki mai jiran gado..
“Godiya nike Gimbiya, Amman ni lafiya ta lau gaskiya, Wanda suka gaya maki basu fadi maki dai-dai ba..
“Tabbas, dan gashi na gani da idona, ga shayi nan nayi maka da hannuna dan nasan kana san shayi sosai..
“Nagode, nan Hakim ya ansa shayi ya aje gefe, ya cigaba da marking din papers dinshi, Gimbiya Zulaha na san tace mashi ya zuba yasha Amman bataga fuskar haka ba sai da tayi ta maza sannan tace..
“Hakim ai ya kamata kasha ka jike makoshinka, da man naga duk gaji da alamu..
“Zansha Gimbiya amman sai zan kwanta bacci, dan bani shan wani Abu in ina aiki..
“To shikenan na barka lafiya Hakim, “toh Gimbiya nagode sosai sai da safe..
Haka Gimbiya Zulaha ta fito wajen Hakim ranta bace dan ya bata mata aiki, tunda boka cewa yayi ya sha gabanta sannan maganin zaiyi aiki..
Shiko Hakim Gimbiya Zulaha na fita ya tashi yayi wanka yasa aka fitar mashi da Tea din da Gimbiya Zulaha ta kawo mashi,sannan yasa aka chanza mashi new bedsheet yayi addu’a ya kwantaciyarshi, cikin dare zai tashi yayi sallahr shi..
Washe gari da wuri Hakim ya shirya ya wucewarshi fada, dan yau weekend…
”Allah ya ja da ran maimartaba..
“maimartaba sarki ina ansawa Yarima mai jiran gado..
“Allah ya karamaka lafiya na samaika lafiya? “Lafiya lau Hakim ya aiki? “Alhmdulh, “Allah yayi maku albarka baki daya “Amin ya haiyu..
Nan ya zauna, su kuma fadawa suka cigaba da fadancinsu, Hakim bai bar fada ba sai karfe hudu, dan zasu dan fita shida Aliyu…
Nan ya shirya suka wuce warsu wani join inda ake sha iska..
Masha Allah wata fine girl ce nagani tana shiryawa, fara ce tas masha Allah, ga dara-daren idanunta wanda lashes tayi lub bisa rufar idanun sai kayi tunani fixed dinsu tayi, girarta tasha gyara kamar anzanata saboda yawanta ga kuma shape da tayi ga kuma uwa uba brownrish ne a girar ita ba baki kiranba ita ba brown ba, shiyasa indan ka kyaleta sai kayi tunani jagira tayi, hancinta yana da tsawo amman ba sosai ba sai dai ace medium shi ba karami ba kuma shi ba mai tsawo da yawa ba, bakin dai dai dashi shine Wanda ake kira round mouth ga pinklips dinta masha Allah dai-dai kiss, fuskarta round face ce Amman ba sosai ba round din..
Tana da breast sosai dan idan kaga breast dinta bazakayi tunanin na yar ‘shekara 19 bace, ga uwa uba hips dinta ga shape coca-cola shape gareta, masha Allah gaskiya GIMBIYA HAKIMA ba daga baya ba wajen kyau ba..
Bayan Gimbiya Hakima ta gama shiryawa, ta dauke post dinta da wayarta kirar IPHONE, iphone 11 pro ce, nan ta dauko agogonta ta manna a hannu, yau Gimbiya wane dan bala’in lace tasa black color ba karamin kyau yayi mata ba, sannan ta dauko gyale da takalmi purpura colar ta daurama laces din, sannan ta jefa sweet a bakinta ta sannan ta fito parlour…
“Allah ya kiyaye hanya uwargijiyarmu, hannu kawai Gimbiya Hakima ta daga masu sannan ta fita waje wajen Bala ta amshi key din mota da hannunta dan yau Gimbiya Hakima da kanta dake bukatar yin drive dan sha’katawa zataje..
Nan ta dauki hanyar join itama..
“Hakim kasan abunda ke ban mamaki a cikin gida?
“Aa Aliyu sai ka fada, “Hmm! Lamarin Hamad wallahi Hakim ya fara bani tsoro wallahi baki daya Hamad ya bata rayuwarshi da kanshi…
“Kaga shine neman mata, shine shaye-shaye, baki daya yanzun baida aiki sai na neman mata..
