GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

(Yar mutan kankia????????)

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

35&36

Washe gari bayan Hakima ta gama yin breakfast ta shirya ta wuce school..

“Hakima! ina kwana?, “Yau kuma da wannan kika zo? “..

“Laifine dan na gaida kawata, kuma Gimbiya yar’sarkin Kano? “..

“Aa baki yi laifi ba, yasu Momy?, “suna lafiya Hakima, kawayena yan gidan sarki suna gaisheki”..

“Uhmmm, “haba Hakima ya zani ce maki friends ɗina suna gaisheki amman Uhmm kawai zaki ceman? “..

“Kedai baki gajiya da complain uwar yan complain imeans ina ansawa haba, dole sai kinsa mutun magana koda baiso”…

“Allah ya baki hakuri kenan yau yan mulkin suna bisa kai, Allah ya kyauta, “Uhmmm”..

Nan Maryam itama ta kama ƙanta tunda ta lura da Gimbiya Hakima batasan yin magana itama sai tayi shiru dan bata san suyi faɗa da ƙawar tata..

Nan suna zauna sai ga Hakim ya shigo lecture, ba ƙaramin kyau yayi ba daman abunka da farin mutun ya ɗauko wani bakin bowel mai bala’in kyau da tsada ya sanya sai ya fito jinin sarautar sak da shi dan yau shima sarautar ta mutso mai shiyasa class din basuga fuskar yin noise ba kowa ya kama girmanshi sun naba’a kamar anyi mutuwa..

Koyawa yake cikin natsuwa da jan-class dan ko shi kanshi yana mamakin yanda yake jin bayasan magana, duk da haka halin shi yake amman yasan na yau yafi na kullun..

Niko Jameey nace jinin sarautar kenan????☺️

Suna cikin yin lecture nan Hakim yayi pointing ɗin Hakima ta fito ta zana mashi wani compoud aiko ba karamin dadi Hakima tayi ba dan har ta shirya irin abunda zata yi ma Hakim, balle da ta lura yau wani mulki yake ji sai kace ɗan sarkin zaria..

Hahahahaha! TEAM Hakim kunji Hakima da wata magana wai Hakim take cema sai kace wani ɗan sarki kuji fa, koda yake tace shi ɗan gidan uban waye????

Tafiya take cikin isa da nuna ita ɗin watace, dan tafiya take amman kamar mai tausayin ƙasa dan bata san taka ƙasar sosai…

Ba Hakim ba harda yan class suna mamakin yanda Hakima take tafiya duk da sun saba da halin Hakima ba sabo bane a wajensu amman suna mamakin izzarta, kamar wata yar’sarki…

Tofa! Team Hakima kunji fa abunda yan class da Hakim suke cema Hakima wai kamar wata yar'sarki☹️????

Tana zuwa gaban Hakim ta miƙe hannu ta amshi maker ɗin da zatayi using da ita, daman takalmin Hakima ba flat bane, masu tsinine dan haka tana sane ta takema Hakim ƙafa, dan sai da yace..

“wash!.

Amman Hakima ko a jikinta dan nunawa tayi kamar bata taka komai ba, ta cigaba da abunda ya sata, baki ɗaya class din sai da suka tsorata…

Hakim ba ƙaramin zafi yake ji ba, dan yana ma tunanin yatsan ƙafarshi ya cire yanda Hakima ta take mashi su, kuma ta saki ƙarfinta baki ɗaya bisa ƙafar…

Amman da yake Hakim jarumin Namijine sai ya dake bai nuna yasan da wani hallita a ƙafarshi ba, duk da jinin da yaga ya fara fitarmai a ƙafa amman ya dake yanuna ma students dinshi bai damuba..

Hakima bata gamaba sai da ta tabbatar da Hakim yaji jiki sanann ta juyo ta miƙe mashi maker, suna haɗa ido ta kashe mashi ido ɗaya tayi mashi nuni da ita Hakima tafi ƙarfinshi dan ta wuce duk wani tunaninshi..

Hakim bai nuna ya ganta ba, haka ya cigaba da lecture ɗinshi har ya samu ya gama sanann ya fita..

