GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

GIMBIYA HAKIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

“Eh naji Momy, “Daughter yanzun har zaki shiga 300 level amman banji kin fara kula samari ba, komai yasa.”?

“Haba Momy ai ni yarinya ce fa duka duka yanzun  nike da shekara sha tara fa, ni gaskiya ban isa aure ba.”

“Aiko kice kika isa aure, ki fara kula samari in ba haka ba Maimartaba ya fidda maki da kanshi kinsan dai kina gama karatun nan aure zaiyi maki.”

“Momy jibaini fa yarinya dani Baffah yayi man aure tun yanzun ina laifin na gama masters din sannan.”

“Daughter waya gaya maki gidan sarauta ana karatu.”?

“Momy amman.. “Da kata Hakima.”

Yakumbo ta tsada Hakima cikin fushi dan ta lura Hakima batada ra’ayin kula samari kuma tana tsoran karda maimartaba yayi mata auren dole…

“Daughter gidan sarauta ba’a karatu sai dai mulki yanzun ne da zamani ya shigo mu masu sarauta muka dauki boko muka sama kanmu Amman mu da mulki aka sanmu.”

“Kuma Ina laifin da ya barki kikayi degree, ki fidda master a zuciyarki kisa aure, Daughter ki fara kula samari kafin dare yayi maki shawarata kenan a matsayina na Wanda ta daukeki diya.”

“To insha Allah Momy zan duba, ni zan wuce Momy na barki lafiya.”

“To Daughter, kin gaida Fulani KO? “Aa yanzun zan wuce wajenta daman daga wajen Baffah na biyo wajenki sanann wajenta, “OK Daughter.”

Haka Hakima ta dauke shashen Fulani tana tunani maganar da Yakumbo tayi mata ba kamar wannan maganar, “Daughter ki fara kula samari kafin dare yayi maki.”

Haka Hakima ta Kama maimata wanann maganar har ta iso shashen Fulani, nan akayi mata iso ta shiga..

“Fulani ina wuni, “Lafiya Hakima ya karatun.”?

“Lafiyalau Alhmdulh, “to Allah ya bada sa’a, “Amin ya Allah…”

“Na sa maiki Lafiya.”?

“Lafiya lau, in kina bukata ki shirya gobe zamu adamawa bikin Yarima Bishir.”?

“Ok daman Yaya Bishir aure zaiyi kenan? Shine babu ko gaiyata.”

“Hakima taya Bishir zai gaiyaceki bikinshi bayan kin gujeshi? Wani irin sone Bishir baiyi maki ba.”?

“Ai Fulani ni yarinyace ban isa aure ba shiyasa ban yarda da soyayyarshi ba.”

“Ai sai ki ta zama Hakima har sai randa kika isa auren sai kiyi, shidai Bishir jibine aurenshi yar’sarkin Yobe zai aure Gimbiya Zaituna.”

“Allah ya basu zaman Lafiya, “Amin ya Allah.”

“Ni zan wuce nasa a fara shiryaman kayana kafin goben.”

“To mu kwana lafiya, “Allah yasa Fulani.”

Haka Hakima ta dawo shashenta tasa Azima ta shirya masu kayansu ita da su Inna Lantana..


“Kilishi kinga wannan maganin shi za’a sama Maimartaba cikin abinci yana ci ya gama aiki.”

“Ar’riri nanaye, Gimbiya wannan abun yayi man dadi sosai bani shi nan naje na sama shi tunda yau nike dashi.”

“Daga ganin Sarkin Fawa sai Miya tayi zaki.”?

“Ai Gimbiya zafi-zafi a kan buga karfe ko.”?

Hmmm! “Ai duk saurin unguwar zoma dan ubanta ta bari a haihu sanann tazo ta yanke cibi.”

“To Gimbiya gayaman ya za’ayi.”?

“Ajiye maganin zamuyi sai nan da shekara biyar sanann.”

“Maiyasa kikace haka Gimbiya.”?

“Eh Kilishi yanzun muka bashi magani yasha ya mutun kafin shekara biyar kinga dole aba Hakim mulki.”

“Kin kawo shawara kuma mai kyau.”

“Wallahi na tsani naga Hakim yayi mulki kona kwana daya ne, dan uwarshi za’a kirata da uwar’sarki, na tsani naji ana kiranta da wanna sunan.”

Haka suka kama tautaunawa sannan kowa ya kama gabanshi..


“Ranki ya daɗ’e angama shirya komai.”

“Azima kin tabbata komai da komai kika shirya.”?

“Eh duk abunda nasan zaki bukata na shirya shi kawai umirnin ki nike jira uwar marayu.”

”Ok zaki iya tafiya ki fiddo naku kayan sai mu wuce shashen Gimbiya Fulani.”?

“Godiya muke uwar marayu, yar’sarki jikar’sarki uwar sar… “Dakata haka mana Azima kinsan bansan wannan surutun naku na banza tashi kije Kiyi abunda na saki kafin ranki ya ɓaci yanzun.”

