GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

Amman Bokan yace duk randa Hamad ya ɗauki buta da sunan zaiyi alwallah yayi sallah wannan sihirin ya kare..

Wanann shine dalilin da baki ɗaya Hamad baya san Hakim dan ko ganinshi bai san yi..

Aliyu shi dan gidan Waziri ne dan sa’annin junane shida Hakim, Hakim wata biyu ya ba Aliyu a duniya duk tare suka taso..

Wannam kenan ☺️

Back to the story kundai summary din kabarin Hakim shida yan uwanshi..

By Jameelah Jameey✍????

Share and comment pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

(Yar mutan kankia????????)

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

33&34

“Hakim lafiya naga duk ka wani zama silent maike damunka? “..

“Hmmm! Aliyu kai dai bari wallahi yau nayi ma Hakima abunda banji dadi ba ko da sau daya ne”..

“Mai kuma ya sake haɗaku da ita? “..

“Kawai dai kasan abunda tayi man a join, to shine nima na rama amman at the end banji dadin abunda nayi mata ba wallahi totaly”…

“Wata sabuwa inji yan-caca, mai kuma kayi mata? “..

“Kawai dai ta tambaye ni zata fita na hanata daman already na fahimceta fitsari xatayi, wallahi banyi tunanin fitsarin ya matseta sosai ba kawai naga yarinya na fitsari a tsaye, baka ji yanda nike ji ba kamar mai”…

“Ayya! Maganar gaskiya Hakim baka kyauta ba, ai koda zaka rama abunda Hakima tayi maka bai kamata kayi mata haka ba”…

“Ko baka san ba’asan mata na tara fitsari ba? Balle ita ta tambaye ka ka hanata gaskiya baka kyauta ba”..

“Uhmmm! Naje nayi ita bata ga abunda tayi man ba, dan haka ni nama kyauta, na lura kifi son Hakima a kaina komai akayi nine banda gaskiya”…

“Yes of course! Nidai naga kai ka wurga mata ɓawon ayaba, maimakon ka bata hakuri sai MULKI DA SARAUTA suka hanaka dan gani kake ka fi karfin da zaka bata hakuri, ita kuma taga bata iya kyaleka har ta rama”..

“To na Hakima naji sai akayi ƙaƙa? Dan haka ba ruwanka faɗana da Hakima kasa ido kayi kyalo shine naga OK?! “..

“Ni kuma bani yin shiru mudin nagani sai nayi magana, kawai ina ganin gaskiya a hana ni magana gaskiya sai nayi”..

“To parrot! Ai sai kai tayi, tunda bakasan kaga bakinka yana shiru ni tashi ka ban waje zani gaida Fulani”…

“Ai bakai daya keda Fulanin ba, dan haka tashi mu tafi daga nan naga Sahibata”..

“Baka da kunya a gabana? Kayi addu’a Allah yasa Maimartaba indan ya tashi badasu ya sa sunanka”..

“Amin ya Allah! Nifa Hakim duk wanda aka bani inaso dan ai duk kamarsu ɗaya dan har yanzun bani gane Maryama balle Sadiya”…

“Hakane kake wahalar banza baka ganesu kenan? “Wallahi ko”to Allah ya kyauta niko dai ba gaya maka zanyi ba”…

“Naji tashi mu tafi! Nan gaba dole na ganesu insha Allah tunda ɗaya zata zama halak malak ɗina”..

Haka suka tafi shashen FULANI shidai Hakim yana mamakin yanda Aliyu yake kare Hakima bayan duk rashin kunyar da take yi mashi..

Shidai baya iya ƙyaleta yaga tana yi mashi rashin kunya dan ko su Maryama sun girmi Hakima da shekara ɗaya ko biyu shiko maganar gaskiya baya iya daukar rainin wayau Hakima..

“Fulani barka da hutawa, “Yauwa Aliyu! Yau kenan a gidan namu? “..

“Laaaa! Ina neman afuwa Fulani amman ina shigowa sosai”..

“Eh ba laifi, dan nasan kafi wancan ɗan neman, dan na lura baki ɗaya Hakim baya san zuminci”..

“Aa Fulani ki bar cewa haka, wallahi kullun sai naje na gaida Mama ko Aliyu? “..

