GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“ok i’ll try my best “


Tunda Hakima ta fito daga Join bata tsaya ko ina ba sai gidan su Maryam nan take gaya mata yanda su kayi da Hakim..

“Wai Hakima gaskiya baki da sauki, amman kiyayi prof Hakim fa, kinga gobe zamuyi test din shi, ga kuma next week exams dan haka ki ajiye makamanki Gimbiya Hakima yar sarkin Kano, ai haka naji bayinki suna cewa ko?

“Mtssssssss!!! Wallahi keki ka damu da test dinshi nidai iyaka mutun ya kadani indai nasan nace banyi failure ba, wallahi sai na shiga na fita cikin ABU Zaria an fiddo man hakina…

“Hakane kuma, balle ma nasan baya kadaki, saboda yanada kirki..

“Wai ke Maryam mai yasa kullun maganarki bata wuce, Hakim yana da mutunci? “To dan yana dashi ai shiyasa na fadi, dan wallahi ya fiki mutunci da tausayi ma, nan ne kawai bamuyi marching ba wallahi Hakima”..

“Godema Allah a cikin gidan ku kika yi man wanann maganar, “inba cikin gidan mu nayi maki ba mai zaki yi man?

“Wallahi sai nasa anyi maki hukunci mai tsanani, sai kinyi wata goma gidan horo horon ma mai tsanani, dan naga baki d’aya baki sona, Hakim kike so ai sai kije ki gaya mashi bai sai kin dunga man haka ba..

“Hmm! Shikenan nayi shiru, wannan tsanar is too much gaskiya Hakima very much ma, taya zakiyi ma dan uwanki musulmi irin wanann tsanar? “

“Nidai!! I tell you, dan haka No Need to touch my friend, ok as with wish Hakima ..

“Ni zan wuce gida mangrid tayi, sai mu hadu test tomorrow by the graces of God, “ok byee thank for visit me, “don’t wrong, thank uh too..

Nan Hakima ta wuce gida, wanka kawai tayi da sallah ta zauna ta cigaba da karatunta, dan yanzun bata da lokacin kowa sai na karatunta tayi missing din gida, amman tayi promise bata ko mawa wani weekend sai dai taje holiday..

Bayan ta gama karatu tayi alwallahr bacci da addu’a ta kwanta bacci da wuri dan eight suke da test din gobe ..


“Gaskiya Kilishi Ina mamakin yanda Hakim yake bata mana aikin mu, ko wane aiki mukayi mashi bai kamashi abun da Mamaki..

“Ni abunda nace Gimbiya mai zai hana mu sake boka, “mu sake boka fa Kilishi? “Eh mana, tunda shi yanka daya aikinshi yaki yi sai mu sake wani mu gamu, ba mu san ida za’a dace ba..

“Kin kawo shawara mai kyau kuwa Kilishi, amman wani hanzari ba gudu ba, “maikenan?

“Ni ina gani harta bayi wanda muke ba aiki sai mun sake wasu amman ya kika ce? “Eh to hakane mu fara chanza boka dai..

“To zanyi ma Lanto magana sai ta chanza mana sabon boka, dan Lanto ba bakon da bata sani ba..

“To hakan ma yayi, ni zan wuce na barki lafiya, “mun kwana lafiya..

“Kaga Aliyu nifa na fara jin bacci, tunda muka dawo duk ka bi ka damai ni da shututunka, har yanzun ban saurari mai amfani ba..

“Yanzun maganar Hakimar ce bata da amfani? Wallahi serious Hakim inasan naga ka auri Hakima dan kunyi marching..

“Kaga ai shiyasa nace maka baka da abun fadi mai amfani dan haka sai da safe, karda nasa ayi man waje da kai..

“Mai yayi zafi Allah ya tashe mu lafiya, “Uhmmm, Hakim yace sannan ya shiga toilet yayi alwallah ya fara sallolinshi da duk abunda ya saba yi kafin ya kwanta bacci…

Bayan ya dawo daga massallaci wanka yayi ya shirya cikin shampoo shadda brown ba Karamin kyau Hakim yayi ba, sannan ya dauki hanyar makaranta saboda test..


“Gaskiya Hakima kin burgeni yau da kika shigo da wuri, “kinji ki da wata magana daman can da wuri nike zuwa school, wancan marar mutuncin ne shine yake ganin bani zuwa cikin lokaci…

“Hmmm!! Nidai Hakima kina bani Mamaki wallahi kedai Hakim bai yin dai dai a wajen ki, “Hmm..

