GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Munbani Ba’ba Bilkisu mai mukayi ma Gimbiya? Daga dawowarta ko sati biyu batayi ba”…

“Taya zan sani Larai? Nima ai yar sakoce, ke kuma Azima tace kije gidan Waziri ki anso mata dinki, Lantana kuma ki goge mata su”…

“Mun shiga ukunmu Allah yasa dai ba wani abu mukayi mata ba, “Amin Ladi nima abunda nike tunani kenan, dan wallahi bansan kiran Gimbiya Hakima dan ba alheri bane”…

“To Ab’u ya zamuyi inba hakuri ba, dan ni wallahi ban so suka dawo hutu ba, muna zaman-zaman mu ta dawo zata matsa mana “…

“Murja wallahi ku iya ganinku, nidai gaskiya nagaya maku, nidai kunga kwanciyata sai da safenku dan yau da wuri zanyi bacci, “to Ba’ba Bilkisu mu kwana lafiya”…


“Gimbiya Zulaha nifa nafara gajiya gaskiya, “Kilishi kwantar da hankalinki dan boka yace nan da wata hudu Hakim ya zama labari, dan yace mutuwa zaiyi cikin ruwan sanyi irin mutuwar da ba wanda zaiyi zargin kashe shi akayi ba”…

“Yauwa Gimbiya Zulaha, gaskiya naji dadin wannan labari naki”..

“Au ai yanzun gashi kingani da naje da kafafuna, ansamu aiki maisauki da kyau, dan Million da’ya na ba boka yayi abunda ya kamata ayi “..

“Da yace na samo bakar Akuya da bakin Zakara da Kaza mai wake-wake da Bunsuru dan shekara goma sha biyar”..

“Dan shekara goma aha biyar fa Gimbiya? “

“Ki tayi gani Namiji da suna Hajara, shiyasa nace ni ina zan samu wannan abubuwan ina gidan sarauta fita sai kabi dare? “

“Gaskiya ko Gimbiya,”ai shiyasa na bashi million daya yayi duk abunda ya dace ayi, da man ni bani san aikin da za’abamu mu zuba ma Hakim a abinci ko abun sha”…

“Nima gaskiya bani san kallar wannan aiki, gwanma kaba da kudi suyi aikinsu da kansu, kai kuma kayi baccinka, ni zan wuce mu kwana lafiya muna zuba ido muga wata hudu yayi zamuyi shagali dan har rawa ma sai nayi “…

“Wai waya ga Kilishi da rawa, ai yana mutuwa zamuyi lokacin ubanshi dan shima na gaji da ganinshi a doran kasa”…

“Au hakane fa, amman ni ban dauki ubanshi matsala ba shiyasa nike mantawa dashi, amman zamuyi lokacinshi mu kwana lafiya”..

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Gimbiya Zulaha da Gimbiya Kilishi sun kasa zaune sun kasa tsaye wajen neman Bokaye..

Basu wurin Boka basu wurin Malan Boka, dan ko wace so take ace nata ya zama Sarki, amman duk tungun da Gimbiya Kilishi take yima Yarima Hamad Gimbiya Zulaha bata gane ba…

Ita dai tasan bata da masoyiya kamar Gimbiya Kilishi, kuma bata da makiya kamar Gimbiya Fulani, dan gani take da Sarki bai aureta ba da Hamad ya zama Yarima mai jiran gado, amman Sarki yayi gajin hakuri yayo mata kishiya ga shinan tana haihuwa da wata biyar itama ta haifi Hamad, dan haka ta uzurtama kanta sai Hamad ya zama sarkin Zaria, dole ta zama uwar sarki dan haka sai inda karfinta ta kare…

Ita kuma Gimbiya Fulani baiwar Allah bata damu da hidimarsu ba, Ita dai tasan rai da lafiya suna wajen ubangiji mu dan haka idan Hakim ya rasu lokacinshi ne yayi, ba dai asiri ba.

Shiyasa bata tada hankalinta ba tasa hidimar gabanta a gaba tana kula da mijinta da yaranta..

Itako Gimbiya Kilishi tana ganin yanda take yar’sarki jikar sarki matar sarki dan haka ya zama dole ta zama uwar sarki bata damu da Humad ba shi bane Babba tunda nan da wata hudu Hakim zai mutu, sauran ta ida dasu Hamad shida uwarshi..