Hakima ta faɗi cikin ɓacin rai dan ba abunda ta tsana duniya bai wuci kace mata uwar’sarki ba dan ita bata shirya aure ba dan yanzun balle har ta zama wata uwar’sarki..

Haka Azima ta tashi tana mamakin Hakima ta lura duk yanda kake da Gimbiya Hakima mudun kace mata uwar’sarki sai ta nemi wulakanta mutum ko waye shi nan Azima ta cigaba da fiddo kayan su amman tunanin na cikin zuciyarta bata tace, “oni Azima ko maiyasa Gimbiya Hakima batasan ace mata uwar’sarki.”?

Batasan maganar ta fito fili ba sai ji tayi Ba’ba Bilkisu nacewa, “ai abunda yasa Gimbiya Hakima bata san kiranta da uwar’sarki saboda bata shirya yin aure ba yanzun.”

“Sannan bata gaji da mulkamu ba san ranta yanda take bukata duk da yanzun Alhmdulh komai yayi sauki ba kamar da ba.”

Hmmmm! “Aiko idai hakane gaskiya muna da aiki nida nike murna ta kusa gama karatunta sai aure amman ace mutun bai san aure.”

“Azima kisa a ranki ki ko gidan aure tare zaki da Gimbiya Hakima sai dai kawai mu samu muna shiga jikinta sosai yanda zata ji kunyar wulakanta mu cikin mutune.”

“To shikenan kawai ku taso mu tafi kunsan bata san jira, “aiko dai.”

Nan suka tafi suka ida shirya ma Gimbiya Hakima
Sannan suka wuce shashen Gimbiya Fulani…

Bayan Gimbiya Fulani ta gama shiryawa suka dauki hanyar Adamawa…

Bayan sun isa Adamawa aka tarbaisu tarba ta girmamawa aka saukesu shashen Gimbiya Fulani dake cikin gidansu nan tayi yan-matancinta..

Bayan sun huta Suka dunguma sai shashen tsohon sarki  Maimartaba Sarki Kabir mahaifin Fulani Aisha..

Nan suka gaisheshi sannnan suka wuce shashen Maimartaba Sarki Al-Khamis shine sarki mai mulki yanzun yayan Fulani Aisha ne uwa ɗaya uba ɗaya ɗanshi ake yima biki Yarima Bishir..

Bayan sun gama gaisawa ta wuce shashen Gimbiya Mabaruka wato mahaifiyarta sai da suka gama gaisawa sannan ta wuce shashen kowa suka gaisa ta dawo shashenta..

Washe gari aka fara hidimar biki ba karamin kudin ake zubda wa ba haka aka kama al-adu kala-kala sune basu je suka kwanta ba sai dare..

Haka ma wan shekare aka ɗaura daga inda aka tsaya bayan angama kowa yaje ya kwanta..

Washe gari aka daura Auren Yarima Bishir da Gimbiya Balaraba yar’Sarkin Yobe..

Nan Gimbiya Hakima taje yi ma Yarima Bishir Allah yasa alkhari..

Tafiya take cikin natsuwa da kwanciyar sai kace wanda take jin tausayin kasa bata san takata, wani irin lafoyaiyen lace ne black a jikinta ba ƙaramin kyau yayi ma Hakima ba abun ka da farar fata sai kace itace amaryarma..

Tunda ta doso wajen Yarima Bishir ya kafeta da ido yana ainama kanshi duk rintsi sai ya mallaki Hakima da sunan matar aurenshi dan ba ƙaramin so yake yi ma ƙanwartashi ba..

Sai da ta iso wajenshi ta fara magana sannan ya dawo cikin haiyacinshi, dan ƙaramin bakinta yake kallo tana motsashi kamar anayi mata dole..

“Ina tayaka murna Yaya Bishir Allah ya baku zaman lafiya”..

“Hakima maiye aibuna a wajenki?  Maiyasa baki sona? Nifa ɗan’uwanki ne Hakima kuma ina masifar sonki da kaunarki”…

“Haba Yarima Bishir taya zakayi wannan maganar bayan abun ya wuce tuni gashi yau aka daura maka aure”..

“Dakata haka Hakima nayi alwari komai nawa zai ƙare sai dai ya ƙare wajen neman auren ki dole ki aureni Hakima ko kina so ko baki so”..

Ya faɗa cikin fushi da ɓacin rai ya barta tsaye da mamaki..

Tota Team Hakim gafa Yarima Bishir nan ya sake dawowa anya wannan abun zai yuyu kuwa?

”'”””””Nidai question nayi maku ina jiran answers????????‍♀️”””””’

By jameelah Jameey ✍????

Share
Comment
Vote
Like
please

????????????????????????????????????????????????????????????????????????
         GIMBIYA HAKIMA
????????????????????????????????????????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button