Tafiya yake yana mamakin yanda Hakima ta raina mashi wayau, ta maidashi wani abokinta..

“Tabbas indan na biyeta Hakima ina iya lahantata, harni Hakim Hakima zata fiddama jini? Tabbas nayi sake da na bari Hakima ta rainani har haka”..

Hakim ne ke wannan maganar yana ɗaukar hanyar komawa gida yana mamakin rainin da ke tsakaninshi da Hakima…

“Haba Hakima wai bakiga abunda kikayi ma prof Hakim ba? “..

“Maryam na fahimci baki san Allah, ni bakiga abunda yayi man jiya ba? Dan na rama sai ya zama laifi? “…

“Ya kamata kubar yar’ramuwarnan keda prof Hakim, sai kace ƙananun yara, sai kace ba jinin sarauta ba”…

“Wannan matsalarkice, dan ina jinin sarauta sai akace karna rama abunda akayi man ko? “..

“Baki fahimceni ba, bake ɗaya bace jinin,”enough please Maryam ni kinga tafiyata gida dan inada abun yi, kuma wallahi Maryam ki kiyaye ni na gaya maki gaskiya ki zaɓi cikin biyu ni ko Hakim byee”…

“Allah ya baki hakuri ke na zaɓe ma ba sai gobe ba, byee”..


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya rashin ganin mutuncin juna sai karuwa yake tsakanin Hakim da Hakima..

Dan ba wata jutuwa suke ba har yanzun, Hakima bata da wanda ta tsana kamar Hakim..

Haka shima Hakim bayan kaunar Hakima, dan baya san mutun marar kunya da ganin girman na gaba da shi..

Kuma ya fahimci baki ɗaya Hakima yarinya ce wanda batasan ta girmama na gaba da ita ba..

Ni kuma nace kuji man Hakim yasan da haka yake biyema Hakima suna kallar wannan bed habib ɗin☹️ kash Allah dai ya shiryasu baki ɗayansu

Hakima tasa karatunta gaba dan har sun fara exams ɗin second semester kuma daman an fiddo mashi result itace over rolla, tayi mamaki da Hakim bai kadata ba a course din shi..

Haka dai suka gama yin exmas dinsu har Gimbiya Hakima ta koma gida hutun season…

Su Gimbiya Zulaha kuwa suna nan sun zuba ido suna jiran wata hudu yayi suga gawar Hakim.. (Lol????)

My guys kudai ku cigaba da biyoni kuga kallar cakwakwakiyar da za'ayi tsakanin wannan mutunan guda hudu☺️????

Gimbiya Hakima da Yarima Hakim

Gimbiya Zulaha da Yarima Hakim

Gimbiya Kilishi da Yarima Hakim

Yarima Hamad da Yarima Hakim

Wai Allah na kai dai Hakim kaga ikon Allah kowa da akai yake faɗa ayya Hakim bakai ne baka da gaskiya ba????

Team Hakim ina jiran Answers ɗinku wai shi Hakim ba shi bane baida gaskiya ba☺️

By Jameelah Jameey✍????

Share and comments pls

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️

 *M. W. A* 

Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ????????


STORY AND WRITING BY

_Jameelah jameey ????_ 

(Yar mutan kankia????????)

BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI

Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne.

NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI????????

37&38

“Gimbiya Hakima! Uwargijiyarmu barka da dawowa wanann masarauta mai albarka”..

“Uhmmm! Ladi ina fatan kuna aiki yanda ya kamata? “..

“Eh Uwargijiyarmu muna yi, muna farin cikin dawowarki uwar marayu”…

“Zaki iya tafiya, ki gayama yan’uwanki da su tabarta da suna aiki akan lokaci”…

“Angama ƴar’sarki jikar sarki, na barki lafiya, “Uhmm”…

“Larai! Mu godema Allah wanan karatun yasa Gimbiya Hakima ta chanza baki ɗayanta”…

“Aiko dai Larai, karki so kiga kallar farin cikin da nike, domin koni jiya da naje yi mata barka da dawowa fuskar sake ba kamar da ba “…

“Alhmdulh! Hakan ma mungode, indai babu wanann zagin dake yi mana ai ba komai “..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button