“Uhmm, Aliyu ya zanyi mashi? Nace ya daina yaron da baki daya baya matuntani, how comes zani cema shi ya daina ya daina Aliyu?
“No way gaskiya Hakim ni shiyasa na fi shiri da Humad shi ba ruwanshi, bai yarda ya baiyema Gimbiya Kilishi ba..
“Eh ai daman Humad da Hamad ba halinsu daya ba, shi Hamad baida hankali shiyasa nike yi mashi uzuri, kuma ina guje mashi ranar da Maimartaba zai gane yana wanna harka wallahi daga shi har Gimbiya Zulaha tausayi suke ba, Allah dai ya kauda tsotsayi, “Amin ya Allah…
“Masha Allah, Hakim kalli wata beb nan na tana tahowa wallahi ta hadu, “kai dai ka bani da kallon matan tsiya, dan haka kyaleni bata wata macen da zani kalla, yana fada yana yarda bawon ayaba, nan ko Gimbiya Hakima ta taka bawon bananar nan take sintsi ya kwashe ta ta fadi kasa…
“Inalillahi na boni, “sannu baiwar Allah inji Aliyu, dan shi Hakim tun faduwarta tana juyowa da shirin bata hakuri yaga Hakima ce ya kyale ta ya cigaba da cin ayabarshi hankali kwance..
“Sannu yi hakuri, “dallah can malan matsa kabani guri tunda ba kai kayi man ba, zaka tsaya yi man wata maganar gulma..
“Aa Allah ya huci zuciyarki, dole mu baki hakuri tunda mumaka yi maki laifi..
Tun ihun da Hakima tayi ma Aliyu ta zanyo attention din mutanan wajen sun tsaya suna kallon ikon mai sama Allah…
“Kai har ka isa ka jefoman banana ka kadani cikin mutune how dare you? Ko dan kace kana sona last week nace nafi karfinka shiyasa kace bari kazo nan tunda kasan nan ne wajen zuwa ka bani kunya cikin mutane to karya ne, ka sani dai Hakima na fi karfenka banza stupid man kawai dakai…
Aiko nan mutane Suka kama yan maganganu suna mamaki kamar yarima Hakim wanann yarinyar take yi ma wanna abun cikin mutane..
Yarima Hakim rasa abunda zai cema Hakima yayi, dan haka ya mike ya wucewarshi rashi bace, nan fa yakara sama mutane confused dan wasu sun yarda wasu ko suna confused sosai..
Nan itama Hakima ta juya warta ta koma gida…
By jameelah jameey✍????
Share and comment pls
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????
????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
*M. W. A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????
STORY AND WRITING BY
_Jameelah jameey ????_
(Yar mutan kankia????????)
BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI
Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.
NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????
25&26
“Hakim gaskiya wannan wannan Yarinya ta cika cika marar kunya, amman abun Mamaki shine baka yi mata komai ba”..
“Uhmmm! Aliyu itace wanda na gaya maka ta watsaman chivita a office”..
“Da man wannan yarinyar kake gaya man? Gaskiya batada mutunci ko daya bata san rajarar mutane ba”.
“Hakima kenan, Aliyu wallahi yarinyar na tsane ta sosai, “Aa Hakim ka daina cewa ka tsane ta, domin karda tsanar ta juya soyayya”..
“What? Aliyu maikake cewa? Kana nufin ni Hakim zani so Hakima? To har abada wallahi ko bcox I hate her, baki daya behavior and character dinta bai yi ma ni ba, kai idan zanga wani yace yana son Hakima sai nayi iyakar kokarina na gaya man bata da halo”..
“Haba Hakim! Ya kake yin haka ne dan baka santa sai ka hana kowa aurenta? “Eh domin ban san tayi farin ciki a rayuwarta..
“That Mean! Kaine kenan zaka zama mijin kenan? “Wallahi Aliyu da dan kai bane da bansan abun zanyi maka ba, taya zanso Hakima?
“Amman Hakim! “Dallah Aliyu, please! can’t uh keep quite or No?
“Shikenan nayi shiru kamar yanda ka bukata, Allah ya bamu sa’a Hakim, amman wallahi ka rage tsanar Hakima a zuciyarka, in my advance kenan, “