Nan Hakim ya shigo yayi masu test sannan ya kama gabanshi…

By Jameelah Jameey✍????

share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

(Yar mutan kankia????????)

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

29&30

“Oyoyo! Oyoyo!! Oyoyo!!! Daughter sannu da dawowa”…

“Yauwa Momy, wallah Momy duk nayi missing dinku, “ai muma munyi missing dinki Daughter, “Amman shine ko ziyara baku kawo man ba?

“Ai Maimartaba yace karda aje, a barki kiyi karatu sosai, yanzun tashi kice abinci sai kije ku gaisa da Fulani..

“Uhmmm! Mai aka dafa man? “Sinasir mana shi nayi maki da kai na ma, “Yauwa thnk you Momy..

Nan Gimbiya Hakima taci Sinasir din sosai sannan ta nufi shashen Fulani….

“Fulani sannu da hutawa, “Yauwa Hakima ya karatun? “Alhmdulh, “Allah ya baki sa’a, “Amin ya Allah..

“Kinje kin gaisa da Maimartaba ko? “A’a sai gobe zani, na dai aika am maman ison ganinshi..

“To Allah yayi maki albarka, “Amin ya Allah, ni zan wuce, “To Hakima dan Allah kiyi hakuri da wannan bayin Allah da suke a karkashinki”..

“To insha Allah zanyi iyakar kokarina Fulani, na barki lafiya”..

Bayan Hakima ta koma shashen ta, waya tayi da Maryam sun jima suna wayarsu sannan sukayi sallama..

“Bilkisu, “Allah ya taimaki Gimbiya Hakima gani gabanki ina jiran umirninki”..

“Ki dauko takalma nan akaima Barau ya gogeman su, dan inasan gobe naje gidan marayu”..

“Angama ranki yadad’e yanzun zani cika umirninki “..

“Uhmmm, abunda Gimbiya Hakima tace Kenan , sannan tace, “kice ma Azima ta ansoman dinkina gidan waziri, Lantana kuma ta gogeman kayan baki dayan su”..

”To angama yar’sarki jikar’sarki, “bayan nan ki gayama masu aiki nan shashen gobe da safe bayan kungama aiki ina san ganinku baki daya”…

“Insha Allah uwargijiyarmu na barki lafiya “…

Nan Bilkisu ta tafi ta gayama Barau sakon Gimbiya Hakima..

“Malan Barau sannu da hutu, “Yauwa Bilkisu yan zauzau ansha zauzau, “Aiko dai Malan Barau ya muka samaiku? “Alhmdulh “..

“Ai mu tunda kuka tafi , muka fara giba da kumari, dan rabon da aima wani bawa a masarautarnan ko yatsa tun tafiyarku ba’a nuna mana ba, daman Gimbiya Hakima itace marar tausayin da mutunci, to kuma tayi mana nisa”…

“Muma ai tunda muka tafi muke jindadinmu, da man kune kuke jamana, tunda bakusan halin Gimbiya Hakima ba shiyasa kuke bata mata rai”..

”Ai baku ganeba Bilkisu Amman.. “Da kata dan Allah, haba ya isa haka Malan Barau , ko baka san baki shi ke yanka wuya ba? Yanzun idan wani yazo wucewa ya jika kana ai banta Gimbiya Hakima kaga kashiga uku kenan, harda ma ni, dan haka ga wanann takalman nan na Gimbiya Hakima ka gogesu kafin gobe”…

“Yanzun duka uban takalman nan zan goge? Kuma kafin gobe? “Eh ashe ma tambayata kake? Kayi yanda ka gadama ni kaga tafiya ta”..

“Gaskiya sunyi yawa dan na Gimbiya Yakumbo nike gogewa tun jiya har yanzun ban gamaba, kuma ni Gimbiya Hakima daga gani sunfi na Gimbiya Yakumbo yawa”..

Nan Bilkisu ta tafi tabar Barau da salati, dan ya rasa yanda zaiyi ya gama kafin gobe da yaga tunanin ba mai fishewa bane ya tashi ya cigaba ya cigaba da aikinshi ya samu ya gama kafin gobe..

“Ku Gimbiya Hakima tace gobe bayan kungama aiki tana san ganinku”..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button