Dan haka sai inda karfinta ya kare, mundun tana da rai da lafiya sai Humad ya zama Sarkin Zaria, shiyasa ta bazama neman bokaye da Malan Boka…


Bayan ko wace ta gama aikinta suka hadu a kofar shashen Gimbiya Hakima suna jiran fitowar ta..

Sai da Gimbiya Hakima ta gama shiryawarta sanann ta fito..

“Kuna jina? “Eh Ranki yadad’e, “naji dadin yanda yanzun kuka maida hankali wajen aikinku, wannan ya nunaman kun fara sanin abunda ke maku ciwo, dan haka sai ku Kara maida hankali sosai, da mai magana? “…

“Aa babu, Allah yaja da tsawancin kwana, “Uhmmm! Kun iya tafiya ku bani waje”…

Nan suka tafi suna mamaki da jindadin chanjin da suke samu wajen Gimbiya Hakima dan tun dawowarta suke ganin chanjin sosai a wajen Gimbiya Hakima ..

“Lantana wuce kicema Bilkisu ta anso man takalman nan wajen Barau, sannan ku tabbatar da kun shirya dan fita zamuyi”…

“Angama ranki yadad’e, nan lantana ta gayama Bilkisu sakon Gimbiya Hakima, sannan suka fara shiryawa itada Azima..

Bayan sun gama shiryawa suka tafi shashen Gimbiya Hakima, ita ma Bilkisu ta anso takalmi har shiryawa tayi suna jiran fitowar Gimbiya Hakima su wuce gidan marayu..

Bayan ta fito suka wuce gidan marayu tayi masu abunda ta saba yi sanann suka wuce kasuwa nan tayi provision dan gobe take koma wa school sun gama hutu, zasu dasa second semester…

Washe gari Gimbiya Hakima ta shirya tayi bankwana da kowa sanann suka dauki hanya Zaria..

ByJameelah jameey ✍????

Share and comments pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

(Yar mutan kankia????????)

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

31&32

Washe gari da wuri Gimbiya Hakima ta shirya ta wuce school dan ko breakfast bata tsaya tayi ba saboda tanada prpratical…

“Lantana!ki tabbarta da kungama komai dan bansan na ɓata maku rai”..

“Allah yataimakeki,Ranki yadad’e insha Allah zaki samaimu masu bin umirninki”..

“Uhmmm”..

Nan Gimbiya Hakima tafi tana sauri dan bata san ta makara dan ta lura lokacin gudu yake ga prof Hakim ne zai shigo masu..

“Bala”..

“Allah ya ji da tsawancin kwana, “idan ka kaini ka juyowarka gida zan kiraka indan mun tashi”..

“Godiya nike uwar marayu Allah ya ƙara maki lafiya da daukaka”..

“Uhmm! Yi sauri Bala bansan na makara lokaci na tafiya”…

Nan Bala ya ƙara bama mota wuta dan shima ya fahimci Gimbiya Hakima batasan tana makara dan taba bokonta Fahinmanci sosai…

Haka suka isa ta fita ta wuce class shi kuma ya wucewarshi gida yana murnar yanda Gimbiya Hakima ta barshi ya wuce gida ba tare da tace ya jira har sai ta gama lectures ba..

“Maryam kinga yanda kika ka ƙara kyau da haske ba kamar ba keba kinga yanda kika koma kuwa? “Hmm! Na kaiki Hakima baki ga yanda kimar Hakim ba”..

“Kinji matsalarki ko? Har zaki fara ɓata man rai ko? “..

“Hakuri Gimbiya yanzun dai ya kika baro su Fulani da Yakumbo? “..

“Lafiya lau wallahi suna gaisheki ma, “ina ansawa, mundawo kenan sai hutu kuma tunda second semester ba wani daɗawa akeyi ba”…

“Ni daman ba wani weekend din da zani sai hutu, yanzun dai muna zuba ido muga anfiddo mana da result”…

“Allah yasa dai muga alkhari”Amin ya Allah “..

Nan dai suka cigaba da maganarsu, nan sai ga Hakim ya shigo…

“Morning class,”morning sir, ba tare da ɓata lokaci ba Hakim ya cigaba da yi masu lecture, lecture ta dauko dadi dan class din yayi shiru ba kajin motsin komai sai maganar Hakim..

A na cikin lecture Gimbiya Hakima taji wani irin fitsari ya matso ta, dan tayi iya bakin kokarin ta na ta matsa fitsarin amman abun ya faskara dan ya ma kusa kufce mata…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button