“Eh gaskiya kana zuwa, nine dai bani shigowa sosai, ina neman afuwa kuma”…

“Ai Aliyu nasan ya zuwa shashen ku sosai, ina nufin baya zuwa shashen Su Gimbiya Zulaha da Kilishi kaga banjin daɗin haka gaskiya Hakim”…

“Allah ya taimakeki yar’sarki matar sarki kuma jikar sarki, amman ba uwar sarki ba dan ni bani san sarauta na barma Hamad yaje ya riƙe”..

“Aa Hakim inkai baka so mu mana so a baka ko Fulani? “..

“Kudai kuyi fatan Allah ya tabbatar maku da alkhari cikin rayuwarku, mu kullun shine fatan mu dan haka idan ba Mulkin bane alkharinka Hakim Allah ya taya Hamad riƙo, in kuma shine alkharinka Allah ya tayaka riƙo”..

“Kuma ba wannan ba Hakim! Ya kamata ka fiddo mata hakanan dan na gaji da ganinka haka babu mata, ina amfani ku dukanku babu aure bakai babban ba ba ƙannanka ba”…

“Insha Allah Fulani zanyi koƙari naga na fidda mata dan bansan Maimartaba ya fara yi man maganar fiddo mata”…

“Aiko yana hanya dan har ya fara yi man magana kawai dai kaine bai kai dayi mawa ba”..

“Ai Fulani kafin ma yayi ma Hakim zai fiddo mata, dan yana nan yana neman wata… “Dakata haka dan Allah parrot uban yan’surutu”..

“Ya ka buge mashi baki? Bangane yayi shiru ba Hakim? Bakasan ya gayaman inda sirikar tawa take dan daman nasan Aliyu yasan inkanada Budurwa ko ma baka da ita dan shine kawai abokinka”..

“Wallahi Fulani banda ko kiyashi amman insha Allah zan fara neman budurwa verysoon insha Allah “…

“To Allah yasa! Inata addu’a dai Allah ya haɗaku da nagari, “Amin ya Allah “..

“Wai Fulani ina su Maryama suke? “Basunan sun tafi gidan su Maryam amman nasan suna hanya yanzun haka “..

“To Allah ya maidosu lafiya, “Amin, “Fulani maiyasa ake barin su Sadiya suna fita wai? “..

“taya zan hanasu zuwa gidan su Maryam bayan kasan wacece a wajensu”..

“Hakane mu zamu wuce Fulani mun barki lafiya, “uhmm”…


“Gaskiya Maryama abunda Yaya Hakim yayi ma Hakima bai kyauta ba baki ɗaya”…

“Dan Allah mai yayi mata? “.

Nan Maryam ta gayama su Sadiya abunda Hakim yayi ma Hakima..

“Wallahi da kun ganta a lokacin sai ta baku tausayi dan kuka ta kama yi ni na kaita gida da kaina”.

“Gaskiya Yaya Hakim bai kyauta ba, muda muke san su auri juna taya haka zata kasance yana yima ta kallar wannan cin mutuncin? “..

“Aa ai ko baya taɓa yuyuwa dan ko ni bani auren wanda ya tsaneni, to wani kallar rayuwa zasuyi bayan nasan baya sona ya tsaneni nida nike son nayi auren soyayya”…

“Kamar kin sani karkiso kiji yanda Gimbiya Hakima ta tsani Yaya Hakim, dan yau ta faɗi kalmar tsana bansan iyakaba”..

“Banga laifinta ba gaskiya ai abun yayi yawa, Fissabililah ai cin fuska baida dadi, sai kace ba yan’uwanjuna ba”..

“Yan’uwanjuna kuma? “..

“Ehman Sadiya yan’uwanjuna tunda su dukansu muslmai ne suna sallah kinga ko sun zaman yan’uwa”…

“Hakane kuma ai nasa mu yan’uwa ne, “Aa ko ɗaya kawai dai jininmu ne ya hadu da nata tun bamu ganta ba”…

“Wallahi ko! Jinike kamar naje na ganta amman ba dama, “aiko dai, dan Allah Maryam ki ƙara bata hakuri sosai please”..

“Ok insha Allah, “mu zamu wuce gida kinga dare ya fara karda mu kashema kanmu kasuwar gobe”..

“Gaskiya ku tashi ku tafi karda ma ku kashe harda ta jibi, “Byeee ki gaida Hakima, “ok zataji byee..

By Jameelah Jameey✍????

Share and comments pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button